NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 63 of 223

abun da kake neman yi ba shi da kyau cin zarafin ƴa mace ne ubangiji ya haramta...".bata ida zancen ba yasa bakin bindiga ya gwaɓe bakin nata nan take ya fashe. "wannan ɗan ƙaramin wa'azin naki babu amfanin da zai yi anan dan haka ki rufe min baki, kiyi abunda kawai nace". "sai dai ka kasheni amma ba zanyi abunda kake so ba". ya jinjina kai sannan ya daki tsakiyar kanta da gindin bindigar, ta saki wata ƙara,"ba za ki gane abunda nake nufi ba saina dawo na sameki a yanda na barki". yace da ita tukunna ya miƙe yasa kai ya fita ya barta da ruzgar sabon kuka, tare da neman tallafin ubangiji. _"bana tunanin akwai wani abun cutarwa da zai riskeki ki kasa guje masa saboda ke ɗin ƴar baiwa ce. ba wannan macijin da kika gani kaɗai ba, har mutum sai kin so zai ya cutar da ke, dan haka duk sanda wani abu mara kyau ya riskoki ki ambaci Allah sannan kuma kiyi kamar yanda na faɗa miki"._ wannan Kalaman na Kulu suka haska acikin kaina a wannan lokaci, dan haka ban tsaya wani aune-aune da tunani ba na dunƙule hannayena tare da rumtse ido tsam. tsohon ya dawo daga shi sai sauran gajeran wandon da ya rage masa yana ƙoƙarin cire shi. sa'annan na buɗe idanuna na watsa su cikin nasa, sauyin launin da ya gani a ƙwayar idon nawa yasa shi razana yaja da baya, sai kuma ya dake ya ƙara tamkewa yana dawowa zuwa ciki, a lokacin na buɗe tafin hannuna da ya jima a damƙe aikuwa nan take wani abun mamaki da alajabi ya bayyana wanda ni kaina sai da na tsorata. kunamu ne manya kamar su na fitowa ne daga cikin jikina, sai dai ba daga jikin nawa su ke fitowa ba, nan da nan kuma suka cika ɗakin kamar a rumbunsu, gaba ɗaya sai suka yi kan mutumin kamin ya farga daga guduwar da yake so yayi tuni sun haye masa jiki, ya fara ihu tare da kiran sunan ƴan'uwan nasa akan su zo su taimake shi, wanda ke gadinsa a baƙin ƙofa shi ɗaya ya iya jin ihunsa, dan haka ya shigo ciki a guje, sai dai abunda idonsa yay tozali da shi yasa ya dakata yana jefawa Ogan tambayar meke faruwa. cikin tsananin azabar da yake ciki yay masa nuni da Mairo wadda ke rakuɓe daga jikin bango tsoro duk ya gama cikata,"ku fita da ita ba mutum bace...wayyo Allah ku nemo maganin kunama karsu ƙarasa kasheni". Yaron yace,"to Oga". ya juya da sauri ya fice ya zagaya ta baya, ya zuge rigar rumfar ta ɗaya ɓarin ya janyo Mairo waje da lallaɓawa yana faɗin ta ɓace musu da gani, sannan ya zuge rigar rumfar duka wai ko da hasken rana zai sa Kunamun su koma inda suka fito ko kuma su mutu, amma ga mamakinsa sai ya ƙara ganin su na sake shigewa jikin mutumin shi kuma yana ihun harbin da suke masa. sauran abokan harƙallar suka yo kansa anata ƙoƙarin ganin an janye shi daga cikin kunamun amma babu hali, ni kuwa a wannan lokacin ba zan iya kwatanta tashin hankalin da nake a ciki ba, dudduba ko'ina nake a jikina, domin gani nake na zama matsafiya, na durƙushe na fasa gunjin kuka dan a ganina idan mutumin can ya mutu to alhakin kisansa na kaina, bayan kuma ni ban san ta ya akai kunamun ma suka fito ba, ni dai nayi abin da Kulu kawai tace mun. ina duƙen ina faɗin Allah ka yafe min sai naji an janyo hannuna, mutanen da aka yi kidnapping ne duk suka sami daman fitowa saboda babu attention ɗin wani security akansu, hankulansu yayi kan Ogansu da ganin ta yanda za'ai su kuɓutar da shi daga kunamun da suka cika ɗakin. "zo mu tsira da ranmu". Matar da ke riƙe da hannuna ta faɗa tana jana ni kuma ina turjewa, kai nake girgizawa ina faɗa mata,"Ki tsaya a cire masa wancan kunamar ni ban san ya akai tazo ba". Matar bata saurare ni ba ta ƙara figata ganin sauran mutanen na neman tsere mana. duk yanda naso na ƙwace kaina daga hannun matar amma na kasa, ƙarshema mutum biyu suka haɗar min suka jani ta ƙarfin bala'i. haka muka nausa jeji muna ta gudu, babu hanklin kowa da ya kawo kanmu sai daga baya ne muka fara harbin bindigu. mun yi nisa sosai muka ji wasu na bayanmu na faɗar an yi nasarar harbar ƴan can bayanmu. munyi gudun kusan awa sannan aka fara rarrabewa kowa na ta kansa. ni kaɗai na fito titi ina tangal tangal ina haki, idanuna ko gani basa yi bare na san inda nake jefa ƙafata. nayi nisan tafiya ina yiwa kaina jagora, ƙafafuna kuwa sai zubda jini suke saboda irin abubuwan da na taka kasancewar babu takalmi a ƙafata, ga raɗadin zafin da ƙafar keyi min, ga ban san a inda zan iya tsayawa ba bare na zauna na huta, haka dai na shiga lalube da hannu har na kai ga wata bishiya na taɓota, na sauke ajiyar zuciya nauyayya na jingina da jikin bishiyar sannan naja jiki na sulale na zauna ƙasa. babu abunda nake buƙata a wannan lokacin irin ruwa, maƙogarona ya bushe yawun bakina ya ƙafe. cikin azama na miƙe naci gaba da tafiya a wahalce dan ban manta da maganar mutanen da muka gudo tare ba su na jadadda min akan kar na tsaya ko hutawa sai na tabbatar da na kawo inda mutane su ke, ba su san da cewar ji kawai nake ba amma ganin Mairo ya ɗauke tuni, kuma ganin ana cikin nafsi-nafsi yasa ban faɗa musu a halin da nake ciki ba, illa godiya da nai musu na kamo
🏠