matuƙa, dukansu sun kasa samun stabilify, sam sun kasa yarda Mairo ta ɓata ɓat, har gwara Kulu ma na iya jurewa, amma Gwaggo kuwa tun da rana ta faɗi ya tabbata babu Mairo babu dalilinta, shikenan ta yanke jiki ta faɗi, shikenan duk wani budget nata akan Mairo ya rushe, nan da nan aka ɗauketa zuwa asibiti, kuma a lokacin ne Kulu ta fito dan ta sulale ta gudu amma halin da Gwaggon ke ciki yasa dole ta janye ƙudurinta domin idan tayi hakan tayi butulci, daga ita sai Inna Zulai aka bari a gida, bata da aikin komai sai share hawaye lokaci zuwa lokaci.
Gwaggo ce kwance kan gadon asibiti, a kallo ɗaya zaka gane fitar hayyacin da tai, amma dai for now ta fara regaining conciousness, likita ya shigo ya auna BP ɗinta sannan ya kalli Malam yace,"to Alhamdulillah jininta ya sauka, zuwa Magrib zamu iya sallamarku sai dai a kula dan Allah wajen kiyaye damuwarta, and then da shan magani in time saboda gaskiya lafiyarta na cikin haɗari". Malam ya ɗaga masa kai da cewar,"tom za'a kula...sannu da ƙoƙari".
zuwa Yamma aka sallamesu suka koma gida, tun bayan dawowarsu kuma gida ya ɗinke da jama'a sai shige da fice suke ana jaje kamar gidan mutuwa, da waɗanda su ka zo jaje tun ranar farko da masu dawowa yanzu dan duba jikin Gwaggo sai gidan ya zama babu matsaka tsinke. Yagana duk wanda yay mata jaje bata iya cewa da shi komai sai kallo da ido, bini-bini kuma sai ta sa gefen mayafi ta matse ƙwalla. Matar Liman tazo ana gaggaisawa ta tambaya ko waɗanda su kai garkuwar da ita sun kira waya?, Amarya tace da ita,"ai Hajiya babu lallai Kidnappers ne tun da har yanzu babu wani saƙo ta waya, munfi tunanin ko ƴan yankan kaine suka saceta, yanzu kwanciyar hankalinmu ma bai wuce ace ko gawarta ne a gani ba zamu fi samun nutsuwar ruhi". Hajiya Saratu ta girgiza kai cikin jimanta al'amarin,"to ubangiji dai shi ya san a halin da yarinyar nan ke ciki. Allah yasa ta faɗa hannu na gari...in Allah ya yarda za'aita adu'a dan yanzu haka ma tun jiya Malam yasa almajirai suka sauke mata alƙur'ani". Yagana ta face majina cikin muryar kuka tace,"ai duk wanda ya ɗauke yarinyar ba zai gama da duniya lafiya ba, kuma sai Allah ya isar mana tsakaninmu da shi...fatanmu Allah ya tsareta ya kareta a duk hannun da ta faɗa".
wata cikin ƴan jajen tace,"kwanaki mu ma fa haka akayi a layinmu, daga fitowar yaro da daddare ke tun ana zuba ido ana saka ran zai dawo shiru har yanzu kusan wata biyu kenan, iyayenma sun cire rai da shi tun da babu irin neman da ba'ai ba, cigiya har gidan talabijin". Marka me koko tace,"ai waɗan nan azzalumai Allah dai yay mana maganinsu shi ne adu'a kawai".
Sunusi ya shigo rungume da buhun shinkafa, Lukman na biye da shi ɗauke da kwalin taliya biyu da na makaroni ɗaya, sai ga Mu'azzam shi ma ya shigo da galan ɗin manja. kafin Amadu ya mara musu baya bakinsa ɗauke da sallama, sai dai kana ganinsa kaga wanda ke ɗauke da matsananciyar damuwa, a tsaitsaye ya gaida jama'ar da ke tsakar gidan sannan ya wuce ɗakin Gwaggo. kishingiɗe jikin pillow ya taddata, ya ƙarasa gabanta ya zauna, har tsawon wasu daƙiƙu bai ce komai ba sannan ya buɗe baki kamar mai shirin yin kuka yace,"sannu Gwaggo, Allah ya ba ki lafiya". ta amsa da,"amin Amadu, ashe kana tafe". "ehh da yake ma tafiyar mota ce shi yasa na makara". Sai Gwaggo ta fashe da kuka,"Mairo dai ta ɓata, ban san a wani hali take ciki ba yanzu". yay saurin kawar da fuskarsa dan ba ya son ganin hawayenta, ya lumshe idanunsa da su kai jazur ya buɗe kana yace,"su da ba fita suke ba dan ubanta gidan uwarwa taje a ranar?". yay tambayar a zafafe. Gwaggo na goge hawaye tace da shi,"to ai ita kasan bata rabo da gidan Yagana, laifinma dai nawa ne kuma duk da haka Allah ya riga ya shirya faruwar hakan, kuma ita Yagana tace lafiya lau su kai sallama da ita ta wuto gida, to ƙarshe sai da safe da ana laluben hanya aka tsinci ledar dubulan ɗin da ta bata a hanya, ananne ma aka tabbatar ɗauketa akayi". yana huci yace,"ni dama gidan Yagana ba son zuwanta na ke ba tunda ba wani iya kula da ita za tai ba...ita ma shashasha da ta ga daren yayi ai sai ta haƙura ta kwana acan". Gwaggo tace,"ko ɗaya ba laifin Yagana bane kasan Mairo ma da shegen taurin kai, kaifi ɗaya ce". "duk da haka akwai laifin Yaganar". Yagana ta faɗo ɗakin tana matse ƙwalla ta hau sababin,"yo ni dama tunda akace min zaka zo garin nan na sallama babu wanda zaka ɗorawa alhakin ɓatanta sai ni, to ni dai sai dai nace Allah ya saka min tunda yana ji yana kuma gani, ai kowa shaida ne ina ƙaunar Mairo, ta ya za'ai nasa a saceta, me ta tare min, kuma ni wallahi ma bani da wannan matacciyar zuciyar da zansa hannu a cutar da rai". tunda ta fara maganar Amadu ke kallonta, har kuma ta gama bai ce mata ƙala ba, sai da ta gama sharar hawaye sannan ta dube shi da cewar,"yanzu kuwa ɗan nan ba zaka nemi yafiyata ba?". ko kallonta bai ba ya miƙe yana zura hannu a aljihun wando, ya zaro ƴan ɗari biyar guda shida ya miƙawa Gwaggo, ta amsa tana saka masa albarka. "yanzu ina zaka je? da kayi zamanka anan k