NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 53 of 223

hannu ya dafi goshina ya kalli idon nawa ya furta,"sannu Mairo". "yauwa Baba". na amsa masa idona na kawo ruwa saboda tausayinsa da naji ya kamani a yanda yake ta magana tattare da damuwa a muryarsa. "yana miki ƙaiƙayi ne?". na kaɗa masa kai,"a'a sai dai zafi da nake ji da yaji-yaji haka". yay ɗan jim kan yace,"bari idan na fita zan taho da zam-zam, Liman yace a karanta fatiha ƙafa bakwai aciki sai kike ɗigawa". Gwaggo ta fito a ɗaki ita ma ta nemi wuri kan tabarmar ta zauna tace da Baba, "naji kana asibitin Makka, yanzu har ma iya yin sammakon zuwa Malam? asibitin da kwana ake can wajen kama layi. ko dai muje na garin nan kawai?". yace da ita,"ai mun yi magana da Salmanu na gidan Malam Liman, yau zai shiga kano kuma acan zai kwana, to na roƙe shi nace dan Allah yayi ƙoƙarin kama mana layi tun da ba shi da nisa da inda yake zaune". Gwaggo ta gyaɗa kai,"ah to da dama ai, hakan kam anyi dabara...mu duka zamu je?". Baba yace,"ai kuna dai jin da yanda aka sami kuɗin kina kiran ku duka, ayi kuɗin mota da ya ya kenan?...ke ki zauna ba sai kinje ba Uwatta ta kaita". ya faɗa yana duban Innata yana ce mata,"ni dai kuyi ƙoƙarin shiryawa da wuri, asibitin nan ance mai kyau ne". Inna ta amsa shi da,"to". ashe Inna bata manta da maganar da zata min ba, Baba na fita ta karkato da hankalinta kan Gwaggo tana cewa,"wai kina lura da yarinyar nan kuwa yanda take ramewa kamar wadda ake zuƙa...jifa yanda jikinta ke neman lalacewa, kalla ƙasusuwa kalla yanda fatarta tayi haske kamar jini zai tsarto". Gwaggo tace,"hmmm ba ta ƙwallafa tafiyar Kabiru da Adawiyya a ranta ba taya kuwa ba zata rame ba...dan shashanci sai kace waɗanda akace sun tafi ba zasu dawo ba". na ɗan turo baki nace, "to Gwaggo shaƙuwa ce fa". na faɗa a raunane. ta taɓe baki tace, "kune ma kashin awaki ƙarshe kenan, to ko su idan suka ji zafin rana rabewa suke". bance komai ba, na yunƙura zan miƙe Inna Amarya ta kuma dakatar dani, ta kafa ta tsare akan saina faɗa mata abunda nasa a raina nake wannan muguwar ramar mara kyan gani, ni kuma nace mata ba komai, da ƙyar dai ta sarara min da tarin tambayoyinta tukunna na miƙe naje ƙarasa shanyata, har dai cewa ko dai aure nake so, to wannan tambayar ce ma sai ta sani kuka saboda naji kunya, kuma a ganina idan har zata min wannan fassarar to kenan tana min kallon ƴar iska ne. har da Ya Amadu ya kira yaji muryata ya tambayeni me nakewa kuka na faɗa masa Inna ke cewa ina son aure, yace Innarsa ko tawa? nace masa tawa, yay dariya yace nayi haƙuri zolayata take. Nayi sallar azahar ina zaune kan darduma na zabga tagumi, ɗakin daga ni sai Kulu a zaune, ta baro inda take zaune ta dawo kusa dani ta kama hannuna. ƙasa da murya tace,"meke damunki?". na dubeta da idanuna da suka soma shanyewa nace,"wai me yasa ba kya son kowa ya san kina magana?". na tambayeta ina lura ƙofar ɗaki saboda shigowar wani. ta lakuce min hanci tana murmushin da yake kauda damuwar raina tace,"sannu sarkin wayo, ai ni na fara tambayarki dan haka ki fara bani amsa menene ke damunki?, yanzu ba ki da aiki sai tagumi da kuka, kuma duk kin rame kina neman lalacewa". ta faɗa da nuna kulawa. ni fa har ga Allah idan tana magana idan ba nutsuwa nayi ba to ba gane me take cewa nake ba, saboda yanayin hausarta bata fita sosai, kamar me gwaranci kamar me yin wani yaren na daban, nai ƙoƙarin maida hawayena nace mata,"Ya Kabiru na ke tunani, ban san a wane hali yake ciki ba yanzu, tun da ya tafi ba muyi waya da shi ba, ba muji ya isa lafiya ba". ta janyoni zuwa jikinta ta kwantar tana shafa kaina cikin tattausar murya tace,"kina kewar Ya Kabiru da yawa?". na ɗaga mata kai alamar ehh. tace dani,"kar ki damu Ya Kabiru yana cikin ƙoshin lafiya insha'Allah, ki hani zuciyarki da munana zato akan tafiyarsa kinji, kiyi yaƙinin yaje lafiya sai ki bi shi da adu'a kuma...sannan kiyi masa uzuri kinga ƙasar can da nan ba ɗaya bane, ana jan kuɗi sosai a kiran waya, shi kuma kin san a irin yanayin da yake ciki na rashi, ki zama me uzuri...amma nasan koma menene yanzu yana can yana fafutukar abunda zai yi ya sami kuɗin da zai kira gida kuma ba dan kowa ba sai dan ke". "to amma me yasa ba zai iya aron wata wayar ba ya neme ni, ai tare da Suhail ya tafi why can't him ya ari wayarsa ya kira da ita...yayi tafiyarsa yana can hankali kwance ni kuma ya barni a damuwa da rashin jin halin da yake ciki". sai kuma na ɗago a ƙirjinta ina goge hawayena nace,"Kulu dama Yaya yana mantawa da Ƙanwarsa?". tayi murmushin da ya bayyanar da haƙoranta tana tayani goge hawaye tace,"ko da Yaya yana mantawa da ƙanwarsa to ina mai tabbatar miki da ke naki Yayan ba zai manta da ke ba...wataran za ki ce na faɗa miki hakan...ki ƙara ba shi lokaci shi ma kina ransa, yau fa gaba ɗaya sati biyu ne ma da tafiyarsa...". nai saurin tarar nunfashinta da faɗin,"ba ki iya lissafi bane, wane yace miki sati biyu?, yau fa kwanansa ashirin da biyar da tafiya, amma ko rana ɗaya bai kira wani yace a duba masa halin da muke ciki ba". maganar nayita ina kuka mai taɓ
🏠