NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 67 of 223

". Md ya tsaya yana yi masa wani irin kallo, ya lura gaba ɗaya nema yake ya maida al'amarin yarinyar kansa, shi kuwa Emanuel gani yake kome ya faru da yarinyar shi ne sila dan haka dole ya tsaya ya kula da ita. Md ya nufa ƙofa yana ce masa,"so ni dai good nite". kamar ba zai ce masa komai ba sai yace,"karka kawo mana tea da safe na lura kaman bata sonsa". "to sai mene take so?". Emanuel ya ɗago yana tsareta da ido, dariya ta suɓucewa Md yace da shi,"ask her mana". Emanuel yay masa wani wawan kallo sannan ya ɗauko wayarsa daga aljihu ya kira Deborah, ko minti biyu ba ai ba sai gata tazo, yace ta tambayi Mairo abunda tafi son ci, Mairo ta girgiza kai a san da Deborah ta tambayeta alamar babu komai. Emanuel yana latsa wayarsa yace da Md,"abu soft ake da buƙatar taci so please ka taho da curstard and do not be let". Md ya kyaɓe baki yace,"aini ba ɗan aikinka bane da har kake faɗa min wani karna makara, you will see me a duk san da na gama hidiman gabana". "ka barshi ma ba sai kazo ba". Md yay dariyar ƙularwa sannan yace,"anyway no escort?". "kasan hanya ai". Deborah dai murmushi tayi saboda tun ɗazu tana ganin yanda suke buga dirama, kuma duk Md ke jansa da tsokana. yayi shiru ya kasa ɗauke ido daga kanta, tausayinta yake da dukkan ransa, kansa yake ta ɗorawa laifin duk da cewar ita ma akwai nata na rashin bin ƙa'idar tsallaka titi, dan haka ba zai yafewa kansa ba har sai ta sami lapia completely. around 9 likitan ido yazo dubata, yay gwaje-gwajensa ya tabbatarwa da Emanuel tana da buƙatar aikin ido a babban asibiti da yake musamman na ido ne, amma for now zai bata wasu maganin da zata yi amfani dasu ciwon ya lafa. tare suka fita da Dr ɗin yaje ya siyo maganin da ya rubuta, tana baccin ya ɗiga mata maganin sannan yaywa Deborah sallama ya wuce makwancinsa. *** cikin kwanaki goma ciwonta Alhamdulillah ya fara sauƙi, ƙafarma an kunce bandage yanzu tana ɗan takawa a hankali, idonta kuma yanzu tana gani da shi sai dai ba wai yanda ya kamata ba. ta kuma saba da Deborah sosai dan 24hrs su na tare, tana koya mata lesson akan yanda harshenta zai kama da yaren da suke yin magana, wanda Emanuel ne ya sata hakan kuma yana biyanta da tsoka. Alhamdulillah tana ganewa sosai, ko magana akai tana ji sai dai ba komai take iya maidawa ba. yau bai shigo da wuri ba, a ɗan turancin da bakin Mairo ya fara kamawa ta tambayi Deborah,"Aunt is that tall Man not coming today?". Tayi mata murmushi da cewar, "his name is Uncle". Mairo tace,"ohh Uncle, to zai zo yau?". ta gyaɗa mata kai da cewar,"umm zai zo ƙila ko yaje office ne". tayi knodding kanta kawai sannan ta ɗauki littafinta taci gaba da rubutunta da Deborah ta bata. kuma rufe bakinsu kenan wayar Deborah tayi ringing, ta ɗauka ta kara a kunne tana gaishe shi, amma sai bai amsa mata ba yace ta bawa Mairo. ta miƙa mata wayar ita kuma tana ci gaba da yankan farce. daga cikin wayar ya kira Maira da,"Beb". ta amsa masa, "Yes Uncle Good Morning". "Morning Beb, how was your night and your body?". "Uncle am feeling better". "thats good. did you eat your breakfast?". duk da cewar taci amma sai ta ce da shi, "no". "why?". tayi shiru bata ce komai ba sai yatsanta da ta saka a baki tana cijawa, cikin dabara ta raɗawa Debora cewar ta faɗa masa,"ta kasa cin komai ne tana son ferfesun kayan ciki ne". Deborah ta amsa wayar tana ce mishi,"wannan patient ɗin naka ta cika kwaɗayi, taƙi cin komai sai fefesu take son ci". yace, "me yasa biki faɗa tun ɗazu ba, bari nasa ayi mata order yanzu". kamin ya kashe wayar ya bawa Deborah uzurin rashin shigowarsa, yaje gudanar da wani meeting ne amma da zarar ya kammala zai shigo, hankalinsa gaba ɗaya yana nan ya kasa samun natsuwa. tace da shi, "ka nutsu kayi aikinka jikinta da sauƙi sosai". "sai dai nazo na gani da idona". ya faɗa yana kashe wayar. sai 7 na dare ya shigo asibitin, kana ganinsa kaga wanda gajiya ta yiwa duka, ya zauna kan kujera yana yiwa Mairo magana sai yaga tayi masa shiru taƙi kula shi, sai baki da ta turo gaba cikin salo na shagwaɓa. yace da ita,"Beb why are you frowning at me?". ya tambaya yana kama babban yatsan ƙafarta. ta kalle shi ta ɗan murguɗa masa baki, yay murmushi ya matso da kujerarsa bakin gadon sosai, ita kuma sai ta kwanta ta juya masa baya. bai saba da ganin rigima irin haka ba, ba su da yara kuma ba shi da me yi masa, dan haka sai yayi tunanin ko wani abun ke damunta, ya ɗauki waya ya kira Deborah ya hauta da faɗan akan mene zata tafi ta barta ita kaɗai, ai kuɗi yake biyanta ba kyauta take masa aikin ba. sai gata ta dawo da sauri har tana haɗa hanya tayi zaton ko jikinta ne ya tashi. tana zuwa ta leƙa fuskar Mairo taga idonta biyu, kawai dai ta ɓata rai ne tana neman fashewa da kuka mara dalili, ɗazu ma abunda ya haɗasu kenan ta fita ta barta da wannan turo bakin gaba. Emanuel dai bai daina faɗansa ba, "idan kin gaji ki faɗa min mana na nemi wata". ta rissinar da kai,"sorry Sir ba fa wani abu ke damunta ba tana fushi ne akan baka zo ba, tun ɗazu take min complain
🏠