NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 49 of 223

e tana jaddadawa Gwaggo a jiƙa min tagarzaje na sha, shi ma ance yana maganin mayu, kamin dai Allah yasa taje ta dawo ɗin. Ya Kabiru na bin ta a baya yace,"ke dai a dawo lapia...zancen tagarzaje kam ba zata sha ba haka kawai ya kuma hargitsa mata ciki...mu magani in dai ba Nafdac bama sha". Ta tsaya sololo tana dubansa tace,"shi kuma Naufdak ɗin mene?". Yace,"ba ki san shi ba". a ƙufule tace,"saboda ban sani ba ɗin ai na tambayeka, Allah sa kuma ba zagina kayi da harshen nasara ba...daɗin Amadu kenan shi magana bata dame shi ba balle har ya faɗa maka ba daɗi". Ya Kabiru ya girgiza kai,"to ni yanzu Yagana me nace acikin maganata mara daɗi". "yo gashi kuwa ina cewa a bawa yarinya maganin da zai taimaketa kana ce min ba za'a bayar ba...to ka tambaya Uwar zoman da ta karɓi haihuwarka ko Uwarka Allah ya jiƙan rai sai da ta sha tagarzaje kamin ta sulluɓoka, ah to kuma bata mutu ba a lokacin sai da ta haifi biyu bayanka". Bai ƙara cewa da ita komai ba ya wuceta zuwa ɗakinsu. Mu na jiyota a zaure ita da Auwalu wanda ya kawo waya Ya Amadu ya kira, ya bata wayar su gaisa tana ce masa a'a ita ba sai sun gaisa ba sauri take akwai in da zata je me muhimmanci, a dai ce tana gaishe shi, kuma dan Allah kar ya manta ya turo mata sallahun manja da ta ba shi. abun takaicin manjan ma kwalba biyu ne, wai ƙawarta ta faɗa mata ɗanta da yake zuwa lagos yace acan akwai ragin ɗari a kowacce kwalba akan yanda ake siyarwa anan, haushi ya cika Lukman yace da ita"idan ba ki cika ɗari biyu kin siya anan ba kya kuma biyan kuɗin manjan gaba ɗaya a kuɗin mota". bata dai ce da shi komai ba tai gaba tana zikiri. sai da kowa ya gama gaisawa da Ya Amadu sannan na karɓa, yay min sannu da jiki sannan yace na kaiwa Gwaggo wayar, tana ɗaki tana aikin mai da kayana ƙasan gado na miƙa mata wayar, kamar ba zata amsa ba sai kuma ta karɓa tana amsa sallamarsa aciki ciki, da tana tsakar gida ne a zaune, amma tun da taji maganar Auwalu yana cewa Amadu ne ya kira ta tashi tayo ɗaki, sai kuma tayi rashin sa'ar gashi na biyota da ita, kuma na saka a handsfree. "to ya wajen na ku?". ta tambaya shi kamar wadda akaiwa dole, ko da yake dolen akai mata. shi ma da ya gane yanayin muryar tata acikin sanyin murya yace "lafiya lau, yauma na fara zuwa aiki, kuma Alhamdulillah wurin yana da kyau...ga ogan ba shi da wata matsala, yanzu haka ma ya bani dubu hamsin yace na siyi kayan abinci da abubuwan da zan buƙata, albashina kuma duk wata za'a ke bani dubu ɗari...insha'Allahu gobe zan buɗe account zan turo dubu ashirin da biyar sai a siyi kayan buƙatar gida". "to Allah ya shi albarka...ya yanayin ibadarka a wurin tun da ance babu musulmai?".  "Gwaggo ai babu wani banbancin addini a wurin, sallolina duk nayi su a office ɗina". "to yayi kyau a dai ƙara kulawa". ya amsa da, "insha'Allahu". sannan ya ɗora da cewa,"cikin kuɗin Gwaggo sai a bawa Mu'azzam dubu biyar ya sai waya a hutar da Auwalu haka...Kabiru ma ashe ya gyaro tasa ban sani ba sai yanzu yake faɗan". "umm ya gyaro jiya, shi ma ai tafiyar tasa ta matso kusa sun ce jibi zai wuce...sun gama yi masa komai na tafiya jiya ma ya amso tikitin jirgin". Ya Amadu yace,"haka yake faɗa min...ai nace da Baba ya daure yaje masarautar da kansa yayi musu godiya". Gwaggo tace,"nima na faɗa masa sai yace ai niyya suka yi ba shi ya roƙa ba, baya son yaje a fara cewa yana zuwa maula...to ɗazu dai Yagana ta masa magana yace zai je bayan tafiyar Yaran nan". shiru kamar babu me kuma cewa komai sai Gwaggo ta numfasa tace da shi,"ni dai dan Allah ka dinƙa kulawa da arna nan Amadu...Allah yi muku abarka sai anjima". bayan duk mun gama shiryawa Inna Zulai ta aikemu gidan ƙawarta da za'ai bikin ƴarta, ta sai mifitai dozin biyar da za'ai rabon kamu. ta gargaɗemu sosai akan karmu zauna Kabiru ya shiga wanka kuma shi shirinsa ba mai wuya bane. mu na kan hanyar dawowa muka ga Malam Liman, har ƙasa muka duƙa muka kwashi gaisuwa da neman tabaraki, "Mairo dai ƙara girma ake gashi nan har kin gama taddo Yayar taki". mu kai murmushi bamu ce komai ba, sai ya ƙara cewa,"Malam Adamu kam ai ya kamata yanzu kuma ya karkata hankalinsa kanku...ku ƙarasa gida Allah yay muku albarka". can mun yi nisa Adawiyya ta kwaɗa uban tsaki tace,"Allah Mairo kina baƙantan rai". ta faɗa cike da zafi. ban dubeta ba naci gaba da jan karana ina tafiya nace da ita,"yi haƙuri to...amma dai ma me nayi miki?". a yanzu dana ɗaga kai na kalleta sai naga ta zabgeni da uwar harara, ta nuna ni sama da ƙasa da hannu kana ta kuma cewa,"dan Allah dube ki...Wai ke sai yaushe za ki sauya ne, duk san da za'a fita ba ruwanki da wani gyara jiki ke kawai ki fita a harbutse, haba dan Allah kinfa girma yanzu, ki fara cin ganiyar ƴan matancinki kuma". taja tsakin takaici, "shi yasa ai har yanzu gaki nan kin gagara yin saurayi, ba me kawo miki sile da sunan kyauta...su ma mazan ƙauyen fa sunfi son mace ƴar gayu, ke ba ki kalla yanda samari suke rawar jiki akan Sadiya da Habiba bane...amma ke kullum jiki ba man arziƙi balle ƴar hoda
🏠