sun fito daga cikin dajin hannayensu riƙe da wuƙaƙe da kuma bindiga, a kallo ɗaya za kaiwa halittar fuskarsu ka san baƙaƙen azzalumai ne na ƙarshe, waɗanda babu ko ɗison imanin tausayi a zuƙatansu. ɗaya daga cikinsu ya dubi wanda ke riƙe da Mairo murya a shaƙe yace,"cika aiki ya ne?, ko firgici yasa ta mutu ne?". wanda aka kira da cika aiki ya bushe da dariya tare da yasar da Mairo a ƙasa yace,"haba bandalago zunubin ai sai yayi min yawa, kai kasan duk girman sheɗancina ina tsoron mutuwar rai a hannuna...bata mutu ba ta nan da ranta kawai dai an sata dogon bacci ne ehh yane ka gane kawai". dukanninsu kallonsu ya koma ga Mairo da ke yashe a ƙasa kamar gawa, sanadin jefar da ita ta bugi dutse goshinta ya fashe jini sai tsiyaya yake. "kam bala'i jini naga yana zuba". cewar ɗayan cikinsu. "to Allah na tuba kai yau ka fara ganin zubar jini irin haka, kamar ba'a sha kashewa a gabanka ba...ku ɗauketa kawai kusa kai". haka ɗaya ya saɓi Mairo a kafaɗarsa, kai ba ka ce mutum ya ɗauka ba, dan ɗaukar irin na dabbobi ne da mafarauta ke musu, suka nausa can tsakiyar dajin su na ta tafiya kamar ba za'a ƙare ba, kamin su sake ɓullawa wani dajin shi ma suyi tafiya me nisa kan su yada zango a wata bukka, su na isa suka jefar da Mairo kamar matacciyar dabbar da suka farauto, mutumin da ke zaune kan kujerar ƙarfe yace,"wannan ce yarinyar?". "ehh oga ita ce". "ok, to ku haɗata acikin waɗancan kajin, naga biyar ta kawo kai, idan muka yi sallar asuba sai mu wuce amma kuyi da sauri dan ina so mu shiga gari da wuri saboda aikin gobe me zafi ne". suka amsa umarnin ogan nasu da, "yanda kace Oga". sannan su kai gaba, sai kuma tsamurmurin cikinsu ya dawo da baya yace,"amma Oga na ke ga kamar mu ɗau hanya tun yanzu ko, dan naji fa ance goben nan akwai tsaro me tsamari a hanya". Ogan ya ɗaga masa hannu,"ba case, aikinmu ba ya da matsala da jami'an tsaro".
su na idar da sallar asuba suka shiga mota da yara sunfi biyar kuma har wannan lokacin Mairo bata farfaɗo ba, sannan su ka ɗauki dogon titin da babu kwana balle kwane-kwane, tafiyar awa shida ta kaisu ga in da suke so, nan ma dai daji ne sai dai bai kai wancan dajin hatsari ba, kuma shi anan bukkoki sun kai shida saɓanin can da bukka ɗaya ce, haka aka taso ƙeyoyinsu har zuwa bakin Babbar bukkan, sannan duk mabiyan da ke tare da su suka tsaya, Wani wanda da alamar shi ne babba cikin ƴan bindigan da ke tsaye bakin Bukkar da bindigarsa zungureriya ya kalli waɗanda suka kawo su Mairo yace,"ita wannan me yasa buku ɗaure mata ido ba". "hoda ce ke aiki ajikinta". ya girgiza kai sannan ya sunkuya ya shiga bukkar babu jimawa kuma ya fito yana takewa wani tsohon farin bafulatani baya, wanda alamu ya nuna shi ne babba a tsangayar ta su, Tsohon ya zauna kan kujerarsa su kuma duk suka zube gwiwoyi ƙasa. ya dube su kamin yace,"kun makara". "bamu taso da wuri bane".suka ba shi amsa. ya jinjina kai sannan ya kai dubansa ga kajin da suke ikirarin an kawo, yay musu kallo ɗaya bayan ɗaya sannan yace,"amma ita wannan sumammiyar da ka gani daga gidan yunwa ta fito...ko da yake koma dai yane dole za'ai aman kuɗin karɓarta, ku tasheta su kuma sauran ku kunce musu ido". aka kuncewa sauran ido ita kuma Mairo anata zabgeta da mari amma bata farka ba, hakan yasa tsohon ya saki harbin bindiga nan kake ji duk waɗanda akayi kidnapping ɗin sun cure wuri ɗaya jiki na kyarma, take kuma ƙarar harbi na biyu da ya kuma saki ya farkar da Mairo cikin ɗimauta da gigita, ta tafi ta rarumo ɗaya daga cikinsu ta cukwikwiye jikinsa ta fashewa da kuka tana faɗin,"Ya Kabiru kazo ka ƙwaceni daga wurinsu kar su cutar da ni". maganarta ta haɗiye saboda yanda wanda ta cure a jikinsa ya damƙo gashin kanta ya barƙalar da wuyanta, tsananin azaba yasa ta buɗe nauyayyun idanunta a wahalce ta dube shi da irin dishi-dishin da take gani. ya doka mata tsawa tare da cewa,"yi mana shiru". sai kuma ya sake ce mata,"wa ye Kabiru?". jiki na rawa ta shiga juya masa kai,"babu kowa a firgice nake ne". tayi maganar a rarrabe. daga nan kuma duka aka tasa ƙeyarsu zuwa wani ɗan ƙaramin gini me ɗaki ɗaya da mitsitin windo sai banɗaki da ke ciki, ana saka su aka janyo ƙofar aka rufe. anan Mairo taga ashe ba ita kaɗai aka sato ba, su birjiki sun kusa kaiwa talatin daga manya har ƙanana kusan Manya ma sunfi yawa, dan idan tana iya gani sosai kusan ita kaɗai ce ma budurwa a wajen. ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka me ƙarfin sauti, nan wata dattijuwar mata da ke daga can nesa da ita ta taso tazo kusa da ita ta zauna, ta ɗago kanta tasa hannu tana goge mata hawaye.
"kiyi shiru ki daina kuka kinji ƴata, adu'a za ki yi Allah ya fitar damu daga wannan musiba amma kuka ba namu bane. idan kika ci gaba da kuka suka jiyo ki za su zo su harbeki ne suyi miki irin ta wancan yaron". matar ta faɗa tana nuna mata wani yaro ɗan kimanin shekara takwas yashe a ƙasa."kin gansa kuka yake suka zo suka harbe shi kuma har yanzu ba su ƙara bi takansa ba alhalin sun san da cewar ya mutu". Kukan da ya ci ƙar