NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 45 of 223

duk iya binciken da suka yi basu gano wani ciwo a cikin nata ba ko kuma wani abu da ya kawo sanadin hakan, sai dai sunyi ƙoƙarinsu wajen ganin sun bata taimakon da zai tsaida aman da shi ciwon da take ji idan ta farka. An rubuta allurai da magunguna masu tsadar gaske wanda akai umarni da a gaggauta wajen siyo su, Baba yay shiru domin ba shi da ta cewa, dama tun farko abunda ya ke ji kenan, idan sun gudarwa asibitin kuɗi, nan ma fa ba komai ne zasu yi musu a kyauta ba. Yana tsaye ya zubawa Mairo ido, wadda fuskarta tayi muguwar rama kamar wacce ta shekara guda a kwance cikin ciwo. Tsausayin kansa dana iyalinsa ya daɗa kama shi, ya maida dubansa ga Kabiru wanda yasa kai zai fita cikin mutuwar jiki, ya dakatar da shi daga tafiyar da cewa, "Ban amince maka da rancen kuɗin kowa ba Kabiru, idan kuwa kai hakan to bada yawuna ba wallahi, kuma fushina zai tabbata akanka". Kabiru ba shi da tacewa saboda haka dole ya dawo ciki ya zauna, Inna Amarya tasa hannu ta goge hawayen da ya sakko mata, "To Malam ko can gida zaka kira a ɗebi samiruna akaiwa Matar liman ta siya". Malam ya girgiza kai yace, "babu abunda za'a siyar, mu jira ruwan da aka saka mata ya ƙare, insha'Allahu lafiya ƙalau zata farka". Har ruwan da aka sakawa Mairo ya ƙare bata farka ba, ma'aikaciyar jinyar tazo ta ƙare jarabarta ta tafi babu wanda ya tankata, dan tun a ɗazu take zuwa tana tambayarsu alluran da akace a siyo su na cewa tukunna dai kamin ruwan ya ƙare, ga shi har ruwan ya ƙare shiru. Wata mata da ke kusa da gadonsu itama tana jinyar yaronta ta taso tazo kusa da Inna Amarya tayi musu ya mai jiki, Amarya ta amsa da Alhamdulillahi. Sannan matar ta dubi Malam tace da shi,"ku ƙara haƙuri nan da ƙarfe tara da rabi akwai wanda yake taimakawa marasa lafiya a wajen sayan magani da abubuwan dai da asibiti suka buƙata...su na yin abin nasu cikin tsari ne zasu bi gado gado har sai an biyawa kowa buƙatarsa". Kabiru ya duba agogo yaga lokacin har tara da rabi saura minti goma, saboda haka suka fasa tafiyar da Malam yace ayi suka ƙara jira. Tara da Rabi dai-dai kuwa sai ga wasu maza sun shigo su biyar jikinsu da rigunan aikin asibiti, sai mata biyu dake biye da su, ɗaya dattijuwa ɗaya tsohuwa. Madam Merry da Madam Gloria kenan, daga kan gadon su Mairo aka fara amsar katin, Madam Merry ta karɓi katin daga hannun Kabiru ta saka hannu sannan tace ya wuce can wajen karɓo magani ya amso, a haka suka dinga zagaye gado zuwa gado har sai da ta tabbatar ta saka hannu akan katin kowa sannan suka bar ɗakin, masu zaman jinya suka rakata da godiya da kum adu'a. *1:00pm.* Agogo ya buga ɗaya na dare, A hankali na shiga buɗe idanuna waɗanda naji sun matuƙar yi min nauyi saboda kukan dana sha, ko'ina na jikina ciwo yake saboda tsananin galabaitar da nayi, bin ko'ina nake da kallo da son tantance a inda nake dan ban fidda tsammanin na mutu ba. Ina kallon gefen haguna Adawiyya ce ta kwantar da kanta kusa dani, hannunta cikin nawa ta riƙe gam, sai Inna Amarya da ke shimfiɗe a ƙasa da gani bata ji daɗin kwanciyar ba. Na maido idona ga hannun damana inda Ya Kabiru ke tsaye a kaina ya jingina da bango, da alama tsumayin farkawata yake dan ina ɗaga kai muka haɗa ido da shi, ya kuwa sauke wata wawiyar ajiyar zuciya tare da lumshe ido sannan ya buɗe. "Sannu". Ya faɗa a san da yake taimaka min wajen tashi zaune. "ina ne yake miki ciwo yanzu?". Ya tambayeni yana duban yanda nake aikin cije fuska. Nayi masa nuni da cikina, "Ya cikina ne wani abu ke yawo yana karta min farcensa". Yay gajeran murmushi tare da cewar, "yunwa ce". Na girgiza masa kai cikin ƙarfin hali nace, "Ya wallahi ba yunwa bace, yawo yake yi ta ko'ina fa...zafi sosai". Yay ɗan jim yana dubana da nazari kana yace, "ko lokacin al'adarki ne yayi?". Na kuma girgiza masa kai, "a'a Ya ai a farkon wata nake yi". "to ƙila an sami sauyin yanayi ne, sannu bari kici abinci sai kisha magani za ki ji sauƙi kinji Mairon Yayanta". Na buɗa idona da ya cika da ruwan hawaye saboda irin azabar da nake ji na kalle shi, ina fashewa da kuka nace, "Ya ciwo sosai, zafi yake min, ina jin kamar ana tsatstsagani da reza ne". Ya matso kusa ya kwantar da kaina saman ƙirjinsa yace, "yi haƙuri zai daina kinji". *Comment&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *Anyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *15)* A wannan daren haka Ya Kabiru ya fita ya nemo min abincin da zanci, tuwan dawa ne da miyar kuɓewa busassa, Inna Amarya ta bani abincin da kanta wanda na samu naci shi da ƙyar shi ma kuma kaɗan, bayan na gama ci Baba ya ɓallo magunguna na sha da ruwan tofin adu'ar da yayi, Adawiyya na gefe tana ta aikin jera min sannu cike da
🏠