nsa yayi dai-dai da fitowar Dr Simon daga ICU da waya maƙale a kunnensa yana magana da wani likitan. Emanuel yasha gabansa dan sam Dr Simon bai lura da shi ba, ya dafa kafaɗar Emanuel yana ci gaba da tafiya. Emanuel ya tambaye shi,"Dr what is her condition now?". ya tambaya anxiously. "Your patient is in dire state, we can not say anything for now. but relax we are trying all we can". likitan yace da shi yana ci gaba da tafiya. Emanuel ya nemi kujera yay zaman daɓaro, yanzu idan yarinyar nan ta mace ya zai yi?. acan ɗakin tiyata kuwa ayanzu manyan likitoci uku ne akanta kowanne acikinsu jiki sanyi ƙalau, almost 3hours kenan da gama yi mata surgery ɗin amma har yanzu bata farfaɗo ba, wanda hakan yasa suka fara cire rai da farkawarta, rigima ta fara kaurewa a tsakanin likiticin su biyu, Dr David na faɗa akan mene ma yasa Dr Simon yay gaggawar yanke hukuncin ai mata Surgery, yanzu gashi nan idan yarinyar ta rasa ranta zai iya jawa asibitinsu matsala, shi ma Dr Simon masifar yake masa ai rashin sanin makamar aikinsa ne ya shi yake faɗin haka, Dr Friday da ya zama madiater shi ne me aikin basu haƙuri. sai kowannensu ya nufi ƙofa zai fita a zuciye, amma ƙarar na'urar da ke nuna cewar Mairo na da rai shi ya dakatar da fitar tasu, Dr David ya dawo da sassarfa, haka ma Dr Simon da Nurses suka ƙarasa gareta a hanzarce.
Bayan wucewar wani lokaci Doctor Simon ya fito, Emanuel ya tsaya jingine da bango yana fuskantar ICU ɗin, da sauri ya sha gaban Dr ɗin yana ƙara tambayarsa halin da ake ciki, yay masa murmushi tare da cewar ya biyo shi office, haka Emanuel yabi shi sai dai bai bar waigen bayansa ba, har sai da idanunsa suka ga an fito da Mairo anyi wani room ɗin da ita kana ya sami natsuwar bin bayan likitan, but still zuciyarsa bata bar taraddadin abunda likitan zai faɗa masa ba.
Emanuel ne zaune kan kujera yana facing likitan tare da sauraron bayanin da yake masa, tun a furucin farko da ya ambaci amnesia yaji hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi.
"mun samu ta farfaɗo and we thank God jikin nata da sauƙi, sai dai kuma ta sami matsala ta Memory Loose ciwon da muke kira da amnesia saboda buguwar da tayi aka, so she will be Inability to remember her past for a long period of time...".
ya sauke ajiyar zuciya yace da Dr,"for how long will she remember everything?". "zai iya taking nata 3-5months.". ya miƙa hannu ya karɓi kati na magungunan da za'a siya sannan ya fita. kai tsaye pharmacy ya nufa ya siyo magunguna da alluran duk da ake buƙata kana ya wuce ɗakin da aka kwantar da ita. tun daga window yay tsaye yana kallonta yanda aka ɗaura mata drip, fuskarta naɗe da bandage haka ma ƙafarta ɗaya, yafi tsawon daƙiƙu uku a bakin tagar yana jin kamar ba zai iya shiga ciki ba saboda yanda tsigar jikinsa ke tashi, sannan ya dawo bakin ƙofar room ɗin ya tsaya, har san da Nurse ta shigo ta karɓi ledar pharmacy ɗin daga hannunsa, ta ƙarasa taje tayi allura a ruwan drip ɗin, bayan fitarta ya ɗaga ƙafa kamar mara lakka ya ƙarasa bakin gadon, tsananin tausayinta yay mugu mugun kama shi, daga irin yanda take numfashi ya isa ya fahimtar da shi irin mawuyacin halin da take ciki. jin zafin ciwon nata yake ajikinsa, haka duk wani shiga da fitar numfashinta auna shi yake da nasa. ya zauna a gefen gadon ya kai hannu ya taɓa wuyanta yaji temperature nata very high, yayi saurin ɗauke hannu sannan ya miƙe ya fita da sauri ya koma office ɗin Dr Simon ya shaida masa yanayin zafin jikinta da ya zarce tunani, tare suka dawo da Dr wanda yana zuwa ya kuma yi mata aune-aune sannan ya ƙara tabbatar masa da babu wata matsala da zarar ruwan ya ƙare zata farka kuma temperature nata ma zai dawo normal, kuma ko da ta farka kar abata komai becouse aikin da aka mata general anesthesia ne zai iya ɗaukanta 24hrs kamin taci wani abun, amma idan an samu Bowel sound ya zama present to za'a iya bata ruwan tea tasha, Emanuel babu abunda ya iya ce masa sai knooding kansa da yayi.
bayan fitar likitan Emanuel ya roƙi Nurse ɗin da ke gyara table ɗin da aka ɗora magunguna alfarmar ta zauna ta kula da ita zai je ya dawo. baifi 30minutes ba sai gashi ya dawo hannunsa riƙe da manyan ledoji, ya zaro 5k a aljihu ya bawa Nurse ɗin ta amsa tana ta murna. shaf ya manta da batun wata waya sai ayanzu da ya jiyo ringing ɗin wata wayar daga waje sannan yasa hannu ya ɗauko tasa a aljihu ya kunna. yay dialling number MD sai da kiran ya kusa yankewa sannan MD ya ɗaga yana masa masifar ina ya saka wayarsa. yace da shi,"i got an accident...hankalina bai dawo jikina ba sai yanzu". a zafafe Md yace,"Emanuel are you Mad?, you have an accident kuma ba zaka kira ka faɗi situation ɗin da kake ciki ba...yanzu kana wane hospital?". "ka bari zuwa safiya zan sanar da kai, amma please karka bari Dad ya san da wannan. idan ya tambayeka akaina ka san ƙaryar da zaka yi masa". dan haushi ma Md ya kashe wayar ba tare da ya amsa shi ba, shi kuma yaƙi faɗa masa ne gudun kar ya faɗawa Dad ko kuma shi yace yanzu zai taho alhalin kuma yana da iyal