NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 51 of 223

daga baiwar da Allah ya halicce ki da ita". na rumtse idanu gam ina girgiza kai da cewar ba zan iya ba, ni ban da wata baiwa. "zai sare ni Mairo". sautin Muryar Kulu cikin kuka ya sauka a kunnena, nai hanzarin buɗe ido na dubeta da yanda ta kare jikinta da hannunta tana ƙudundunewa a jikina. ban san lokacin da wani ƙarfi yazo min ba, nasa hannu na kaiwa kansa duka, shi ma sai yay saurin kautar da kansa. mamaki, al'ajabi da kuma tsoro suka kamani a san da nayi jarumtar ƙura masa ido, sai naga nan take ya karayar da kai ƙasa sai kuma jikinsa ya motse, da gudu kuma ya fara jan jiki yay hanyar rariya, kamar ƙiftawar ido sai na neme shi na rasa. daga haka kuma ban ƙara sanin me ya faru ba, sai farkawa nayi na ganni shimfiɗe kan tabarma, Baba a gefen damana yana min tofi, Gwaggo na min firfita, sai sauran ƴan gidan da su ke kewaye da ni. Inna Amarya ta kamani na yunƙura na miƙe zaune ina mai da numfashi. Baba yace da ni, "Sannu". na amsa da,"yauwa Baba". Yagana ta taso daga in da take ta juye rubutu a kofi ta miƙo min tace na shanye, zanyi gardama ta rufeni da faɗa, ba shiri na amsa na kafa baki zan sha amma sai na kasa, Ya Kabiru ya karɓi kofin daga hannuna ya buɗe bakina ya toshe min hanci ya tsiyaya min a haka har na shanye. "Ina ne kuma yake miki ciwo?". Yagana ta tambaya. "ba ko'ina, aini lafiyata ƙalau". na faɗi hakan ne gudun kar na ɗaga hankalinsu, na yi silar rugujewar tafiyar su Adawiyya, amma a zahirin gaskiya idona da nake kallonsu da shi ba sose nake gani ba, ganina ya sauya dishi-dishi nake gani, ga zafi da jijiyar idon nawa ke yi. Inna Zulai tace,"kin tabbatar dai babu abunda ke miki ciwo ko?". nace,"ehh Inna ni lafiyata lau". Yagana tayi ƙaramin tsaki tana cewa,"mun sani dama, in dai kece ai ba kya cuta". sai kuma Gwaggo ta hauni da faɗa akan ai bana adu'a nake shiga banɗaki, nace mata wallahi ina yi yaune kawai na manta ban yi ba kuma shi ma dan na taho a matse ne, Baba yace to karna kuma mantawa, ita adu'a ba'a sakaci da ita. su Adawiyya suka ci gaba da shirin tafiya makaranta, zumuɗi yasa ko abinci ma ta kasa ci, tunda Ya Kabiru ya tafi nemo mota ta kasa zaune ta kasa tsaye dan daɗi, faɗi take yanzu tunda ba tare zamu tafi ba zata wuceni a aji kenan. nace mata ai nima ba jimawa zanyi ba, da zara wannan tsohuwar ta gama rigimar tata shikenan zan taho. jikina duk yayi sanyi lokacin da suka fito za su tafi, na ƙanƙame Adawiyya ina kuka itama tana kuka, ina cewa ba zan iya zaman gidan babu ita ba dan Allah a barta mu tafi tare, itama kukan take tana faɗin ba zata iya zaman makarantar babu ni ba, sai da Baba ya tsawatar mana sannan ta muka saki juna. ba zan iya kallon tafiyarsu ba dan haka na juyo gida na bar su Gwaggo a waje, na shigo ina bin jikin bango, Kulu ta taso tana tambayata menene, na kaɗa mata kai nace,"ba komai". dan ita ma nasan muddin na faɗa mata cewar bana gani sosai to zata iya faɗawa Gwaggo, saboda ita ma na lura ta damu da al'amurana kamar ciki ɗaya muke, har na shige ɗakin Inna Amarya ina jin kallon da take bina da shi, na malale akan gadon ƙarfen Innata ina fuskantar rufin kwano, idona a rufe yake inaji da raɗaɗin ciwon da yake min. nayi shiru kamar mai bacci, amma ba bacci nake ba, na lula ne acan wata duniya ta tunanin wasu murɗaɗɗun al'amura da ke addabar ƙwaƙwalwata tun kwanakin baya, to amma ba su suka fi damuna ba ayanzu. ayau rana ta farko bacin tausayin Kulu da nake ji sai naji ina sonta, na san a haife ta haifeni, dan haka naji ina mata so irin na uwa, ba dan komai sai dan sadaukarwar da tayi akaina yau, banda taimakon Allah da kuma taimakonta da tuni na zama tarihi, dan tabbas macijin nan sai ya sareni...lallai ya kamata na saka mata da wani abun a rayuwarta, take zuciyata ta ƙudurci aniyar nemawa Kulu hakkinta na wofuntar da rayuwarta da iyayenta suka yi...dan haka dole na miƙe tsaye, na ƙara ɗaura ɗamarar yin karatun boko mai zurfi dan ganin na cimma matakin da Gwaggona ke so na kai, bayan Babana da zan taimakawa ita ma Kulu na taimaka mata. tafiyarsu Adawiyya da kwana uku shi ma Ya Kabiru ya tafi, ranar tafiyarsa kuwa na sha kuka kamar raina zai fita, har nafi jin tafiyarsa akan ta Ya Amadu, dan shi da zai tafi da ƙyar aka ɓareni ajikinsa, shi kansa sai Yagana ce ta tuge hannunsa daga rungumeni da yayi, kuma har da ƙwallarsa, hawayen da naji su har ƙasan zuciyata, su ka kuma tugunzuma tunanina a san da ya duƙa ƙasa gabana ya zube gwiwoyinsa yana hawaye yana roƙona akan na kula masa da kaina, kar nayi abun da yake ba dai-dai ba, sai naji duk duniya babu wani abu da yake min daɗi, ji nake tamkar nayi bankwana da farinciki kenan. a sannan nima na tsuguna gabansa na faɗa jikinsa na ƙanƙame shi, kuka nake me tsuma zuciya, ina kwaɓar zuciyata daga wautar da take yi. tun sa'ilin da na mallaki hankalin kaina na sani, bayan so na jini da zuciyata take yiwa Ya Kabiru har da wani ƙazamin so da ba zai zama me amfani a garen ba. "Ya Kabiru dan Allah ka tafi dani". na faɗi hakan a san da na ɗago kaina daga ƙi
🏠