ka baki buɗe irin na mamakin yadda taci da yawa har haka tana dubansa tace, "amma Uncle tare ne muka cinye ko?" lakuce mata hanci yayi kafin yace,"ke ɗaya kika cinye, dama ance sirara ci ne da ku". tana murmushi ta ce, "no Uncle wayo ne har da kai ne muka ci". ta faɗi hakan tana ziro ƙafafunta zuwa ƙasa da niyyar miƙewa, da sauri ya tareta da cewar, "to where?". "toilet". "me za kiyi a toilet kuma?". "zan wanke bakina". har bakin toilet ɗin ya rakata kana ya dawo yana jiran fitowarta, sai da Deborah ta dawo ɗakin sannan yay musu sallama ya tafi, wayarsa ma bar mata yayi, amma yaja mata kunne in dai bata yi bacci da wuri ba zai goge game ɗin daga wayar kuma ko sun koma gida zai ce Dad kar ya bata waya.
***washe gari likita da ya shigo ya ƙara duba jikin Mairo, da duk wasu gwaje-gwaje da suka kamata, yaja Deborah gefe ya sanar mata akan idan Emanuel yazo ta sanar masa su taka da yarinyar zuwa bakin titi, may be a samu a dace, ko da bata yi recalling duka ba zata ɗan iya tuna wani abun, kasancewar a accident ne tayi loosing Memory nata so ganin gimlawar motocin ka iya sawa tunaninta ya dawo, ita kanta Deborah tana tausayin yarinyar, dan tun da ta sami sauƙi most of times tana lura da ita zata ga ta dafe goshi kamar mai tunanin wani abu ko me son tuna wani abu, idan ta tambayeta sai ta ce mata she was thinking like there is something crucial da ya kamata tayi, but ta kasa sanin menene shi.
me aiki na mopping akai knocking ƙofa, "yes come in". cewar Deborah. sai taji shiru ba'a shigo ba dan haka ta umarci me aikin ta leƙa ta amso abinci ne. ita kuma taci gaba da kimtsa kayan Mairo acikin medium trolly ɗinta dan likita yace gobe za'a ba su sallama. fitowar Mairo daga wanka ta tsaya nunawa Debora wajen ɗinkin da aka yi mata, tana mata complain akan yana yi mata ciwo, tayi mata sannu tare da ɗauko magani ta shafa mata a wurin, sannan ta nuna mata kayan da zata saka. "ki saka waɗan nan may be idan Uncle yazo ya tafi da ke church tun da kinji dama-dama". tayi knodding kanta kawai sannan ta ɗauki lotion ta shiga rubbing jikinta. Emanuel da Md da Deborah tun a farko sun zauna kan ƙiyasin wanne addini Mairo zata kasance kenan aciki, Md yace masa ai za su yi considering ne da garin da ya sameta, so kuma kan titin ma da ya bugeta ɗin daji ne, amma garin da ke gaban shi 99% ɗinsu there all christians, dan haka suka tsaya akan ittifakin cewar itama christian ce kamarsu.
rigar fara ce long slip me kyau, sai mini skirt ɗin black, haka ta sakasu kuma tayi kyau acikinsu gwanin sha'awa, Deborah wacce ta fita ta dawo ita tayi mata makeup tare da gyara mata gashin kanta da yayi yalayala da shi a gadon bayanta.
ta zauna bakin gado ita kaɗai tana shan ice cream, Deborah ita tuni ta ɗauki hanyar church kasancewar yau sunday, Emanuel ya shigo maƙale da waya a kunne yana magana, ta ɗago tana dubansa har ya ƙaraso ciki ya zauna kusa da ita, ba ƙaramin kyau yayi ba acikin shigar tasa wadda suka yi anko da ita shi ma baƙin wando ajikinsa da farar riga long slip, sai zuba ƙamashi yake kamar wani ango, ita bata taɓa ganinma yay kyau irin yau ba.
ya kama hannunta a sanda yake cewa da MD,"ai kai dai munafuki ne". daga can ɓangaren Md yay dariya da cewa, "munafurcin ƙaniyarka nayi". a san da Emanuel ya juyo da Mairo tana fuskantarsa, ya maƙele wayar a kafaɗarsa yana saka mata sarƙar cross yana cewa da Md,"ai da Dad bai yarda dani ba sai kaga yanda zanyi da kai. da Favour(Matarsa) zan haɗaka na faɗa mata gaskiyar kana cin amanarta a waje". Md yace,"da ka hargitsa min gida kuwa". Emanuel yay ƙwafa da cewa,"zan so haka, dan am tired of ganinka da wasu Matan a waje ahalin kana da taka...Mumu kawai aika kusa haihuwa kayi hankali". sosai Md yay dariya da cewar,"you be Mumu too. ya ku kai Dad ɗin kuwa?". "kasan yana da fahimta, damuwata ɗaya yanzu Mom...amma dai ka bari tukunna idan na shigo office gobe mayi maganar. yanzu zan tafi chapel time na ƙurewa". "oak see you letter, ka gaida min da patient naka". "alright zata ji...bye".
Kusan Mairo taso fahimtar hirar abin da yake faruwa, duba da yanda ta kafe shi da ido sai ya kai hannu idonta zai tsone, sai ta riƙe hannun tana dariya, shi ma yay dariyar tare da kama fuskarta yana duba idanuwanta.
"Beb idonkin nan har yanzu yana ciwo, bari ayi discharge namu gobe sai kema a maki visa ku tafi tare da Obi a duba naki acan". "waye Obi kuma ina ne can wurin da zamu?". ta tambaye shi tana tsare shi da ido. "he is your Brother too...inda kuma zaku je Germany shi ma yana ciwon ido zaije a wanke masa". "to kai ba zamu tafi tare da kai ba?". "Beb bana iya yin nisa da office indai ba Seminar ba". "oh to yayi". ta faɗa tana maida bakinta da ta cuno. yace da ita, "nima zan sha ice cream ɗin". sai ta miƙa masa sauran, ya maƙe kafaɗa yana cewa,"um um". sai kuma ya buɗe mata baki, dan haka ta ɗebo a spoon ta ba shi. sannan ya miƙe da ce mata shi zai tafi Church ta kula da kanta yasan Deborah ma ta tafi. ta ɓata fuska da faɗin,"ni fa?". ya kwantar da murya da f