NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 44 of 223

kansa na fita na bawa almajirai, dan har ga Allah ni bana jin daɗin cin abincin ba tare da ita ba. A ɗaki na sami Gwaggo zaune tana sauraran radio, na tambayeta "Gwaggo ina ajiyata?". Tace, "na bawa Innarki". Na wuce ɗakin Inna tana lazimi ta min nuni da inda ta ajiye naje na ɗauka, Basma tazo ta ƙaraci nacin zamanta na hanata ko ɗanɗane nace wallah bata ci. Sai dai tun a yankan farko dana saka a bakina cikina ya ƙulle, ina gama ci kuma sai amai kamar zan amayar da kayan cikina, numfashina ya fara neman sarƙewa, tari yaci ƙarfina babu ƙaƙƙautawa cikin ƙanƙanen lokaci na fita hayyacina. Inna Amarya ta sallame daga lazimin tayo kaina cikin salati da kiɗima, ta shiga ƙwalawa Gwaggo kira itama tazo, ganin abun dai ba me ƙarewa bane Ya Kabiru ya bawa lukman yace yaje chemist ya karɓo maganin amai, babu jimawa sai gashi ya dawo, ba zan iya haɗiya ba saboda halin ha'ula'in da nake ciki, sai Inna Amarya ce ta jiƙa da ruwa kaɗan Gwaggo ta buɗe bakina aka tsiyaye min ya wuce da ƙyar, duk da jiƙe-jiƙen magungunan da Gwaggo keyi tana bani ina sha, da tarkacen magungunan asibiti da Ya Mu'azzamu ya ɗebo, amma abu babu sauƙi sai a wurin Allah dan abu sai gaba yake daɗa yi. Baba duk ya rikice ya rasa abun yi, sai can da ya saita hankalinsa ne yay tunanin yi min tofi, haka Baba ya dinga tofin adu'a ana bani ina kwankwaɗewa. Ya Kabiru na sassarfa ya fita ya kira Ado me chemist anan kusa damu, yana zuwa ya duba ni yaga mawuyacin halin da nake ciki, nan ya shawarci Baba akan a tafi asibiti kawai, Baba ya amsa masa da "to" ya kuma yi masa godiya dan yayi min allurar tsaida amai yace a bar kuɗin. Kowa yay jigum ana jiran ganin ikon Allah akan allurar da aka min, amma ina amai yace bai san wannan ba, ciwon ciki ma haka, kuka nake kawai ina kiran mutuwa zanyi, ina kiran a yafe min, furucina yasa jikin kowa yay sanyi, tashin hankali ya ƙara bayyana a fuskonin kowa. Gwaggo kuwa kuka kawai ta ke tana riƙe dani ajikinta, ni dai na tabbata a yanzu babu abin da ya rage acikina illa kayan ciki, amma abinci da ruwa kam babu su, dan a yanzu haka idan nayi kakarin aman sai dai na tofar da jini, hankalin kowa ya daɗa tashi, ƴan'uwana duk kuka suke su na ta jera min sannu. Ya Kabiru yace da Baba, "Baba mu wuce asibitin tun da kaga babu sauƙi". Baba wanda damuwa ta bayyana ɓaro-ɓaro a fuskarsa, yay shiru bai ce komai ba, Inna Zulai da ke shafa min ruwa ajiki saboda zafin zazzaɓi ta ɗago ta dube shi tace, "Malam kayi shiru, halin da ta-ke ciki fa yafi kamata da asibitin". Baba kamar zaiyi kuka yace,"ku kun san halin da ake ciki, asibiti wajen kashe kuɗi ne masu yawa, a yanzu kuwa idan muje wa zai bamu?, aina zamu samo?, ni da ban ajiye ba ban bawa wani ajiya ba, yanzu haka babu ko kuɗin mota ajikina...dan haka mu zubawa sarautar Allah ido insha'Allahu sauƙi zai sauka gareta". Sunusi yace da Baba, "to ai Baba ba asibitin kuɗi za'aje ba, na gwamnati zamu". Baba yay murmushi mai ciwo sannan yace, "Sunusu ina nusar da ku ne ku gane ko munga likita kyauta akwai kuɗin magani, ko shi ma maganin kyauta zasu bamu?". Shiru ya ratsa biyo bayan tambayar Baba, can Ya Kabiru ya laluba aljihunsa yace, "Baba muje ga ɗari biyar ajikina zata ishemu zuwa asibiti, magani kuma ko ba'a siya duka ba sai a nemi mai muhimmanci ciki a siya". Baba yana dubansa yace, "kana dana siyan magani kenan?". "Allah zai kawo Baba". Gwaggo na gefe tana goge hawaye tace da shi,"Kabiru jeka da sauri samo mota, kaga numfashinta neman ɗaukewa yake gaba ɗaya". Ya fita jiki na sassarfa jikinsa gaba ɗaya ya wanke da zufa, yana fitowa ƙofar ɗaki kuma yay karo da Kulu a tsaye tana kuka. Ya tsaya yana dubanta da kuɗin da ke hannunta, kuɗaɗen da bana ƙasar nan bane, yaja numfashi ya sauke, kamar zai ce da ita wani abun sai kuma ya wuce kawai, ta bi bayansa da ido a san da hawaye ke daɗa sauka saman fuskarta, sannan ta koma ɗaki taci gaba da ruzgar kukanta tare da nemawa Mairo sauƙi a wurin mahallicinta. Babu jimawa Kabiru ya dawo da mai adaidaita, yana shigowa ya kinkimi Mairo wadda ta jima da sumewa, an watsa ruwa an watsa amma babu alamar zata farfaɗo. saboda a sami sauƙin kuɗin mota Malam yace Inna Amarya da Adawiyya ne kawai zasu je asibitin, Gwaggo dai taso da ita aka tafi, sai dai babu yanda zatayi dole tayi alkunya, kuma bata da haufi akan kulawar da Inna Amarya zata bawa Mairo kamar yanda zata bata. Inna Zulai ta tattaro wasu ƴan canjikanta na saida mafici ta bawa Malam tace a haɗa da su, Malam ya karɓa ya baiwa Kabiru yace ya haɗa dana wurinsa. Da zuwansu cikin ikon Allah suka sami ganin likita har aka basu gado, ɓangaren Gwaggo hankalinta yay ƙololuwar tashi da jin zancen, tace zata nemi kuɗi ta taho a yanzu Baba yace a'a ta zauna ai jikin da sauƙi tun da harta farfaɗo daga suman an kuma yi mata allurai bacci ya ɗauketa. A ɓangaren Malam kuwa faɗa ya sha shi a wajen likitoci, na ɓata lokacin da akai wajen kawota, har suke ce masa da sun ƙara wasu lokuta sai dai su kawo gawarta, sun kuma shaida masa a
🏠