Gwaggo suka faɗa babu sauyi. taya akai furucin na su yazo iri ɗaya?, me yasa su ke cewa nayi karatu saboda kaina ɗaya?, na rasa gano amsar taƙamaimai. na buɗe lumsassun idanuna na dubi Yagana, ita dai sam bakinta ba ya shiru, idan ba ta waƙa to tana mita, ko da yake tace ita ko ya ta rufe baki bata magantu ba to idan ta buɗe sai taji bakin ya buga, dan haka bata ga dalilin da zai sa ta dinƙa rufe baki ba haka kawai bayan Allah ya tsaga mata shi dan tayi magana.
"Yagana dan Allah ni kam ku barni na tafi makaranta tunda naji sauƙi haka". ta kalleni tace,"kin san mun san ciwonki saɓanin ke da baki sani ba, saboda haka ki cire ran tafiya makaranta nan kusa muddin ba warwarewa kika yi gaba ɗaya ba". na miƙe zaune kamar zansa kuka na shiga roƙonta Allah da Annabi amma ƙarshe matar nan sai tasa auduga ta toshe kunne wai lokacin saka maganin ciwon kunnenta yayi alhalin kawai dan ta gaji da roƙona ne, haushi ya ƙumeni, banda ina sonta ina tausayinta da sai nace Allah yasa ciwon kunnen ya kamata tunda shi take fata.
na ƙaraci kumburina da kukana na miƙe na fita na iyo alwala. gefin magariba muna hira da Yagana, rabin hankalina na kanta rabi na kan dubulan ɗin dana gaji da haɗiyar yawu akansa, wanda a dalilinsa ne akaƙi kulani ɗazu aka kuma fake da cewar ba'a san na shigo ba har ana ɗora min laifin rashin sallama saboda kar a bani. ga labarin da take bani akan wani tsohon bazawarinta na neman ƙullar min da ciki saboda dariya, wai ita tsabar ta iya yiwa maza shagwaɓa har kukan jarirai take yi.
ina ta dariya na miƙe na shiga uwar ɗakinta, ina ƙara tunzurata da labarin, laluben inda ta ɓoye dubulan ɗin nake amma na rasa, ban san da cewar kwanukan dana taɓa basu zauna da kyau ba a ma'ajiyarsu , sai jin ƙarar murfi nayi ya faɗo ƙasa, ai ban kai ga runtse ido ba Yagana ta rafko sallallami,"Allah yasa ba ɓari kika min ba". nace,"ɓari sai kace bana gani, kwanukan da kika jera ne ba'a dai-dai ba suka rikito". "umm to ya zanyi yarinyar nan ce Zubaida da bata iya aikin kirki ba, gyara minsu dan Allah...amma kiyi a hankali akwai ajiyar mutane a wurin kar ki ɓata". nayi gajeriyar dariya, Yagana ikon Allah, wai ajiyar mutane tama maidani wata ƙaramar yarinya.
a can ƙarƙashin kayan wankinta na ɗauko kwanon dubulan ɗin ta ɓoye shi. "me kike yi aciki ne na jiki shiru?, karfa kiga kayan mutane ki taɓa, ajiya aka bani kayan ƙawata ne Hajiya Fatsima". "babu abunda na ke taɓa miki Yagana ke dai ci gaba da bani labari ina jinki". nace da ita yayin da nake cika bakina da shi. taci gaba da ce min,"yanzu kinga shi Amadu duk wadda ta aure shi sai ta kamu da hawan jini saboda rashin maganarsa da sakin fuska. shi kuma Kabiru duk wadda ta aure shi ciwon zuciya farat ɗaya zai kamata saboda kishin mata da za su ke rububi akan mijinta...Allah na tuba ance babu kyau amma wannan yaro yanda kika san shi yayi kansa, a gidansa dai aljanun ƴaƴa na kyau za'a ke haifa". tana ta labarinta ina ta kai dubulan baki, taji shiru ta kira sunana na amsa. "au na ji kinyi shiru". "ba komai ina jinki ci gaba, ina linke miki kaya ne". bata dai yarda dani ba sai da ta shigo, tana shigowa kuwa ina naɗar wani ina ƙullewa a leda, mu ka haɗa ido na basar. "amma ke kuwa da jan magana kike, ke idan baki taɓa abunda ba naki ba sam ba kya jin daɗi. dubulan ɗin nan fa ba wani yawa gare shi ba aka kawo min kina gani bai fi nayi masa ci ɗaya ba, amma ba za ki barni da shi ba kin tasa a gaba kina neman ganin bayansa". "au ashe naki ne?". "nawa ne mana ɗazu Saratu tayo min aikensa, ni ban fiya so akesa min ido akan abuna ba wallahi". ina ƙunshe dariyata nace,"kuma da kika ce ba naki bane". bata bani amsa ba ganin ba cin hankali nake masa ba, tayo kaina na miƙe na fice da gudu, ta hau sababin ita shi yasa bata so idan nazo na shigo mata ɗaki saboda ni da ɓera halinmu ɗaya.
muna zaune can tace da ni,"ke ɗazu da kika shigo fa ina kallonki kamar a firgice kike, me ya faru?, naƙi bi ta kanki ne gudun kar ki ce sammin". nace mata,"Salmanu ne ɗan gidan Liman ya biyoni". ta saki baki tana dubana, "to shi ne kuma sai akayi ƙaƙa?". nace mata,"ni ban san me zan masa, ya dai ce na gaisheki". tace,"to Allah yasa biki rashin hankali ba dan nasan halinki". ina ɓata rai nace,"rashin hankalin me kuma Yagana?". "akwai wani rashin hankali da ya wuce kiƙi sauraronsa, ke kin san yanda manyan mutane keji da yaron nan a garin nan kuwa, kika same shi ai ba ƙaramin auna arziƙi kika yi ba, wallahi abun sam barka ne wannan yaron ya shiga cikin zuri'arka". da mamaki na ke dubanta nace,"to wai ke Yagana ce miki akai yace yana sona?, kawai fa ce yayi ya rakoni saboda yaga layin ba kowa". naga ta ɗaga hannu sama taiwa Allah godiya, na tambayeta mene tace ba komai, kamin ta ce min,"jiya jiya Kakarsa ta gama yi min ƙorafin Salmanu yaƙi sauraron wata mace, abun duk damunsu yake su na ganin kamar ko bai da lafiya ne, ga shekaru su na ta ja. tace har gidan ƴan'uwansu akai kai shi gidan kyawawan ƴan mata ko zaiga wacce tayi masa amma yaron