ta gutsuro cinyar kaza zata kai baki ta dakata da ci ta tsare shi da ido saboda yanda taji amon faɗa na tashi daga cikin wayar. dan haka ya miƙe ya fita daga waje gudun karta fahimci abunda ke faruwa. Emanuel ya kwantar da murya ya shiga yiwa Dad bayanin abunda ke faruwa, da dalilinsa na ɓoye masa bai sanar masa ba, sannan ya ba shi haƙuri akan hakan. daga ɓangaren Dad yay shiru yana nazari akan ɗansa, auna zantukan nasa yake akan mizani na duban hankali da zurfin tunani, wani ɓari na zuciyarsa ya bijiro masa da cewar anya zancen Emanuel gaskiya ne ba bin Mata ya fara ba, banda haka tsawon shekaru bai taɓa ɓoye masa wani abu ba sai da akazo irin wannan gaɓar, gaɓar kulawa da mace a sirrance, sai kuma yay saurin watsi da zancen da zuciyarsa ke raya masa, sam ɗansa ba zai aikata makamancin hakan ba, ya yarda da shi ya yarda da tarbiyar da ya ba shi, Emanuel kaman yasan Dad na tantama ne da maganar tasa dan haka ya katse shirun nasa da cewar, "Dad believe me am not lying to you...idan kuma har zan faɗa maka akasin haka to ƙarya nake, amma if you are still doubting ka kira Onoaka(Md) ka tambaye shi". "is oak na yarda da kai, amma kar irin haka ya kuma faruwa kayi shiru gudun faruwar wata matsalar. yanzu ina ita yarinyar?". Dad ɗin ya faɗa yana sauke murya ƙasa. "tana room, bana so ta fahimci cewar bata da wata alaƙa da ni ne shi yasa na fito waje, idan ta gane hakan zata iya shiga damuwa, she would like to know who she is, and where to find her parents after she is no longer in her thoughts.".
Dad yace,"haka ne, Allah ya bata lafiya. kai mata wayar zamu yi magana". Kamar yace da Dad a'a, dan ba ya so kwata-kwata Dad yayi mata maganar sanadin ciwonta. yana shiga ya miƙa mata wayar da cewa,"Dad on the Phone". ta karɓi wayar ta riƙe kamar mai son tuna wani abu sai kuma ta kara wayar a kunne. "Hello Dad good evening". "good evening daughter, how is your body?". "am felling better Dad". "Good. Hope your brother is not bothering you?". ta jijjiga kai da cewar,"Yes Dad". ta faɗa tana kallon Emanuel da ya harɗe hannaye idonsa akanta. sannan tace,"Dad When are you coming to check on me?". "i will be there when your Mom comes back". "Where did she go?". "she travel to egypt for her seminer but she will soon be back. bari na barki haka you should rest oak". "oak thank you Dad, Good Night". daga haka ya gimtse wayar. ita kuma ta miƙawa Emanuel wayar tana cewa,"Uncle kamo min irin game ɗin wayar Aunt". tana faɗa tana gutsirar nama. "yanzu lokacin cin abinci ne bana game ba". sai ta dakata da cin naman ta dubi Deborah tace ta bata tissue, ta miƙo mata shi kuma ya tambayeta,"me za ki da ita?". "zan goge hannuna na ƙoshi da abincin". ta faɗa murya a ƙasa irin tayi fushi ɗin nan, Emanuel ya zauna kan kujera yana bata haƙuri, "kici abincin bari na tura miki game ɗin a wayar Aunt". "ni fa a wayarka nake so". yace,"ehh ai zan tura daga wayar Aunt ne, kinga ni banda ita". tayi knodding kanta,"umm". ya karɓi wayar Deborah ya tura game ɗin Rolling Sky sannan ya miƙe ya fita daga waje yana installing na game ɗin, bayan yace da Deborah ta zuba Ferfesun yana ɗayan white ledan ta bata taci. Debora ta zuba ferfesun a plate ta aje gaban Mairo, ita kuma ta ɗauke kai tana aikin tura baki gaba, Deborah tayi ƙwafa da cewar,"kin san Allah ni kam zan fara maganinki da wannan shagwaɓar taki, kinfa ji sauƙin da za ki ke cin abinci da kanki amma ko yaushe sai kice lallai sai na baki". ta kuma gwame baki tana ƙara ɓata rai. Debora taja gefe ta ce,"sai kuma kiyi ai, ni da ƙara feeding naki kam sai da safe". tana gama faɗar haka ta miƙe zata fita sai ga Emanuel ya dawo, tun daga nesa da ya hangi yanda tayi kicin kicin da fuska ya dafe goshi, sannan ya ƙaraso yana tambayar Deborah me yasa bata sa taci abincin ba. "she said she want to it by her self, thats why na ƙyaleta". bai ce da ita komai ba ya ƙarasa kujera ya zauna yana kallon Mairo da tai frowning face nata sak ƴar baby, sai shi ma ya ɓata fuska da ce mata,"sa hannu kici abinci". dan ya lura idan su na biye mata to taɓarar tata yawa zatai, duk da yana mata uzuri da sabon halin da ta tsinci kanta, may be da ace ba tayi loosing memory ba ba zata ke hakan ba, although a yanda yake kallonta ba ya tunanin ta fara period, kasancewar wani girma na manyan breast bai nuna ajikinta ba.
still fuskansa a ɗaure yace,"ba za ki ci ba?, you want me to start beating you bah?". tai saurin girgiza masa kai alamar a'a, sai ya sassauta muryarsa ganin yanda tasha jinin jikinta da sauyawar da yay, yace da ita," do you want me to feed you?". tayi Knodding kant alamun eh, ya matso da kujeran gaban gadon ya amshi plate ɗin da ke hannunta, ɗan kaɗan ya ɗebo a spoon, daidai bakinta ya kai spoon ɗin sai yaga ta kawar da kanta gefe. "Beb again. kina so muyi faɗa ko?". tana aikin ƙifta idanu ta girgiza masa kai. "oya open your mouth". ta buɗe baki ta shiga amsar ferfesun, bai ƙyaleta ba sai da taci da yawa kana. ta dubi plate ɗin taga mugun cin da tayi, dan ha