NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 5 of 223

ani kusa da ita kuma muke gudunta, lalurar nan ba ita ta ɗorawa kanta ba fa". "ai biki fimu sanin hakan ba ko". "to ayi haƙuri". Inna Amarya ta shigo ɗakin tana faɗin,"ni dai na rasa wannan dalili, idan kun san matar nan za kusa jininku suke ƙyamarta me zaisa kuce zaku jawota jikinku dan taimaka mata. To ni dai gaskiya a daina samin Ƴa a gaba da faɗa, tunda ma ba ita ta-ke kai kanta wurinta ba, yauwa! ita da ke zuwa inda ta-ke ita za ku yiwa faɗa...idan ka gama abin da ya kawoka ɗakin sai ka miƙe ka fita, ni ban kiraka dan kasa min ƴa a gaba kana mata faɗa ba, kiranka nayi kaji damuwarta ka lallasheta, ah tau tashi kaje haka Amadu na gode, mu kwan lafiya". "mu kwan lafiya kuma Inna?". Tana warware tabarma tace, "ehh Amadu mu kwan lafiya ni kam". Yana murmushi yace, "yanzu fa garin ya waye Inna, ƙarfe tara ne fa". "ehh na sani ai kaje ni kam dan Allah na gaji da ganinka haka".  Siririyar dariya sauke bisa laɓɓansa ya fita a ɗakin bayan yace da Inna Amarya ya wuce wurin aiki. [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *MissAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *2)* Safiyar yau zaune nake kan kujera ina wanke-wake, yayin da Adawiyya kuma ke shara tsakar gida bayan kammala wankin bayi da tayi, can gefe kuma Inna Zulai ce tana lissafa mafitai da take sayarwa, sai Gwaggona da ke kai da komowa zuwa madafa kasancewar yauma girki a hannunta yake. Inna Amarya kuwa na ɗaki bata fito ba, dan dama ita uwar ɗaka ce da wuya ka ganta a waje, in dai ba wai ranar girkinta ba ko kuma ya kasance duka iyalan gidan ana zaune a tsakar gida. Baba ne ya fito daga ɗakinsa yana gyara zaman hularsa yake cewa da Adawiyya,"kira min Kabiru". Ta ajiye tsinstiyar da ta-ke shara ta fita cikin hanzari domin cika umarnin Baba. Ni kuma na dubi mahaifin nawa da kyau ina yaba kyawunsa da kuma jin ƙaunarsa na ƙara fizgar duk wasu hudoji na jikina, ban ankare ba sai ji nayi hawaye sun cika min ido saboda tausayinsa, na lumshesu zuciyata na daɗa bugawa da sonsa da ƙaunarsa. "Baba Sannu da fitowa". Nace da shi ina miƙewa na ƙarasa inda yake na karɓi buhun hannunsa da zai fita da shi, ba komai bane acikin buhun sai kayan faskaran icce. Babana Adamu Hashimu asalin mutumin garin bichi ne dake cikin jihar kano, kuma sannane ne aciki da wajen ƙauyen bichi saboda sana'arsa ta siyar da itace wadda ya gada a wurin mahaifinsa Malam Hashimu, babu inda zaka shiga ka fita acikin ƙauyen bichi ka tambayi Malam Adamu me faskare ace maka ba'a sansa ba, ko kuma ka tambayi gidansa ba'a kawoka har dakalin gidanmu ba, Haka zalika shi ɗin manomi ne domin kuwa yana da gonaki har guda biyu a fagolo, sai dai a sakamakon ƙwacen gonakin da gwamnati tayi Babana ya rasasu dan ciki har da nasa guda biyun, haka yanaji yana gani babu yanda ya iya dole ya haƙura dasu dan bashi da inda zai kai kukansa a karɓar masa hakkinsa, sai dai ya kai kukansa ga sarki Rabba adalin shugaba, dan yace ba zai yafe musu ba, domin da albarkar wannan gonaki biyunne Baba ke noma abincin da za'aci a gidansa har na tsawon shekara, shinkafa, wanke, gero, masara, dawo, maiwa, waken suya da barkono duka suna daga cikin abinda Baba ke Nomawa. Malam Adamu mutum ne mai mutumci da tsananin kyautatawa, kamilin dattijo mai wadatar zuci, bashi da kwaɗayin abin duniya ko kaɗan, hakan yasa girmansa da ƙimarsa ke ƙara yawaita a wurin jama'ar garin bichi, matan Malam Adamu huɗu, Hajiya Hajara itace matarsa ta farko wadda ya kaita saudiya tun silalla na da daraja, ayanda tarihi ya nuna Hajiya itace jarumar matarsa dan babu ruwanta da duk wata harkar fitintinu na kishiya ko kuma dangin miji, matar rufin asiri domin ko a wancan zamanin da Baba ke da ƙarfinsa Hajiya ta ɗauke masa nauyin karatun yaransu uku, Ƴaƴan wurinta biyu dana abokiyar zamanta ɗaya, wanda kaf cikin yaran gidanmu su kaɗai ne suka sami ilimin zamani na boko har matakin da suke akai yanzu na diploma, ƴaƴanta uku Kabiru, Aminu sai autarsu Safiya wadda a lokacin haihuwarta ne Hajiya ta rasu, itama kuma ranar data cika sati a duniya tabi bayan mahaifiyarta. Inna Zulai ita ce matar Baba ta biyu, kuma ita ce su kai zama tare da Hajiya, fitinanniyar mata ce, dan ko da yaushe tana kan hanyar zuwa wurin bokaye a burinta na a lalata zamantakewar dake tsakanin Baba da Hajiya, sai dai har Hajiya ta rasu burinta bai cika ba Allah bai sa tayi nasara ba, akaf Matan Baba ita ce wadda taci gida domin ta tara Ƴaƴa da yawa, Amadu shi ne Babba, Sunusi, Mu'azzam, Lukman, Sadiya, Adawiyya, Mubarak, Saleh, Jamila da Habiba sai auta Zubaida. Sai Gwaggona Suwaiba da ta zo a mata ta uku, Mace mai sanyin hali dan bata faɗa ko kaɗan, sai dai akwai miskilanci, idan Inna Zulai zata zo tsakiyar kanta sau dubu ta sauke buyaginta Gwaggona ba zata ce mata kanzil ba, kuma mutane su na ta faɗin daga Hajiya sai Gwaggona a matan da Baba yayi sa'ar samu, saboda Gwaggo da Hajiya halinsu kusan ɗaya ne, banbacinsu Gwaggona miskila ce bata kuma ɗaukan rainin dangin m
🏠