NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 57 of 223

nan sai ce yayi shi baiga ma mace ko ɗaya a gidan ba. Allah sarki ashe rabon akan Mairona yake". tai zancen tana janyoni jikinta sannan taci gaba da cewa, "idan ku ka ƙara haɗuwa ya tsaida ke ki tsaya ki saurare shi dan Allah, muddin kika samu yace zai aureki to wallahi Allah ya taimakeki, dan kin samu mijin kerewa sa'a". ni kam na gaji da jin zancen nata, dan haka na taƙaita shi,"to Yagana naji, insha'Allahu zan saurare shi ɗin naji batunsa". "yauwa to Allah yayi miki albarka, wallahi tallahi Mairo ina sonki, kaf cikin jikokina albarka, Allah ma shaidata ne". nace,"nima Yagana ina sonki". ban bar gidan Yagana ba sai da akayi sallar isha lokacin ƙarfe takwas da mintuna, babu yanda Yagana bata yi dani ba akan na kwana naƙi nace ni gida zan tafi, tace to nafi ɗin tunda cinyeni zata yi cikin dare. nace mata,"ni bance ba, inda dai zata bani dubulan to zan kwana". baiwar Allah haka kuwa ta tashi ta ɗauko min kwanon gaba ɗaya tace gashi na cinye dama tunda aka kawo ni ta ajewa saboda ta san ina sonsa, na karɓa nayi godiya nace amma fa duk da haka ni tafiya zanyi ba zan kwana ba na sauya shawara. "Mu kwan lafiya Yagana, gobe ba zaki ganni ba sai mun dawo daga asibiti". tai min shiru kamar bada ita nake ba. sai da zan fito sannan tace,"ai gwara ki tafi ni dama ba jin daɗin zamanki nake ba, tunda ke hannun ta'adi gareki...shi yasa ɗazu ko da kika shigo ina sane na baiwa banza ajiyarki saboda shegen kwaɗayinki, ki gani ba za ki iya kauda kai ba sai roƙa". tafiya nake sauri-sauri gudu dudu duk a tsorace saboda yanda garin yayi shiru, baka jin komai sai kukan tsintsaye a sararin samaniyar subhana, ko hasken farin wata ma babu kasancewar ana hazo, faran-faran nake jefa ƙafafuna burina bai wuce naji na isa gida ba. na waiga hagu da damana naga babu kowa sai ni kaɗai sai kuma kukan karnuka daga can nesa, hakan yasa na ɗage zanina na arta ana kare, gudun da kona minti biyu banyi na nayi tuntuɓe jina kake a ƙasa tim na kifa, kafin na yunƙura na ɗago naji an toshe min hanci da baki an ɗagoni an sureni sai cikin mota. matuƙin motar ya bawa motar wuta da gudun gaske suka bar unguwar, ni dai ƙwala ihu nake ina neman ɗauki sai dai babu mai iya jina, dan duk motar a zuge take da glashi. "Babana, Innata, Gwaggona, Yagana". sunayen da nake ta kwaɗawa kira kenan cikin ihun murya dana tabbatar dai saceni aka yi. wanda ke gaban mota ya waigo ya saita goshina da bindiga yana cewa,"ko ki mana shiru ko kuma na ɓula kanki". cikin dakiya da tsiwa nace masa,"ba za'a yi shirun ba, idan ka fasa kuma kai ba ɗan halak bane...wallah ni dai ku barni ko na tara muku jama'a". na kusa dani ya shaƙi wuyana iyakar shaƙa yace, "oh bakinki ba ya mutuwa kenan, oga harbeta". da naga da gaske mutumin harbeni zai yi jiki na ɓari na runtse ido na shiga bashi haƙuri, daga haka naja baki na gimtse sai shashsheƙar kukana da ke tashi ƙasa-ƙasa. babu yanda ba suyi dani ba akan nayi musu shiru naƙi, mai tuƙin yace, "ku sumarta kawai". ina kallo na gaban ya kuma waigowa ya baɗo min hoda, take ganina ya ɗauke gaba ɗaya, shi ma jin nawa nema nake na rasa shi gaba ɗaya. *Comment & Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *18)* kamin ɗaukewar jina gaba ɗaya ina jin a san da na kusa da ni ke waya yana cewa,"mun ɗauketa kamar yanda aka ba da umarni, yanzu haka muna kan hanyar barin garin gaba ɗaya". yay jim kamin ya sake cewa,"babu wani abu wai shi ɓacin rana acikin aikinmu, mu nasara ko da yaushe bata barinmu...idan muka ce za muyi aiki to kawai an gama an wuce wurin, sai dai fa kuɗin fansarta dole zai tashi daga farashin da muka sa, dan naga yarinyar tafi ƙarfin farashin miliyan ashirin". gabana ya yanke ya faɗi rasss saboda tsananin tashin hankali, da gaske yau ni Mairo aka yi kidnapping?, abun da nake ji a labari, kuma har ake ambato waɗannan maƙudan kuɗin dan fansata, bayan Babana ba shi da su ba kuma shi da me ba shi?, kafatanin dangin uwata da na ubana su kansu aka haɗa ba su kai iya adadin kuɗin ba, gatanmu a rayuwar nan shi ne Allah, shi ke rufa mana asiri ya kuma suturtamu, babu makawa Babana yaji batun wannan kuɗin to la shakka cigaban rayuwarsa abu ne mai wuya. wasu zafafan hawaye suka shiga sitiri a saman fuskata kamin daga bisani na ɗauke wuta gaba ɗaya. tafiya ce me nisan gaske mutanen su kai, tafiyar da kamar ba zata ƙare ba, aƙalla sun ɗauki kusan awanni takwas zuwa tara kamin su iso wani titi da babu gimlawar komai sai ƙarar iska da ke kaɗawa. wajen ƙungurmin daji ne da tsirrai ke rayuwa wurin, motarsu bata jima da tsayawa ba a wurin sai ga wasu mutane dukansu a tsamure
🏠