NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 50 of 223

ko jambaki, a'a ke kawai ki fita zaro zaro kamar tsohuwar bazawara in dai za ki je ki biya buƙatr kanki shikenan, kina tafe sangalolo babu rangwaɗa babu ɗan karya ƙugu, alhalin ke jiki ba jiki ba kamar sillan kara, gaba a shafe baya a shafe". na kalleta na harareta nace,"wallahi ƙarya kike kice ta ko'ina a shafe nake, ai ba ki leƙa ƙirjin kin gani ba". ta kawo min duka da karan da ke hannunta, har yanzu kuma bata saki fuska ba. "ni Allah maganar gaskiya nake miki ba wasa ba, bi ki san irin kishin da nake ba idan naga ana zuwa zance wurina ke banda ke, kar ki buɗa zuciyata kiga irin damuwar dake ciki tun ace naga samari na kawo min kayayyaki ke kuwa sai wanda aka sai miki a gida... ko me baƙin jini ai sai haka, ki fita babu me kulaki sannan a gida ma babu me zuwa wurinki, sai kace wadda aka yiwa asiri da mujiya...kina biye maganar Yagana tana hure miki kunne da cewar ke matar manya ce...to matan manya ai sai waɗanda su ka fito daga babban gida, ke kuwa ba ƴar kowa ba...to Allah ki gyara haka, in dai ba so kike mu kuma yin faɗa ba, kina dai jin abunda Baba yace ko ba muyi candy ba mijin aure yazo aurarmu zai yi". na dakatar da zancenta da cewa,"kinga maida wuƙar ki daina ɓacin rai, kishin samari akaina kiyi fatali da shi...dan in faɗa miki maganar gaskiya burin rayuwar Mairo bata gina ta akan samari ko aure nan kusa ba, tun da Mairo ta mallaki hankalin kanta, ta gina burin rayuwarta akan karatu, karatun boko, karatun da zai bata mutunci da martaba a duk inda ta shiga...amma saurayi kam baya gaban Mairo". ta tuntsire da dariyar ƙeta har da sunkuyawa,"sai dai na jiki amma ba in yarda ba, dan wallahi babu macen da zata ce saurayi ba ya gabanta, ko da ike ance abin da baka samu ba haɗa shi da baka so...a ƙaddara ma hakanne, yanzu alal misali Suhail yace yana sonki za ki amince masa ko kuwa shi ma za ki fatali da shi ne?". na waigo na dubeta, "wane kuma Suhail?". nai tambayar bilhaƙƙi ba da rainin wayo ba. tace, "Suhail dai da kika sani ɗan ethopia abokin Ya Kabiru". nayi tsaki, "to ai ba shi ba, ko sarkin ethopia ɗinne da kansa wallahi ba ya gaban Mairo balle wata tsiya Suhail". nayi gaba abuna na barta da maganganunta. a taƙaice dai da gudu na shiga gida saboda cikina da ya murɗa, ina sallama kuwa na faɗa banɗaki, ruwan tsarki ma ce nayi da Zubaida ta biyoni da shi. gama tsarkina kenan na miƙe, kallon gabana da zan yi naga maciji sharfaɗeɗe baƙi wuluk ya ɗaga kai yana ƙoƙarin kawo min sara, a gigice cikin ɗimauta na kurma ihu ina kiran sunan Gwaggo, "na shiga uku Maciji a banɗaki". na sandare saboda hasken idonsa da ya dallare ni da shi, ƙafafuna suka kasa gaba suka kasa baya, na zama kamar wadda aka dasa a wurin, dan ko motsi na kasa, ba wai saboda tsoro ba, sai dan nima ban san dalili ba. ku ka nake ina neman agajin jama'a, ga mazan gidan duka sun fice, Matan babu abun da za su iya yi min, duk sun yi cirko-cirko a bakin ƙofa su na kallona su na ihu da neman taimakon maƙota, kan kace mene wannan gidanmu ya cika, kuma da yake juma'a ce maza duk sun wuce masallaci. idan Gwaggo tai yunƙurin shigowa sai ya maida bakin saran nasa gareta, hakan yasa na haneta shigowa. siffanta munin kamanninsa ya zarce tunani, ganin yana ƙara kusanto ni na rumtsa ido gam so nake naja da baya amma ina abu yaci tura kamar aikin tsafi. hawaye ne ke gangaro min kawai, rayuwa kam tuni na sallama da ita. na riga na gama fidda tsammani da sake yin nunfashi a doron ƙasa, sai ji nayi an riƙo hannuna, na buɗe idanuna da ke a rufe ina kallon Kulu wacca ta yi shahadar shigowa, ita kanta sai ta bani tsoro, dan ko a maza babu me ganin wannan macijin yace zai kawo ɗauki in dai ba wai dama da shirinsa ba, to ko Uwar da ta haifeni ma ta kasa wannan sadaukarwa, amma ita saboda ganganci da rashin hankali tana ganin mutuwa tana tunkararta. na haɗiye wani wahaltaccen yawu a maƙoshina a san da na maida kallona ga Macijin da a yanzu ya maida harinsa kan mu biyun. Kulu ta damƙe hannuna sosai, su Inna kiranta su ke da kwakwazo akan ta fito amma kamar bata jin su. murya tana rawa nace,"ki fita dan Allah kar kema ya cutar da ke". ganin dai ba ta da niyyar fita nai ƙoƙarin hankaɗata gefe amma ko kusa na kasa motsa jijiyar jikina. sai muka tsaya muna kallon kallo da ita, kamin tasa hannu ta juyar da fuskata ga majicin da bana ƙaunar ganinsa saboda girmansa da baƙinsa. "wallahi Kulu idan biki fita ba yau zan tona miki asiri acikin gidan nan". na faɗa ina kuka. tayi ƙasa da murya tace,"alƙawari kika ɗauka, kuma alƙawari kaya ne, wanda kuma duk ya saɓa wutar Allah zata ci shi". ta kasheni da dukkan jijiyoyina, dan tabbas nayi mata alƙawarin ba zan faɗawa kowa tana magana ba har zuwa ranar yankewar numfashina, duk da cewar bata san dama can nasan tana maganar ba. ta ƙara yin ƙasa da murya sosai tace,"ke ɗin ƴar baiwa ce, kina da baiwar da ba kowa Allah ke bawa ba cikin bayinsa, dan haka za ki iya da wannan macijin duk ƙarfin cutarwar kuwa da yake da ita, karki karaya, ki buɗe ido ki razanar da shi
🏠