NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 55 of 223

hannu take tana faɗin, "kai jama'a ni Rakiya yau na gamu da gamona. yanzu ke wannan abar yaushe kika shigo min gida?, ni dai Rakiya inda raina nata ganin abunda ke neman fin ƙarfina akan jikokin da buwayi gagara misali ya bani...yanzu banda abunki Mairo ai sai kiyi sallama da za ki shigo na san da wani ran bayan ni, to inma ciwon baki kike ai kya min alama, amma haka kwatsam sai na tsinceki shememe akan shimfiɗata kamar gawa. ba kiji yanda na tsorata na firgice ba ca nake ma gamo nayi, Allah kayi min magani amma dai magana ta gaskiya kam an shiga da hakkina". takaici bai barni nace mata komai ba naja guntun tsaki na koma nai kwanciyata. "tsaka ma da tayi tsaki ga yanda aka maida ita nan balle ke, idan halin ƙwarai ne kici gaba da yi. ni dai wallahi har nayi tashen ƴan matancina ban raina na gaba dani ba...kuma Adamun zai zo ya sameni naji idan shi ya ɗaure muku gindin yi min irin haka. ke ni banma san san da kika sauya daga mutuniyar kirki ba, da babu ruwanki gwanin sha'awa amma yanzu nema kike ki fanɗare". na katse mitar tata da cewa,"wai sallamar da nayi a wani sashin jikin naki ta sauka da kunnenki ya gagara jina?". ta juyo daga fitar da zatai cikin girmama zancena ta ce,"sallama?, aina?, to ni kam ban san kinyi ba. tun da nake zaune a tsakar gidan nan banga shigowar wani bil'adama ba da yay sallama ba, kinga fa da ilimina na san darajar sallama. kawai ke dai ki bar borin kunya kice biki yi ba, to na yafe miki a wuce wurin, amma kya ƙyala min sharrin naji naƙi amsawa, salon kija a rubuta min zunubi". saboda a zauna lafiya na huta da jarabatarta nace,"to kiyi haƙuri". tace,"to shi ne zance amma yarinya kya tsaya yi min musu bayan kin san kece da rashin gaskiya". "kai Yagana nace kiyi haƙuri". sai kuma ta kuma ɗaga murya daga sassautata ɗin da tayi, "to wai da ban haƙura ba kya ga na barki kici gaba da zamar min a gida alhalin kin shigo babu sallama kamar wadda ta shiga gidan kafirai. kiyi adu'a kawai Allah ya yafe miki". ban sake ce mata komai ba na maida murfin idona na rufe, naji da abunda ke damuna ma kaɗai ya isheni balle wannan mitartata me hawa kai. Yagana na fitowa tsakar gida taci karo da awaki akan kwanon abincinta, daga inda take taja tayi turus, tayi salati da sallallami ta riƙe haɓa da cewar,"kai yau naga abunda ya isheni bai ishi ubangijina ba. yanzu dama Mairo abinci kika kawo min shi ne kika barwa awaki anan saboda mugunta, anya kuwa yarinyar nan ba ki gamu da aljanun tunbotsai ba, dan wallah al'amarin naki kuma ya fara bani tsoro...da ma ni tunda kika ce min kin fara gane-gane na fara sarewa da sabbin halayenki da nake gani. to lallai dole na koma wurin Malam Kabiru dan ban yarda ke bace da kanki, Adamu yazo ai ƙoƙarin magance lamarin tunda aka fara da haka wataran za'a iya faɗowa a rufeni da duka a rasa me ƙwatata gida daga ni sai halina...Allah dai ya saka min". ta ƙarasa tana kore awakin daga kan abinci, ta ɗauki kwanon tana sake sabuwar masifa akan yanzu harda nama acikin abincin amma Mairo ta salwantar mata da shi, to kanta ta yiwa ba ita ba, tunda Uwarta ce ta girka abinci kuma taja mata asarar albarkarta. har ta gama gyaran tsakar gidan bata daina mita ba, shaf ta manta ma da batun Mairo a gidan sai da ta koma ɗaki, tana ganinta kuma mita sabuwa ta ɓarke, sababi iri-iri, faɗi take,"ni ai da kika san aiken dole Suwaibar tayi miki da kika zo ƙofar gidan sai ki aiko yaro yay sallama dani na karɓi abuna, amma fisabilillahi sai ki shigo ki zauna min akan sabon botikin da Mujibu ya siyo min, abu ko sati biyu bai yi ba kin fasa min shi, haka kwanaki kika min sanadin robata sabuwa fil". nace,"yanzu Yagana ni ina naga mazaunin da zan fasa wannan botikin me ƙwari, kawai salon kija min faɗa wurin Baba Mujibu". ta nuno min botikin tana faɗin,"yo ina zancen jan faɗa, ki gani da idonki mana ki san ba ƙarya nayi miki ba...ni da za ku gane ma ku bar zuwar min gida gaskiya, yarana ba arziƙi garesu ba su na ƙoƙarinsu wajen ganin sun wadatani da abubuwan buƙataduk dan kar naje yawon aro, amma ku dai Ƴaƴan Adamu sai dai idan baku zo min gida ba...to zan faɗawa uwar kowa kar wacce ta ƙara aiko min ɗanta gwara ake aiko almajiri ina bashi sadaƙa, ko in taka inje da ƙafata, haka ɗazu yarinyar nan Zubaida daga zuwa wanke-wanke omon ɗari da ashirin taga bayanshi a kwanuka uku". ni dai duk abunda take ina jinta ban tankata ba amma har ga Allah ta isheni, a zuciyata ina jin kamar na miƙe na ɗaure mata baki irin yanda Sadiya da Sunusi suka yi mata kwanaki, ta ishesu da masifar sun shigar mata ɗaki babu izini, su ko suka ɗaure mata baki da hannu har sanda Allah ya kawoni na kunceta. "Mairo ki dage kiyi karatun boko don kankin kanki ba kamar yanda wasu suke yi ba dan ace sun yi". maganar ta haska acikin kwanyar kaina, furucin da mutane uku suka yi min shi a ranaku daban daban, Baba yay min, Gwaggona tayi min, haka Ya Kabiru a randa zai tafi furucin da ya fara yi min kenan, kaina a ɗaure yake tun a ranar dalilin kasancewar furucin iri ɗaya da yanda Baba da
🏠