NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 54 of 223

a zuciya, yayinda Kulu ke aikin shafa kaina tana lallashina da bani haƙuri akan nayi masa uzuri nima ina ransa zai kira, ni kam ƙaro ɗan sautin kukana nake ina cewa ko da ya kira nikam ba zanyi magana da shi ba, ba zan ƙara kula shi ba har ya dawo. jiyo motsin shigowa yasa Kulu tai azamar miƙewa ta koma wurin zamanta, ni kuma nasa hannu na goge fuskata gudun kar Gwaggo ta tuhumeni. Gwaggo ta shigo tana cewa dani,"kije Zulai na kiranki, daga nan ki ɗau abincin Yagana ki kai mata, naga yaran nan har yanzu ba wanda ya shigo". na amsa da to na miƙe jiki a mace na fita. a tsakar gida na sami Inna Zulai da Innata su na ta shafta, sai Allah wadaran gwamnati suke akan rashin tsaro na ƙasa, Inna Zulai na bada labarin rashin imani da wasu ƴan garkuwa suka yiwa wata mata, abun ban tausayi idan kana jin irin wannan ma duk sai kaji duniyar ta isheka. "Inna sannu da zuwa". tace da ni,"yauwa Mairo, ya sauƙin idon?". na amsa da,"da sauƙi". "Allah ya sauƙe...kinga dama can inda naje ne naji su na batun maganin ciwon ido na islamic shine na bisu na karɓo a gwada ko za'a dace kamin aje asibitin". ta faɗa tana ɗauko kwalin maganin daga jakarta. ta miƙawa Innata ta amsa tana faɗin,"an gode kuwa. dama yanzu Malam yake cewa gobe za aje asibitin cikin birni ance na can yafi kyau...to amma wannan ɗinma sai a fara gwada shi ɗin kamin goben ai ba'a san ta inda za'a dace ba". "aiko dai an gode wallahi". cewar Gwaggona, ita ma ta karɓi maganin daga hannun Innata tana duba shi. Inna Zulai tace,"haba Suwaiba mene na godiyar...ta fara gwada shi yanzu, yace kwalli ne zata ke yi da garin". nima na amsa da, "to Inna an gode". daga haka ta miƙe ta wuce ɗakinta, ni kuma Gwaggona ta umarceni dana kwashe shanya na kuma wuce na kaiwa Yagana abincinta, na bata haƙuri yaran da za su kawo mata ne basa nan. a ɗaki Innata ta ƙwace maganin da Inna Zulai ta bayar, ashe bani ɗaya ce ke tantama da sauyin halin Inna Zulai ba na lokaci ɗaya, a hankali Innata take cewa da Gwaggona, "haka kawai wa yasan ina taje ta karɓo, yarinya tayi amfani da shi ya ƙara kashe mata ido ayi me ɗungurin gun...dan ni wallahi wannan tuban na Zulai ban yarda da shi ba, ba haka kawai ba dole da wani nufin, masu iya magana suka ce kaji tsoron muguɓ da ya shiryu a lokaci ɗaya". Gwaggona tayi murmushi tace,"to yanzu ya za'ai da shi?". "ajewa za'ai ace mata ana amfani da shi...ai baka saurin yarda da tuban mutumin da ka san can ba ƙaunarka yake ba". ni dai na fita na ɗauka abincin Yagana nayi gidanta, tafiya na ke tsigai tsigai kamar zan faɗi, na shigo lungun gidan naji takun tafiya ta bayana, da ina tafiya a hankali sai na daɗa saurin tafiyata akan wadda nake, duk da cewar ba a hankali nake tafiyar ba dama, amma dai dole na ƙara sauri kasancewar layin shiru ba kowa, tsab sai a yanka mutum ba'a sani ba. ta gefen ido nake bin gefena da kallo da son ganin wake biyoni haka saboda duk a tsorace nake, gani na ke kamar wani ne me shirin cutar dani, dan inda mai tafiyar kansa ne to da yanzu yaci ace ya kai ga inda zai je. ina kawowa ƙofar gidan Yagana sai ganin mutum nayi ya sha gabana. "Mairo dan Allah tsaya ki saurareni". ƙirjina ya buga saboda faruwar baƙon al'amari a gareni. na ɗaga kai na dube shi, Salmanu ne ɗan gidan Malam Liman, ɗan gayu kuma ɗan bokon garin bichi, saurayin da akayi shaidarsa akan kyawun ɗabi'unsa da nagartarsa a duk samarin bichi, saurayin kuma da ƴan matan birni da na ƙauye ke tururuwa akansa. na haɗiye wani yawu a maƙoshina sannan nace da shi,"ina yini". bai amsa ba sai cewa da yay,"ai ni ya kamata na miƙa gaisuwa ba ke ba". nace da shi,"a'a ai ni ce ƙarama dan haka ka amsa kawai". "to shikenan na amsa ina kuma godiya". ya faɗa yana harɗe hannayensa a ƙirji. daga haka ba wanda ya sake cewa komai, shiru ya gimla a tsakaninmu na tsawon ƴan sakanni, sai ni ce na katse shirun da ce mishi,"da wani abu ne?". ya kaɗa kai sannan yace,"a'a ba komai, nima na tsinci ƙafata ne da biyoki a san da idanuwana suka yi tozali da ke, shi ne zuciyata ta umarceni da na zama bafadanki". ban ce komai ba dan ni wannan zancen nasa ban san ina ya dosa ba, saboda haka nasa kai na shige gidan Yagana, ina kuma jinsa yana cewa na gaisheta, ban dai tsaya sauraronsa. ƙafafuna na rawa na ƙarasa cikin gidan har bakina na harɗewa wajen yin sallama. na nemi ƙaramin botikin fenti na ƙarfe na zauna. Yagana na daga can ƙasan rumfar da akayi mata kwanaki ta shan iska, da babban faranti a gabanta tana juye dubulan aciki tana ƴan waƙoƙinta irin na wacca gida yayi mata daɗi babu wani abu da ke damunta. sarai ta san da shigowata amma ta baiwa iska ajiyata, nima kuma na shareta kamar ban lura da ita ba, na nemi botiki na zauna akai, har san da ta kammala abunda take ta taso ta wuce ta gabana tayi ɗakinta, tana shiga kuma na miƙe nabi bayanta, da shigata na malale akan katifarta saboda yanda nake jin jikina kamar ba ruwa saboda rashin ƙwarinsa. can bacci ya fara ɗaukata salatin da Yagana ta zabga ya farkar dani a zabure, tafa
🏠