NOVEL SHARES -
..to billahillazi Mairo ki shiga hankalinki, idan kin san wani ba ki sa wani ba, in wani ya barki wani ba zai barki ba...to ni dai na roƙi ki rufa mana asiri haka, kar a kuma irin ta ɗan gidan Ladiyo da kika ƙwalawa dutse da kuna yara tasa aka shanye miki ƙafa". Na tura baki gaba nace,"to ni Yagana yaushe rabona ma da faɗa da wani, ko fita yanzu ba yi nake ba...shi kuma Auwalun munafiki da ya kai miki gulma ai shi ya fara zaginmu yace mana ƴaƴan me faskare". Ta gwame baki tace,"to da ƴaƴan shugaban ƙasa kike so yace muku...ko kuwa ƙarya yayi ku ba ƴaƴan me faskaren bane, ni in da yay magana dani ma ai sai in faɗa masa abunda bai sani ba Kakanku ma me faskare ne, kinga idan ya tashi yace ƴaƴan me faskare jikokin me fakare, zancen banza kawai...ke ba ɗiyar kowa ba sai jin kan tsiya...". Na katseta da cewa,"Yagana babu fa zancen jin kai anan wurin, babu ɗan halak ɗin da za'a zagi ubansa yaja baki yay shiru, balle kuma ni Mairo, wallahi kaf faɗin duniya ma ba acikin garin bichi ba babu shegen da zai aibata sana'ar ubana nayi shiru sai na rama...ke fa da kanki kike ce mana kada ɗan banzan da yay mana mu ka ƙyale dan za'a raina mu, balle shi shegen munafikin na san ba gaskiya ya faɗa miki ba, dan da kema alokacin ko baki tsine masa ba sai kin masa iyaka da gidanki...kinga kuwa irin cin kashin da yay mana daga Adawiyya ta bige wani tsamurmurin yaro ba ta sani ba, Wai shi ɗan birnin da naira ta zaunawa ajiki, shikenan su duka suka hauta da masifa saboda sun ga sauna...ni kuwa na bi su har inda suke nayi musu wankin babban bargo". Gwaggo ta hamɓareni daga kusa da ita ta hauni da faɗa,"dama irin abunda kike shukawa a wajen kenan, faɗan ma ki rasa da wa za kiyi sai da Auwalu yaro me hankali...to daga yau ɗin nan na gargaɗeki, kar na kuma ji tunda ba sa'anki bane shi...kuma ita Adawiyyar da ace ta na kallon gabanta ta ina zata bige wani har a zageta...shashashai biyu kawai, to wallahi ku iya talaucin gidanku, dan duk ranar da ku ka kai wani bango naga kadarar da za'a siyar a ƙwato ku". Gwaggo bata rufa baki ba Baba ma ya ɗora da nasa, su ka hau mu caa ni da Adawiyya faɗa suke mana ta inda suke shiga bata nan suke fita ba, haƙurin ma da mu ke bayarwa basa ji. Baba faɗi yake,"idan kuma kun sauya wasu iyayen ne sai naji, dan ni dai nasan ba tarbiyar gidana bace wannan".
Yagana ta taƙaita faɗan nasu da cewa, "kai Adamu naji kana batun tafiyar makarantar yaran nan anjima...to Magana ta gaskiya banda Mairo za'a tafi, ita a barta sai ta gama warwarewa...". Nayi karaf nace,"warwarewa kuma ta yaushe, ni naji sauƙi". Taja carbi tayi hailala uku sannan tace, "kaga ai irinta, in dai da Mairo a wuri bata barina na magantu, to kace mata tayi shiru da kai na ke maganata". Ta dubi Ya Kabiru tace, "yanzu kai ne zaka shirya ka rakani gidan Malam Kabiru, naje na zayyane masa komai game da ciwonta...ai mata rubutu ya bada turarukan sammu...an fara da irin haka ba zai yiwu ta shiga dokar daji babu tsari ba, dole a miƙe tsaye...tunda iyayen ba masu lura da ƴaƴa bane, kwanaki ita Suwaiban da nayi mata magana ma cewa tayi Allah na tare da su, bayan Allah shi da kansa yace tashi in taimakeka...kuma fa alhalin tana ganin wannan yarinyar halittarta dole a miƙe tsaye akanta saboda baki da kuma ƴan hasidin iza hasadin...Allah ya jiƙan Alhaji da yana raye tun kuna jarirai zaku dinga shan rubutun tsari...dan haka ni dai a matsayina na Rakiya in har na isa ina kuma da iko akan Mairo to babu inda Mairo zata je a yau, a barta sai wani jiƙon".
Baba zai yi magana ta ɗaga masa hannu, dole yayi shiru.
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*16)*
To babu yanda dai Baba ya iya, dan bin umarnin Yagana dole in har ana son kwanciyar hankali, sannan kuma Baba yana neman albarka.
Ta yunƙura ta miƙe Sannan tace da Ya Kabiru,"tashi muje ka rakani kamin lokacin tafiyar ta ku yayi". Yace da ita,"A'a fa Yagana ki kama hanya ki tafiyarki ke ɗaya kawai, ni da zan kai yara makaranta, yaushe muka je muka dawo har na shirya". "to amma dai naga ai da sauran lokaci tafiyar, yanzu ne fa zamu dawo ba zama za muyi ba...ina so ne a haɗa har kai da Amadu na amso muku na farin jinin ƴan mata ko Allah yasa a dace". Ta faɗi hakan tana ƙunshe dariyarta. Nace da ita,"abun ai ba rashin farin jini bane kije ki duba kiga irin tururuwar da ake akan su". Ya Kabiru ya kalleni yace,"barta ni tuni ina da matata a hannu, dan haka ta riƙe taimakonta Amadun ma baya so". Ta doki cinya tayi bakin ƙofa tana faɗin,"kwayi da wata". Ta fice tana cewa su Gwaggo sai ta dawo, su ka rakata da adawo lafiya. Tana nufar zaur