NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 62 of 223

a huta kai da kasha hanya". "Gwaggo zanje asa cigiyarta ne a gidajen radio, idan nace zan zauna babu lokaci kwana ɗaya ne aka bani a wurin aiki". "tom shikenan sai ka dawo...Allah ya bada sa'a yasa a dace". yasa kai zai fita Yagana tace,"ni dai dama bance ka ban silanka ba balle ka dinga hararata har kana neman bigeni, ɓatan Mairo shi ya dameni ba karɓan kuɗinka ba". He is not in the mood ɗin da zai tsaya bata amsa amma duk da haka dai ta ba shi dariya, sai ya gimtse kawai ya wuce ɗakin mahaifiyarsa. ganinsa yasa Inna Zulai ta rasa inda zata tsoma ranta dan daɗi saboda yanda ɗanta ya sauya cikin watannin da basu haura biyar ba. ji take kamar ta maida shi cikinta, sauyin weather yasa yayi wani looking fresh, shaddar da ke jikinsa kanta ba ƙarama bace ga wata makekiyar waya da yake riƙe da ita a hannu, cikar haibarsa ta ƙara fitowa, kana ganinsa kaga wanda kuɗi suka soma zaunar masa. ta kamo hannunsa ta zaunar da shi bakin gado tana yi masa sannu da zuwa, shi ma kuma anasa ɓangaren yana ta farin ciki da ganin mahaifiyarsa. ta ɗebo ruwan sanyi a randa ta kawo masa ya sha, suka zauna su na hira duk da cewar shi ɗin dai ƙarfin hali yake amma hankalinsa ba ya kwata-kwata. yana dubanta yace,"Inna ya na ganki ke kina cikin ɗaki ga jama'a kuma a waje". fuskarta na nuna damuwa tace,"to kasan halin Kakarka ai, naga tana neman ɓatan raine shi ne nayo ɗaka kamin zuciyoyinmu ni da ita su huce". ya miƙe tsaye yana faɗin,"Allah ya kyauta". sannan ya zaro dubu biyar ya bata, ya kuma shaida mata zai je kano asa cigiyar Mairo a radio, ta bishi da adu'a da fatan nasara. yana jin Yagana san da zai fita tana faɗin,"miskili kawai". *** yau kwanan su Mairo biyar a hannun kidnappers, kullum kuma sau ɗaya ne ake kawo musu abinci shi ma biredi ne da zuma za su tsoma suci, daga nan sai washe gari su da ƙara ganin wani abincin, sai uban ruwa da ake ɗirka musu, bayin Allah duk har sun saba da hakan. Mairo dai gaba ɗaya tafi kowa lalacewa saboda yanda taga anata ɗaɗewa ana barinta, wasu an biya kuɗin fansarsu wasu kuma an gaji da ajiye su ne sai a siyar, ko kuma dan rashin imani sai a kashe su. Matar da ta saba da ita ƴan'uwanta sun zo sun fansheta, shi yasa bata jin daɗin wurin gaba ɗaya, ita yanzu jira take kawai su kasheta ta huta, domin ta jima da sallamewa da rayuwa tun a sanda taji adadin kuɗin da za a bayar kafin a bayar da ita, da ma ita tasan bata da me biyan wannan kuɗin, dan kaf danginsu babu me shi, yanzu tashin hankalin da aka sasu aciki ma sa iya cinye kuɗin a magani. la'asar ɗin yau su na zaune aka banko ƙofar ɗakinsu, su ka zabura suka zubawa ƙofar ido, in da sabo yaci ace sun saba da su to amma sanin cewar basa shigowa su fita ba su kashe rai ba yasa basa samun nutsuwa da zuwansu, kuma yau dan mugunta ma ko abinci har yanzu ba'a basu ba. su uku ne su ka shiga su na saita kan bindiga, a tsorace kowa ya dinga ja da baya musamman Mairo da ke daga bakin ƙofa. Ogansu ya nuna wani Dattijo ya manyanta sosai yace,"taso". sannan ya kalli Mairo yace,"ke kuma ki shirya". sannan su ka fice tare da wancan mutumin. manyan mutanen da duk suka san nufin maganarsa akan Mairo sai su ka fara hawaye. ta kalli wata sabuwar mata da aka kawo jiya da ta fara sabawa da ita tace,"Yaya ina za su kaini?". ta rungumeta tace,"nima ban sani ba". hankalinsu ya karkata kan wani mutum da ya kalli gabas ya ɗaga hannu yana adu'a, "ubangiji Allah ka dubi wannan yarinya ka ceceta daga hannun azzaluman nan, Allah kar ka basu ikon keta mata haddi". ya duƙar da kai tare da fashewa da kuka. kamin su ƙara motsi aka kuma banko ƙofa, wanda ya shigo ya kalli Mairo acikin kaushin murya yace,"taso muje". jikinta ya hau rawa saboda tsoro, ta ƙundundune jiki tana kuka tana ba shi haƙuri, uwar tsawar da ya sakar mata yasa ta gimtse baki, ya ƙaraso ciki ya figo hannunta su kai ƙofa, mutumin nan da ke ta bin Mairo da kallo yana jin inama ace yana da damar da zai ƙwaceta yace,"dan Allah ku tausaya mata yarinya ce ita...ku ƙara haƙuri iyayenta za su zo su fansheta amma karku lalata rayuwarta". wani mugun kallo ya juyo yaywa mutumin yana kai sigari bakinsa ya zuƙa, ya saki ƙwafa ya juya za su ƙarasa fita mutumin ya ƙara cewa,"Ƴata kiyi ta ambaton Allah cikin hukuncinsa da ikonsa za ki kuɓuta insha'Allah". yana rufe baki mutumin ya saita ƙirjinsa ya ba shi harbin bindiga take ya mutu, shi kuma yaja Mairo da ke turjewa ya fita. cikin wata rumfa da suka kafa na leda ya nufa da ita, yana zuwa ya tankaɗata ciki tare da cewar,"Oga gata nan a huta lafiya". tsohon ya taso ya nufo gareta fuska babu annuri, yay tsaye kanta yace da ita,"tuɓe". ya faɗa murya a ɗage. take sabbin hawaye suka shiga kwaranyowa Mairo, tsoro ya ƙara ninkuwa a zuciyarta, tana girgoza masa kai tana faɗin,"a'a". yasa ƙafa ya take mata ƙafa cikin kakkausar murya ya kuma ce mata,"kamin naje na dawo ki tabbatar da kin tuɓe idan ba haka ba kuma zan kasheki". ta rumtse ido ta buɗe kafin ta sami ƙwarin giwar ce masa,"Ya Kabiruna ya faɗa min
🏠