NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 66 of 223

i. har drip ɗin ya ƙare bata farka ba, sha biyu na dare yana tare da ita kamin ya tashi ya tafi hotel ya kwana acan, ya barta da Nurse ɗin ɗazu yace ta kwana da ita. washegari bai shigo asibitin ba sai around 9, hankalinsa gaba ɗaya na kan Mairo da ita ya kwana a ransa, abunda ma ya hana shi sammakon shigowa sai da ya biya office. kai tsaye ɗakin da take kwance ya shiga, tare su ke shi da Md, da mamakinsa sai yaga bata kan gadon kuma babu kowa a ɗakin, yana dube-dube sai yaga Nurse ta fito da ita daga toilet tana dafe da kafaɗar Nurse ɗin tana takawa da ƙyar, ya zuba mata ido sai ya miƙe ya ƙarasa ya ɗaukota ya kawota kan gadon ya jinginar da ita ajikin pillow. Nurse ɗin tayi masa bayanin jikin nata da sauƙi dan Dr ma yace zuwa dare za'a iya warware mata bandage ɗin fuskarta. Mairo tayi shiru tana sauraronsu dan jinta take a wata sabuwar duniyar, ita kanta maganar da suke yi ba ganewa take ba, gashi ba ganinsu takeyi sose ba hasalima sai ta kusa rumtse ido gaba ɗaya ne take samun ganin abu very tiny. "How are you feeling now?". Emanuel ya tambayeta yana kamo hannunta ya riƙe cikin masa. ta dai ji maganar da yayi amma bata san me yace ba, tayi shiru sai Nurse ɗin ce tace da shi,"i noticed like she is not hearing english". Md ya girgiza kai da cewa,"i also noticed that". Emanuel ya dube shi yace,"to mene abun yi kenan?". "amma ai lossing memory ba ya shafar language na mutum". Debora tace"um ba ya shafar yaren mutum, ita ɗin bahaushiya ce tun da ɗazu da hausa tayi magana". Md ya ɗaga kafaɗa,"alright, shi ma english ɗin da sannu ai zata iya making". "me taci da ta farka?". Emanuel ya tambaya. Deborah tace da shi,"babu komai yanzu dai za'a iya bata". ta ɗauki ƙaton tea flask ɗin da suka zo da shi ta zuba tea a mug sai ƙamshi yake, ta miƙawa Mairo cup ɗin tana cewar ta amsa da yake ita tana jin hausa kaɗan-kaɗan kasancewar tayi zaman Kano. Mairo ta miƙa hannu tana laluben ta inda zata amsa Cup ɗin, suka tsaya dubanta da mamaki kafin Debora tace da ita,"me ya sami idon naki ne, ga ta inda na ke miƙo miki abu ke kuma kina miƙa shi ta wani wurin". muryarta na rawa kamar zata yi kuka tace,"ai bana ganinki ne". "ba kya gani?". Mairo ta ɗaga kai,"ehh ina ganin duhu amma bana ganin hannun naki". Debora ta sauke numfashi sannan ta dubi Emanuel wanda ya tsareta da ido yana jiran cewarta tace masa,"akwai matsala fa a idanunta, she says she cant see very well". Emanuel ya juyo yana duban Mairo da mamaki, how comes hakan zai kasance, to ko dama ita makauniya ce shi yasa ta sanyo kanta kai tsaye titi har ya kasa kauce mata. Md ya katse masa tunani da cewar,"what are you thinking?". yace da shi, "ina tunanin mene yay cousing na ciwon idon nata, dama can da ciwon ko kuma a accident ɗin nan ne?". Md yace,"gashi kuma babu wani abu da zata iya tunawa bare ta bada amsa". Emanuel yayi shiru, Md ya ƙara cewa da shi,"ya kamata fa Police su shigo cikin lamarin nan, tun da ba za kai ta zama da yarinya ba, ai kayi iyaka yinka tun da ka kawota asibiti akan lokaci". ya girgiza masa kai,"bana so Police su shiga zance i have already told you that...ko asibiti ma da su kai maganar rufe bakinsu nayi da kuɗi". "to kana nufin zaka ke ta zama da ita ne?". ya ba shi tabbacin hakan ta hanyar jijjiga masa kai. "to office fa?". "ai kana nan, ko ba zaka iya aiwatar da aikin company ba idan bana nan?". Md bai ce da shi komai dan ya rasa ta cewa gaba ɗaya. Debora ce ta bawa Mairo tea ɗin tasha, sannan ta bata magunguna da allura. Emanuel ya tashi daga kan kujerar da yake ya koma gefen gadon ya zauna, yana riƙe da hannunta ya tambayeta,"what is your name?". da mamakinsa sai yaji tace,"my name...". sai kuma tayi shiru. "ehen said it your name is what?". "i dont know my name". a yanda tayi maganar sai ta ba shi tausayi.  su na ta hira shi da Md ita kuma duk tana jinsu bada sanin abunda suke faɗa ba ko kuma ganinsu ba, ita dai har tsawon awannin da suka shuɗe Emanuel bai saki hannunta ba. sai around ƙarfe biyu na rana sannan suka fita shi da Md zuwa restaurant suka ci abinci suka dawo, time ɗin kuma tayi bacci, ya tambayi Deborah ya sauƙin jikinta tace masa, "ai bayan tafiyarku tana ta kuka wai idonta na ciwo". "ko asibitin ido za'a kaita?". ya jefa tambayar ga Md. sai Deborah tace masa akwai likitan ido da yake zuwa da daddare. misalin bakwa na dare Md ya umarci abokin nasa da ya tashi su tafi, Emanuel yace da shi ya tafi shi zai kwana nan ne. Md ya dube shi da tsantsar mamakinsa yace,"zuwa wane lokaci zaka bar yarinyar nanne ka koma harkar gabanka?". "ni kuma for how many times kake so nata maka repeating cewar zanke zama da ita anan zuwa lokacin da za ai discharging nata". "amma kana tunanin za su sallameta nan kusa ne?, muna fa da meeting cikin satin nan kuma kasan ya kamata kake shigowa office saboda hakan". "zan yi posponding meeting ɗin". "zuwa yaushe?". "time ɗin da zamu bar asibiti". "then sai kayi ya da ita kuma?". "zata zauna tare damu har lokacin da tunaninta zai dawo a nemi iyayenta
🏠