NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 64 of 223

hanya har Allah ya fito dani, ban san ko ina ne ba nan ɗin, sai dai na kanji kamar sautin gimlawar ɗai-ɗaikun motoci. a san da naji na ɗora ƙafata bisa kwalta, daga gefe naji an hankaɗani nayi sama na faɗo ƙasa tim. cikin kwakwazo na tsala ƙara, Kafin na samu damar yin wani tunani akan abin da ya sameni ko neman taimako sai naji duk jikina yay collapse, idanuna sun rufe da kansu, sannu a hankali kuma na ɗauke wuta gaba ɗaya kamar zarar rai. duk yanda mai motar ya kai maƙura wajen taka burkin motar tasa dan ganin ya kaucewa Mairo abun ya faskara. yasa duka hannu biyu ya doki stearing tare da kifa goshinsa akai. yay shiru kamar ba zai ɗago ba, can ya shiga ɗago da kansa a hankali yaja dogon numfashi ya furta,"help me Jesus". muryar tasa ta fita acikin wani irin amo, sannan ya ɗago ya dubi Mairo da ya buge sheme ƙasa jini na malala, da hanzari ya buɗe motar ya fita ya ƙarasa gareta da sassarfa ya ɗago kanta, bakinsa motsi kawai yake amma ya kasa cewa komai sai bin jikinta yake da kallo da kuma jinin da ke zuba daga kanta. ya ruɗe, ya rikice, ya dabarbarce ya rasa abun da ya dace yayi, sai yaji kawai ruwan hawaye sun cika masa ido, ya janyota zuwa saman cinyarsa yana tattaɓa fuskarta, "Girl, Girl open your eyes". a sama-sama take jin maganarsa, sai dai sam bata fahimtar me yake cewa, ta buɗe lumsassun idanuwanta ta zuba ƙwayar idonta akansa tamkar tana ganinsa, sai kuma ta mayar ta rufe, numfashinta na up and down, da murya can ƙasa tace,"ruwa". bai ji me tace ba dan haka ya kai kunnensa saitin bakinta yana cewa,"say it clearly i can't hear you well". ba dan taji me yace ba sai dai ta ƙara maimaitawa dan a yanzu babu abun da take buƙata sama da ruwan, Daga haka bata sake sanin komai ba jikinta ya saki gaba ɗaya. nan take Emanuel ya kuma ruɗewa, kun san inyamuri da tsoro, gani yake da ya miƙe da ita mutane zasu yi masa caa aka duk da hanyar ba hanya ce ta jamaa ba, babban tashin hankalinsa ma kar yarinyar ta mutu. ya ɗaukota jini duk ya wanke mata fuska, ya buɗe bayan mota ya zirata aciki, hannunta ya faɗi akan ƙirjinsa ta damƙo sarƙar cross ɗin da ke wuyansa ta tsinko. ya dubi sarƙar ya dubi hannunta ya rumtse ido, da ma shi tun tasowarsa daga abuja yaji ajikinsa something bad will happen to him, daɗi da ƙarawa da yaga star ɗin jikin sarƙar tayi duhu. wawiyar ajiyar zuciya sauke sannan ya buɗe hannunta zai cire sarƙar sai yaji ta riƙeta da kyau dan haka ya barta ya rufe murfin ya zaga ya shiga yaja motar with high speed, tuƙin yake amma hankalinsa gaba ɗaya na kanta, ya miƙa hannunsa ɗaya ta baya ya riƙo nata, yaci gaba da dariving da hannu ɗaya, fatansa karta mutu, ga shi there is no any hospital nearby bare ya miƙata, haka dai har ya shigo garin ikoyi. *Comment&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *20)* *Lagoon Hospital, 17B Bourdillon Rd, Ikoyi, Lagos.* shigowarsa cikin hospital ɗin yana yin parking ko rufe motar bai tsaya yi ba ya ɗauketa ya nufi emangency da sauri, nurses ɗin da ke tsaye a emergency su na ganinsa suka turo gado su ka shiga special room da ita, Emanuel na tsaye a varander yana ta kaiwa da komowa hankali a hargitse, tsawon minti ashirin likita ya fito daga room ɗin sannan ya buƙaci nurse da ta ce Emanuel ya biyo shi office. acan office Dr Simon ke yiwa Emanuel bayanin sai anyi mata surgery aciki saboda glass ɗin da ya caki cikinta ya shige sose, kuma rashin aikin zai iya haifar da matsala babba ga yarinyar at the end ma a rasata. Emanuel ya rumtse ido gam tare da dafe goshi, ba shi da wani choice da ya wuce ya amince, tunda shi ne silar halin da take ciki, kuma ko da ace ƴan uwanta za su zo suma amincewar za su yi saboda ta rayu. ya karɓi takardun da Dr Simon ya miƙo masa, yasa hannu akai sannan ya bar office ɗin ya koma mota, yana kallon yanda wayarsa keta ringing da sunan MD da kuma Sectery amma babu kiran da yayi picking aciki, ƙarshe da ya ga kiran na neman damunsa sai ya kashe wayar gaba ɗaya. "Nurse! bring injection quickly". Dr Simon ya faɗa yana ci gaba da aikinsa. da sauri Nurse ɗin ta miƙo allurar ya karɓa yaywa Mairo, tunda aka kammala tiyatar Dr ya tsaya yana duban fuskar Mairo da ƙirjinta na tsawon daƙiƙu, sannan ya maida dubansa ga Nurse ɗin kusa da shi yana girgiza kai yace,"her health is fading. Bring the oxygen fast". yana saka mata oxygen ɗin ya ke ƙara faɗin,"Nurse prepare the CPR". wucewar awa da mintuna shiru-shiru basu fito daga ɗakin tiyata ba, ganin shirun yayi yawa tsoron da Emanuel keji ya ƙara ninkuwa, ya fito daga motar jiki a mace ya nufa ward ɗin da suke, zuwa
🏠