NOVEL SHARES -
har da cewan sai mun tashi mun bika. ƙarshe ma abincin da kasa akayi order bata ci ba wai hannun delivary Man ɗin da ƙazanta she cant eat". abun yaso bashi dariya, dan haka ya miƙe ya ɗagota daga kwancen yana bata haƙuri da lallashi, sai da ƙyar ya shawo kanta tayi murmushi ta haƙura, tace masa,"amma Uncle idan ka sake me zan maka?". yace mata,"purnish me...yanzu dai kici abinci". ya faɗa yana buɗe takeaway ɗin da tun safe yake ajiye. ta dakatar da shi da faɗin,"ni fa ba zanci wannan ba, naka nake so". ya mayar ya ajiye sannan ya fita zuwa siyo mata wani.
*_Waiting For Your Warm Comments, likes, and Opinions...Your Support is all i need...LOVE YOU ALL._*
*Vote!Vote & Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*21)*
Har ya isa Lagoon Restaurant shi kaɗai ya kanyi murmushi idan ya tuna da rigimar Mairo, an haɗa mishi komai da ya buƙata ya juya ya shiga mota, har zai mata key sai ya ɗauko wayarshi ya kira Deborah tana ɗauka ya ce da ita, "give the phone to Beb". Miƙawa Mairo tayi wacce ke daga kwance ta amsa murya cike da shagwaɓa ta ce, "yes Uncle". murmushi yayi kafin ya ce, "is there anything you want bayan ferfesun?". cije leɓe tayi tayi shiru tana nazari, ta lura ko ɗazu da ya shigo he looks extremely tired, dan haka kamar tana gabansa tace,"nothing more". "for sure?". yanayin yadda yay tambayar tabi ta ba shi amsa, daga haka ya kashe wayan, sai da ya shiga Mastergrillerz ya siya kaza gasashshiya tukunna ya ɗakko hanyar dawowa shi ma nan sai da ya ƙara tsayawa ya jidi choculates kana ya wuce asibitin.
Hira suke ita Deborah, tana bata labarin wani masifaffen Pastor a church ɗinsu, ita kuma sai dariya ta ke yi, tana ce mata idan zata ce Church ɗin zata bita saboda gansa, kuma idan taje sai ta saka masa ƙafa ya faɗi ya ƙume, tun da dai shi ma ya kori Aunt ɗinta daga wurin ibada, ai da yanzu adu'arta ta amsu ta warke sun tafi gida, dan ta fara gajiya da asibitin kullum mutum na zaune wuri ɗaya, Deborah tace,"zan nuna miki shi idan mun je, ɗan ƙarami da shi sai jarabar tsiya".
Emanuel tun da ya dawo sai ya tsaya a bakin ƙofar bai shiga ba kuma bai fita ba, su ma basu lura da dawowar tasa ba, shi kuwa haka kawai sai ya kasa ɗauke idonsa daga saman fuskar Mairo saboda yanda dariyar tayi matuƙar amsar fuskarta, ba ya so ya shigo ya katse mata jin daɗinta, yanda ta cija yatsa tayi ƙwafa mai ƙarfin sauti tare da tuntsirewa da dariya irin wadda ta tamawa wata muguntar sai abun ya ba shi dariya shi ma, dariyar tasa ne ya karkatar da hankalinsu gare shi yana shigowa fararan haƙoransa duka a bayyane.
Debora ta miƙe ta isa gare shi ta amshi ledojin da ke hannunsa, Mairo kuma ta bishi da ido har ya ƙaraso sannan tayi masa sannu da dawowa.
ya zauna kan kujera yana faɗin, "ni ma sai an bani labarin tunda dai ba'a jira na dawo anyi dani ba". Mairo tayi ƴar dariya da cewar, "i will gist you Dear Uncle, buh before then fara bani abun da ka siyo min". ta faɗa tana miƙa masa tafin hannu. ya ɗauko ledar ya dire mata a gabanta zai buɗe sai wayarshi tayi ƙara, dubawa yayi sunan Dad ya fito akan screen, kamar ba zai ɗauka ba saboda ɗazu da ya je office Sectery ya sanar masa Dad ya shigo jiya bai same shi ba, kuma ya kira wayarsa bai yi picking ba, and yace ya kira shi bai kira ba, saboda haka yake tsoron ɗagawa dan shi mai laifi ne. sai da kiran ya kusa katsewa tukunna ya ɗaga, tambayar da ya tsammaci ji daga bakinsa ita yaji a yanzu,"i called your number several times but it didn't get through, whats going on?". a yadda yaji muryar Dad ɗin sam babu walwala alamar yana cikin damuwa da rashin samun nasa sai yaji ƙirjinsa ya buga. yay shiru yana tunanin abun da zai ce, Dad ya katse shirun nasa da kiran sunansa, "Emanuel". "yes Dad". yay saurin amsawa. "am asking you something you kept quite, ko akwai wani matsala ne da yake faruwa but you hide it from me?, jiya ma fa baka je office ba kuma na tambaya an tabbatar min da hakan, Oya Emanuel tell me what you are hiding becouse you are not like this, am convinced there is something fishy going". a yanda muryar Dad ta fita ta ba shi tsoro dan bai fiya yi mishi magana a haka ba, sai dai Md ko su Joseph. ya soshi girarsa yana auna abun da zai cewa Dad ɗin, ba ya masa ƙarya kuma ba ya ɓoye masa duk wani abu da ke faruwa da shi, infact ma this time around ne abu ya taɓa samunsa ya rufe bai sanar masa ba, kuma ba dan komai yay hakan ba sai dan gudun tashin hankalinsa tun da ba cikakkiyar lafiya gare shi ba, amma yanzu tun da har ya gano da kansa ba shi da yanda zai yi dole ya faɗa masa.
ya ɗago ido ya dubi Mairo wadda