iji ko kaɗan, Gwaggona ni ta fara haifa sai dana shekara goma ciff a duniya sannan ta ƙara samun arziƙin haihuwa ta haifi Basma, Gwaggo da kanta ta shawarci Baba ya ƙaro aure, dan tun bayan haifata da ta yi taga haihuwa ta tsaya mata tsawon shekaru daga ita har Inna Zulai, ga Baba da son ƴaƴa dan kullum a adu'arsa Allah ya ƙara azurta shi da ƴaƴa na gari yake duk damu goma sha biyar da Allah ya ba shi.
Aisha ita ce mata ta huɗu a wurin Baba wadda muke kira da Inna Amarya, ƴar gidan sarkin noman garinmu ce, Tsakanin Inna Amarya da Gwaggona sam babu wani abu wai shi kishi, illa iyaka mutunta juna da suke. shekaru kusan goma sha biyu da Inna Amarya ta shafe a gidanmu bata taɓa haihuwa ba har yau, ko ɓarin ciki wannan, kuma dama tun bayan aurota babu jimawa na koma wajenta da zama, a ganina ba jin daɗin zaman wurin Gwaggona nake ba, dan ita takan hantare ni a wasu abubuwan da nake ko tayi min faɗa, amma ita kuwa Inna Amarya zallar gata ne take nuna min da sangarta, dama tun a lokacin da ta cewa Gwaggona zan koma wajenta Gwaggo tace mata ai gani nan in dai zata iya da halina ta ɗauka.
bayan auro Innata Inna Zulai taci gaba da haihuwa dan yanzu haka ma wani cikin gareta, duk da ƴaƴa goma sha ɗaya da ta mallaka tace har yanzu bata gama cin gida ba.
To tsakanin Inna Amarya ne ma da Inna Zulai ake samun ƴar tsama, dan ita Inna Amarya bata barin ta kwana, ko ba ita aka taɓa ba in har za'a taɓa Gwaggo to sai inda ƙarfinta ya ƙare, ita kuma Inna Zulai da shegen habaicin bala'i da bata gajiya da yinsa, martani kuma sai dai idan Inna Amarya bata ji ba, darajar Ya Amadu kaɗai Inna Zulai ke ci wataran har Inna Amarya ta ɗaga mata ƙafa, dan Ya Amadu mutum ne, idan baka sani ba zaka rantse kace Gwaggona ita ta tsuguna ta haife shi har Ya Kabiru, Ya Amadu sam bai ɗauko baƙin halin uwarsa ba, kuma baya goyon bayanta akan abubuwa marasa kyau da take, hasalima shi mai yawan yi mata nasiha ne wataran har ya tarasu duk ukun yay musu nasiha, idan ya gama ta kaɗe zane tace ita dama ai ta jima da sallama shi, dan ba tun yau ba ta gama gane Gwaggo ta shanye mata ɗa, to saboda haka yaje gashi ga Gwaggon nan, da ace shi ɗaya ta haifa sai tayi kuka, to amma Allah ya bata da yawa, dan haka ba zata bari takaicinsa ya kasheta ba. Ya Amadu yana kuka da wannan halin na mahaifiyarsa sosai, sau tari yakan zubar da hawaye agaban Gwaggo sai dai Gwaggo ta lallashe shi ta ƙara bashi haƙuri, tace masa yaci gaba da haƙuri duk lalacewarta uwa ce, yaci gaba dayi mata adu'a Allah ya ganar da ita.
Gidamu ginin ƙasa ne daga ciki, daga waje kuma ginin bulo wanda babu ko fulasta ajikinsa, shi ma ginin bulo ɗin anyi shi ne babu jimawa, dan waccen shekarar ne lokacin da Ya Amadu yabi Yayan abokinsa lagos ya tayashi aikin company ɗin mahaifinsa acan, to a wannan lokacinne Ya Amadu ya dawo da shatara ta arziƙi da Baban Joseph ya haɗa masa, Kuma ko da ya tashi dawowa Obi abokinsa shi ya dawo da shi ya kawo shi har ƙofar gida a danƙareriyar motar gidansu, shi ne har aka rushe ginin ƙasar ƙofar gidanmu aka tada na bulo, da shi dasu Ya Kabiru suka yi aikin dan ko ƙwandalarsu basu kashe ba a wurin neman me aiki, Sannan ni da Sadiya da Adawiyya da Lukman ya kaimu makarantar boko Government Secondary School Bichi, ya kuma ƙarawa Baba jarin itacce, itama mahaifiyarsa ya ƙara mata jarin Mafitai da ta-ke siyarwa, sannan ya sarowa Gwaggona kwalaben manja yace ta-ke saidawa, sauran abunda ya rage masa kuma ya biya kuɗin koyan ɗinkin da ya ke zuwa.
A wannan lokacin dai gidanmu an godewa Baban Joseph da kuma yi musu adu'ar samun hasken musulunci, ko ni idan naje makarantar boko sai na shiwa kafirin nan albarka, na kuma yi masa adu'ar Allah yasa ya musulunta, domin ta silarsa yau gani a makarantar boko da naketa fatan kasancewata aciki.
To ita dai Gwaggona da Yagana(Kakarmu ta wurin Uba) sam basa son hulɗar Ya Amadu da Obi kai harma da shi Joseph ɗin da ya ke ɗauka matsayin uban gidansa, ayanda ta-ke nunawa ta tsani ahalinsu gaba ɗaya dukkuwa da basu taɓa ganin ko mutum ɗaya daga cikinsu ba, acewarta Obi ba abokin hulɗa bane karya dulmiyar mata da ɗa, ko kuma shi Joseph ɗin ya cutar da shi, dan arna abun tsoro ne, Baba ya kan fahimtar da ita akan alaƙar tasu ba wani aibu bane, ta dalilin hakan ma sai shi Amadu ya zama silar jawosu cikin musulunci, Gwaggo dai ba zata tanka ba illa iyaka taɓe baki da takeyi, kusan kuma duk sanda Ya Amadu zai ce mata Oga Joseph na gaisheta sai tayi kunnen uwar shegu da shi, idan ya kuma magana tace ai taji, ranar nan kuma tace masa ita dai wannan gaisuwa da ake kawo mata kusan kullum tunda babu tsiyar da ta-ke ƙara mata a ƙyaleta, ko shi Joseph ɗin ya riƙe gaisuwarsa ko kuma shi Ya Amadu yake riƙe aiken saƙon iyaka shi, wani lokaci da sukayi waya da Oga Joseph tana zaune a wurin sai Ya Amadu yake ce masa itama Gwaggo na gaida shi, da alama shi Joseph ɗinne ya fara tambayarta, Ya Amadu na gama wayar ta dube shi tace ni Amadu a tarbiyar da nayi maka ban koya maka ƙarya ba, k