NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 47 of 223

Zulai in da ace matar arziƙi ce ai mai iya yiwa gidan nan kuɗin mota ce duka a tafi asibiti tun da ke da sana'arki me kauri a hannu...ta in da nake godewa Allah kenan da Amadu bai yo mugun halinki ba...yanzu ke da me wayo ce ma ai rawar jiki za ki kama ko dan ki samu fada a wajen mai gida...to matsalar ke ba kya jin faɗa balle shawara, da an soma magana sai kice za ki zumɓurowa mutum baki, shi yasa sam bana son zuwa gidan nan, ga shi dai gidan ɗana ba na ɗan wani ba...to amma gwara aje gidana a sameni yanda zanyi da dalili idan an min abin da bai gamsarni ba...to Allah dai ya kyauta". Magana take tayi ta hana kowa cewa uffan, da ma ita idan ta fara bata gajiya kamar radio, ta nufi zaure tana mitar Gwaggo da nuƙu-nuƙu a wajen shiri, zuwa asibiti ba wajen biki ba ta rasa shirin me ta tsaya yi. "to ni da nace ki ɗauko sutura ba duka kayanki nace ki ɗauko ba fa, ina nufin ki ɗauko abunda za ki sutarta jikinki". Gwaggo tace, "to ai Yagana ke ce tunda kika shigo kin hana kowa magana". Yagana ta saki baki galala tana kallonta,"au so kike kice da asiri na shigo kenan tunda har za ki ce na rufewa kowa baki...to ni wallah ko da ƙawayena da suke bin bokaye ni dai Allah bai taɓa nufata da zuwa ba har na gama tashen ƴan matancina.....". Gwaggo tayi saurin katseta da cewa, "yi haƙuri Yagana ba haka nake nufi ba, ina nufin kina ta faɗa ne...". Ai Gwaggo bata ida zancenta ba Yagana ta tari numfashinta, "ai da ike ga jarababba ta afko muku gida...to ni kinga ma nayi tafiyata kisha zamanki, ko da kika ga na damu da naje banda Mairo ce babu abunda zaisa na ɗaga hankalina haka, dan da ace su Sadiya ne sai dai na bisu da aiken gaisuwar jinya, wanda yake maka ai shi kake damuwa da shi, Mairo kuwa ai ba daga nan ba". Har ta isa zaure kuma sai ta dawo tana cewa,"ni kuwa ina mara lafiyar gidan nan har yanzu dai bakin bai buɗe ba ko?, wannan Mata tana ganin jarabawar rayuwa, Shekara da shekaru cuta babu sauƙi, Allah dai ya kawo sauƙi, ko da ike ma wa ya san me kika aikata aka garƙame bakin...Saleh ungo ka bata wannan alawar nima Mujibu ne ya bani ita jiya da daddare, to ban samu shanta ba ma har yanzu da ike inata fama da ciwon haƙori kuma babu na arziƙin da ya iya zuwa ya dubani, iyalin Adamu dai sai Allah ya min magani kawai...ungo don Allah ɗayar na sha in haƙorin ya warke, haka kawai Allah ya haɗa jinina da ita mugun tausai take bani wallahi, ace mutum ba um um, wannan baki ai sai ya gume da uban wari". Saleh ya karɓi alawar ya miƙawa Kulu, Adawiyya kuma tace da ita, "to Hajiya Yagana idan kin gama faɗan naki an hutar da ke zuwa asibitin, ki dawo ga Mairon a gida sun dawo tun ɗazu, masifarki ta rufe miki ido kika kasa ganinta". Sadiya tace,"ai da kin barta taje ƙafarta ta gaya mata". Yagana da ta kai zaure ta dawo tana zabga salati,"ke Adawiyya amma ku dai halinku sai ku, yanzu tun ɗazu kun san da hakan baku faɗa min ba ku ka barni ina ta zuba magana ni ma da bana iya shiru da bakina". Na tafi na rungumeta ita ma ta rungumeni, sai ta shiga matsar ƙwalla tana ƙara faɗin ciwona ya ɗaga mata hankali ainun, dan Allah na dinga kiyayewa da shegen kwaɗayina na ciye-ciye, ba komai ake kaiwa ciki ba dan wani abun guba ne. Mu ka koma ɗakin Gwaggo muka zauna aka ci gaba da hira, Ya Kabiru na bada labarin yanda aka karɓemu a asibitin da yanda suka sare da siyan magani, sai da wasu Arna da su ke bada tallafi suka zo kana aka sami magunguna. Yagana tace,"to Allah yasa su na da rabon musulunci". Gwaggo tace mata, "jiya ma ai da za'a tafi babu kuɗin mota Zulai ce ta ɗauko ƴan canjinta ta bayar, da su aka samu na siyan ruwan da aka ƙara mata". Ta ajiye kofin kunu da ta kai bakinta, "to Allah shi albarka yasa kuma dan Allah akayi". Babu dai wanda yace mata ƙala, sai ni da muke hirarmu, tana cewa na shanye kunun tas ko na samu naji ƙwarin jikina. Baba ya dawo ya miƙo min leda, na karɓa nayi masa godiya da adu'a, nama ne balangu aciki, Yagana ta warce ledar tana cewa ba zanci ba, jiya ma aishi naci yasa ni leƙawa lahira amma saboda ban san ciwon kaina ba zan kuma ci, Yaya Kabiru yace mata ai na jiya tsire ne, tace ita dai koma mene ba zanci ba, to ita inta kafe kan magana babu mai iya ja, haka ina ji ina gani dole na maida yawun bakina, ta bawa Saleh tace ya kaiwa tumakinta su ci, ta kuma gargaɗe shi akan shi ma kar yaci. Su na magana da Baba akan zancen asibiti yana faɗa mata aiko binciken da likitoci su kai sun ce ba daga abunda taci bane, amma shi yana tunanin ba zai wuce shawara ba. Yagana ta kifa kai da hannu tana jero salati,"oh ni Rakiya, idan ance ba daga abunda taci bane to kar dai ace mayu ne suke ƙoƙarin kamata". Baba yace,"ah haba Yagana ciwo ne dai kawai". "hmm Adamu ka bari kawai, amma ni dai zanyi iya dafa qur'ani mayu ne su ke son kamata ko kuma baki, kasan kambun baka ma mugun abu ne". Ta dube ni tace,"ina dai ce har yanzu halinki dana sani ya nan na rashin barin ko ta kwana? Dan ko shekaranjiya yaron nan Auwalu ya labarta min irin ɗibar albarkar da kika yi masa kwanakin baya.
🏠