ɗumbin tausayina, har tsawon wani lokaci da magani ya tsarga min cikina bai bar yi min ciwo ba, ciwon da nake jin inama zare raina akai na huta, tun ina kuka sautinsa na fita har na koma sai hawaye da ke sauka ta gefen idona, Baba kansa ya sare da lamarin nawa ya barwa Allah yayi ikonsa akai...cikin hukuncin ubangiji kuma wajen ƙarfe uku na dare sai ciwo ya tafi, na neme shi na rasa, kafin asuba nayi garau dan bacci harda munshari, kuma na tashi ras da ni, ƙarfe takwas aka bamu sallama muka koma gida.
Inna Zulai na shara muka shiga gida, ganina yasa ta tsaya kallona da maɗaukakin mamaki, kamin ta wurgar da tsintsiyar ta rungumeni jikinta, sannu da barka take ta jera min ba adadi, lamarin nata har ya bani mamaki, ta sakeni ta kama hannuna mu kai ɗakin Gwaggo, ƙwalawa Gwaggona kira take tana ta fito taga ikon Allah. Gwaggona da ta fito ta ganni tsaye da ƙafafuna kamar ba wadda aka fidda ranta daren jiya ba, tsananin farin ciki yasa duk ta ruɗe ta kiɗime, ta jefar da kwallar da ke hannunta ta rungumeni, godiya take ga Allah tana kuma yi min sannu, ta sakeni ta ɗago tana dubana, tana ƙoƙarin maida ƙwallar idonta ta ce, "Mairo kinga yanda kika rame...babu dai inda ke miki ciwo yanzu ko?". Ta ƙarashe muryarta da damuwa. Nayi murmushi nace, ,"Gwaggona ki kwantar da hankalinki ni kam na warke, babu inda ke min ciwo yanzu haka". Ita da Inna Zulai suka haɗa baki wurin faɗin, "Allah ya ƙara lafiya". Dai-dai lokacin kuma da su Baba suka shigo, Inna Zulai ta wuce tana musu sannu da zuwa tare da amsar kayan hannunsu, ni kuwa binsu na ke da ido da al'ajabin sauyin da aka samu a tsakaninsu.
a ɗakin Gwaggo dai da aka yada zango babu hirar da ake sai ta ciwona da ya kiɗima kowa, duk faɗi suke ba su taɓa zaton zanyi rai ba, Sadiya ta kawo min duka tana cewa inda na san ba mutuwa zanyi ba ai sai na faɗa mata tayi bacci harda munshari, ina dariya nace,"yanzu dai ban ce kinyi ƙarya ba amma kina so kice min baki bacci ba jiya?". "hmm ba za ki fahimci halin da aka shiga ba ne". Shi ne abunda ta iya cewa kawai, Inna Zulai ma tace,"to ai ko ni nan wallahi baccina sama-sama nayi shi...ga Kabiru ne kaɗai me waya a gidan balle mu kira muji halin da ake ciki, to tare ku ka tafi da shi, da asubar fari kuwa da naji su Salisu sun buɗe ƙofe gida ba kiji gabana yanda ya faɗi ba". Na ƙyalƙyale da dariya har ina kifawa jikin Gwaggona nace, "wooo ni Mairon Baba ashe dai a gidan nan ana so na har haka". Inna Zulai ta ƙwalo min mafici tana miƙewa ta fita dan kawo min Kunu.
Shigowar Kakarmu Yagana sai gida ya ɓarke da sabon bidiri, ita bata san an sallamomu ba, ashe tun a daren jiya da akace mata an kwantar dani a asibiti sai ta ɓarke da gudawa jin ance an tafi da ni a sume, ta zauna kan dakalin ƙofar ɗakin Baba tana kuka har da su zuƙar majina, Kuka wiwi kamar wadda aka aikawa saƙon mutuwa, faɗi take, "yanzu ko a wanne hali yarinyar nan take ciki oho, ya Allah ka bata lafiya...shi kuma Adamu da rashin azanci ai sai ya dawo ya sanar damu halin da ake ciki ko kuma ya turo shi Kabirun, amma duk sai su zauna acan su yi shiru abin su, ko da ike zani ce ta tadda muje, danma dai Allah yasa ba Amadu bane, in wannan yaronne sai ta mutu ma a binneta bamu sani ba...to yanzun ma wa ya sani ko ta mutu ni Rakiya...yarinya me hankali da tunani kaf jikokina albarka...Allah na tuba kar nayi saɓo ita cutar ga yara nan rututu a gidan amma ta rasa wa zata ɗauka sai abokiyar hira ta". Yagana ta miƙe tana gyara zaman gyalenta da yaƙi zama tana cewa, "ke Suwaiba ɗauko sutararki mubi sahunsu ni ba zan iya wannan zaman jiran tsammanin ba, in jini kawai acan hankalina zaifi kwanciya...ke ma dai banda soluwar Uwa ce ace an kwantar da ƴarki a asibiti amma kina zaune anan hankali kwance wai kin barwa kishiya riƙonta, to idan da mugun nufi aranta fa tayi mata wani abu ta ƙarasata fa...ko da yake ba Zulai bace balle nace, amma ita ma Aishan ba na shaideta ba tun da shi mutum ba sanin abin da ke cikin zuciyarsa kayi ba...yanzu mutane sun zama Allah a fili fir'auna a zuci, kiga su na ta haba-haba da kai su na nuna maka duk duniya ko uwar da ta santoloka duniya albarka, nan kuwa duk buge ne a zuciya ji suke kamar su kasheka...to matsalar idan kasha tabara kasha yasin kuma ka ɗora da tofin Allah ya tsine shikenan ka gama da su, takaicin duniya ya kamasu, su rasa kataɓus". Ta yi shiru tana gyara ɗaurin zani kan taci gaba da cewa, "ki zo muje ƙawata Harira ta kawo min ajiyar kuɗi sai na ara mu yi kuɗin mota da su, na san har da rashin kuɗin motar ma ya hanaki wanke ƙafa kibi sahunsu tun duku-dukun asubahi...ni gaba ɗaya wannan zama naku na rasa irinsa wallahi, ban taɓa ganin kishiyoyi marasa hankali da tunani irinku ba, ace wai idan ɗayanku na cikin mawuyacin hali ba za'a sami mai taimaka masa ba...to s'a kowacce ta kama nata ta ɗaure a gindi, wannan dai ba hali na gari bane sam ku sauya tun kamin ƙasa ta cika muku baki". Ta ɗago tana duban Inna Zulai wadda tayi kicin-kicin da fuska tun a ɗazu, tace da ita, "yanzu ke