uma daga yau idan ka ƙara cewa wannan zindiƙin kafirin ina gaisheshi wallahi sai ƙaga yanda zamu kwashe da kai acikin gidan nan, to fa daga wannan lokacin Gwaggo ta fara share Ya Amadu, ta koma komai zatayi sai dai Ya Kabiru, dan ko gaisuwar Ya Amadu sama-sama ta-ke amsa masa, babu shiri kuwa ya fara janyewa daga Oga Joseph koma nace ya janye gaba ɗaya, yana tare da shi ne dama saboda a rufawa kai asiri, tunda duk sanda ya buƙaci yay masa rakiya zuwa Lagos yana samun kuɗi sosai a wajensa, harma yayi masa alƙawarin zai yiwa Daddynsu magana a nema masa gurbin karatu a jami'a dan ya ɗora degree nasa tunda yana da diploma.
"Baba to kaje a aske maka gemun mana tunda naga yana damunka".
Na faɗa idanuna ƙyar akan haɓarsa da yake sosawa, ya bani amsa da cewa, "yau insha'Allahu zani a aske, ni nafi ganewa askin wanzamai su kuma su Amadu sai suce ba haka ba". Ina murmushi nace, "to Baba ai na kilifa ɗin yafi yin kyau, kuma kaga shi ance ba'a fiye ɗaukan cutukan zamani ba".
Kafin ya bani amsa Ya Kabiru ya shigo, ya tsuguna yana cewa da Baba gashi.
"Yauwa Kabiru nace ya za'ai anjima dan Allah ka nemo mota ƴar ƙurƙura akai itacce gidan galadima". "babu damuwa Baba sai a nemo, zanwa Hamisu magana idan baza shi cikin gari ba saina karɓi tasa". "to Na gode Allah yayi muku albarka. Ina Amadu yana nan ko ya wuce makaranta?". "ehh naji dai ya fita ɗazu to amma ban sani ba ko makarantar ya wuce tunda banji ya min sallama ba".
Baba yasa hannu a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙa mishi,"Dubu huɗu ce ka bashi ya auno masara da shinkafa ya kawowa Suwaiba". Yasa hannu biyu ya amsa tukunna ya fice, shi ma Baba yay sallama da Matansa ya fita, mu kuma yaran mukabi shi da adawo lafiya.
Da yamma muna zaune ƙarƙashin rufin kwanon ƙofar ɗakinsu Lukman wanda yake kallon ɗakin Baba, Inna Amarya ce ta gama yi min yankan farce ta-ke kuma saka min lalle kasancewar gobe zamu koma makarantar boko hutu ya ƙare, an gama sawa Adawiyya nata tun ɗazu, Adawiyya itace sakuwata dan tsakaninmu shakara guda ne ta bani, komai namu tare Inna Amarya ta-ke haɗamu tayi mana, mun zama tamkar ƴan biyu duk da cewar uwarta ba son hakan ta-ke ba, dan wani lokacin Inna Zulai har kulleta take a ɗaki ta zaneta akan shige mana da ta-ke yi, haka zataci kukanta ta gama, tana buɗeta kuma ta kuma dawowa wurinmu, burinta ma bai wuce ta koma wurin Gwaggona da zama ba dan kayanta da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai ta kwaso ta maida su can, shi yasa abin da ke shiga tsakaninta da uwarta harara da hantara.
Ya Kabiru ne ya shigo hannunsa riƙe da baƙar leda, yasa Zubaida ta miƙo masa kujera ya zauna gefe kusa damu, fuskar nan tasa ɗauke da murmushin da baya rabo da shi, marabar shi da Ya Amadu kenan, Shi mai fara'a ne da son mutane saɓanin Ya Amadu da baya son mutane kuma miskili ne na ƙin ƙarawa, shi idan ka ganshi a gidan yana hira to da Baba ne ko Gwaggo ko Ya Kabiru wanda suke tamkar ƴan biyu dan tsiransu shekara ɗaya ne a haihuwa.
Ina bala'in son duka yayyuna biyun nan saboda kyawawan halayensu da ke burge kowa, da kuma yanda suke nuna min tsananin so, dan komai suka rakiito da tsarabarsu nawa ne ni da Adawiyya, Ni yarinyace wacce ta san kyau kuma nake son kyau, saboda hakane na gane duka yayuna biyun da nake matuƙar so kyawawan gaske ne, hancinsu har baka irin na Baba, ga fararen idanu da dogon gashin ido, na kan kasa tantance acikinsu waya fi wani kyau, idan na tambayi Adawiyya sai tace ai Ya Kabiru yafi kyau tunda yafi Ya Amadu haske kuma yana da wushirya, sai nace mata a'a shifa Ya Amadu har dimple ne da shi kuma bakinsa yafi na Ya Kabiru ƙanƙanta, haka muke zama muyita wannan musun da junanmu, ƙarshe sai Yagana ce ta raba mana gardama tace ai Ya Kabiru yafi kyau tunda shi ingarman namiji ne, Kalar mazan da mata suka fi so, ba ƙaramin daɗi naji ba da batun Yagana domin akomai ina so naji ance Ya Kabiruna yafi, haka itama Adawiyya akomai tafi so ace Ya Amadu yafi.
"Sannu da dawowa". Inna Amarya tace da Ya Kabiru wanda yake latsa ƴar ƙaramar wayarsa. "yauwa Inna Amarya". Ya amsa mata yana buɗe kwanon abincin da Basma ta ajiye masa agabansa yanzu.
Gwaggo ta fito tana ce mishi, "Kabiru kuma saina jiku shiru daga kai har Amadu baku kawo cefane ba. Shi ne kawai saina bada aka siyo taliya ƴar murji akayi jalof, Allah yasa dai zaka iyaci". Tun shigowarsa idona yake akansa na kasa ko da ƙiftawa, babu wanda ya lura dani harta shi ɗin dana ke ta aikin kallo, gani nayi ya ɗan yatsine fuska kaɗan kamin yace, "zanci mana Gwaggo, ba dai abinci bane kuma duka kowa yaci zai rayu lafiya. To ni wane da bazanci ba". Ya numfasa bayan ya sosa girarsa sannan yace, "Gwaggo kiyi haƙuri da mukaje kai itacen gidan Galadima ne bamu dawo da wuri ba, sai yanzu ne dana dawo na miƙa mishi kuɗin".
"ai tunda ansamu wanda za'aci ɗin shikenan, dama bana son yin abinda ba kwa son ci ne, na bada a siyo ƴar gwamnati naji tayi tsada shi ne nace to kawai a karɓo taliyar murji.
Allah sa shi wancan ɗin idan yazo ya iya ci". "zaici mana Gwaggo, yanzu ma