NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 52 of 223

rjinsa na zuba masa idanuwana masu kama da jin bacci, ya ƙara damƙe hannuna yana faɗin,"banda iko, da ace ina da iko Mairo babu abunda zai min ni shamaki da tafiya da ke, to Baba ba zai bari ba...amma ki sani tafiyar nan zan yita ne saboda ke, haka abun da zanje nema acan zan nema ne saboda ke, saboda ke kaɗai Mairo, ke ɗaya tal da kika zama jini da tsokar Kabiru...burina a rayuwa na jiyar da ke daɗin cikinta, na shayar da ke farin ciki na rayuwa, na zama katanga a tsakaninki da baƙin cikin da duk zai kusanto ki...ki cika alƙawarin da kika ɗaukar min kinji ƙanwata". yay furucin ƙarshe yana mai ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali. ayanzu gidanmu da babu Adawiyya babu Ya Kabiru jinsa na ke babu daɗi sam, gidan ya zamar min tamkar kango, Sadiya ba wata hira muke zama muyi da ita ba saboda shegen son girmanta, Basma kuma Yayan Gwaggo da ya zo daga kano ya tafi da ita gidansa, wata ƙila ma ta koma can da zama a yanda naji Gwaggo na faɗa, Zubaida kuwa ba zama take ba saboda makarantar Allo. duk da cewar ina da karaɗi acikin gidanmu to amma yanzu babu jigona, duk sai nayi sanyi, dan tun tafiyar Ya Kabiru kullum ina ƙunshe a ɗaki ina kuka, na ci kukana na ƙoshi ba tare da sanin kowa ba, kukan da gangar jikina kaɗai tasan ma'anarsa, sai zuciya da ke jin zafi da raɗaɗin rashin Ya Kabiru a kusa da ita. ***** kusan sati biyu kenan bani da cikakkiyar lafiya, ko da yaushe da ciwon mara nake yini, ga ciwon ido da ya uzzura min, ga munan mafarkai da nake ta famanyi kuma na kasa faɗawa Gwaggo. ina shanyar kayanmu da na wanke Mu'azzam ya dawo, ya miƙo min waya yace na riƙe Ya Amadu zai kira. na karɓa na soke a zanina ina jiran shigowar kiran nasa. Inna Amarya da ke zaune bisa kujera tana bakacen shinkafa tace dani, "ke wai ni anya yarinyar nan lafiyar ɗaya kuwa?, gaba ɗaya kin sauya, duk kin yi sukuku, aje shanyar nan kizo". na bar shanyar na ƙarasa gareta na zauna kusa da ita, kaina a ƙasa ƙirjina na bugawa, zuciyata na taraddadin Inna Amarya ta gano SIRRIN ƁOYEN da ke shimfiɗe cikin ƙwayar idona. ______________________________________ *ZAN BARSHI A RAINA.* Ba wai dan ba ya sonta ba, a'a sai dan saboda tsananin ƙaunar da yake mata hakan yasa shi sadaukar da soyayyar da yake mata ga wanda zuciyarsa take ganin ba shi ne ya dace da ita ba matuƙar yana raye...duk da irin bala'in son da yake mata amma ita tata zuciyar ta gaza fahimtar hakan daga gare shi duk da tsantsar shak'uwar da ke tsakanin su in baka sani ba ka gansu tare baza ka ta6a d'auka ba masoya bane, a sanda tata zuciyar ke can ta faɗa tarkon son abokinsa amininsa ABBAS wanda ya riga shi furta mata kalmar so. Bai farka daga neman halaka kansa da yake ƙoƙarin yi ba sai da maganar aure ta shiga tsakanin Amininsa da Abar ƙaunarsa, ya danne zuciyarsa ya haneta nuna ƙulafucin da take akan Hanan, yana ji yana gani Amininsa zai Aure muradin ransa. Kuma a kowacce rana, kowanne yini, kowacce daƙiƙa, kowanne fitar nunfashi, a duk bugu na zuciyarsa Sonta ƙara ruruwa yake a gare shi, tausar zuciyarsa yake yana lallashinta sai dai kash duk yanda yaso ya daure ya kasa, ba zai iya ba, rashin kasantuwarsu a inuwa guda zuciyarsa zata illata...shin me zai faru?, zata kasance mallaki ne ga wanda ya sadaukar da ƙodarsa akanta?, ko kuma zata kasance mallaki ga mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa akanta?...AB-NAN ne ko AF-NAN??. Kada ki/ka bari a baku labari ki nemi naki akan farashi me sauki mai arha kwasha-kwasha akan sari naira dari biyu (#200) kacal👌🏻🤸🏻‍♀️ domin Neman karin bayani ki nemi ni akan wannan number +234 704 524 2700 *Comment&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *17)* maganar da Inna zata yi min ta katse a lokacin da Baba ya fito daga ɗakinsa yana min magana. "ke gobe sai ki shirya zaku je asibitin makka a duba miki idon naki, lokacin karatunku nata tafiya ga su Adawiyya har za su shiga cikin wata guda". kaina na ƙasa cikin ladabi da girmamawa nace,"Allah ya kaimu goben Baba". ya amsa da, "Amin". Inna Amarya tace da shi,"kuɗi sun samu kenan?". ta faɗa tana murmushi. ya amsa mata, "ehh to kusan hakan...yanzu Alhaji Nasiru ya kirani za'a kai icen dubu biyar gidansa...kuma jiya Amadu yace ya tura dubu biyar, to kinga idan aka haɗa insha'Allahu za su isa a biya buƙata".  Innata ta gyaɗa kai tace,"to Allah ya daɗa rufa asiri, gwara ai maganin ciwon tun kamin yay tsamari tun da jiya ma fa da daddare ce tayi bata gani gaba ɗaya, yau kuma kaga duk sai naga idon ya ƙanƙance sose gashi harda ɗigon jini". ta ƙarasa faɗa tana ɗagowa da Baba fuskata a san da ya iso wajenmu. Baba yasa
🏠