NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 43 of 223

". Bata bani amsa ba sai Habiba ce tace,"ina ga fa fitila ce ta suɓuce daga hannunta ta fashe, ƙila kuma da kaya kusa da wurin ta kama bata sani ba". "Allah ya kiyaye gaba". Na faɗa ina riƙe yatsan Adawiyya da ta ƙone ina mata tofi, ta rungumeni tare da fashewa da kuka tana bani haƙuri, haƙurin da ban san na menene ba har sai da ta ce min ledar kayan da Bella ta bani ce ta ƙone. Har raina naji babu daɗi sai dai to ya zanyi tsautsayi ne, saboda haka ma ban tsaya jin ba'asin Kyautar mene aciki ba sai dai da Gwaggo ta dawo na faɗa mata, tace to ai babu komai ba rabo bane ita kuma Bella an gode mata. Hankalin kowa a gidanmu bai gama kwanciya ba sai da Auwalu yazo yace sunyi waya da Ya Amadu yace sun sauka lafiya, idan ya sauka a masaukinsa zai kira, Nan Baba yayma Auwalu godiya da ƙoƙarinsa. Bayan anyi sallar magriba Ya Kabiru yace nazo na raka shi unguwa, Inna Amarya tana tayi masa tsiyar wai ko taɗi zan rakashi, shi dai murmushi kawai yay bai ce komai ba, ya kama hannuna muka fita, wani shagon kayan kwalliya muka je ya siya min ɗan kunne da turare, akan hanyarmu ta dawo sai dana sa ya siya min tsire tukunna muka ɗauki hanyar gida. "idan kin aje kayan kizo". Yace dani san da muka shigo zaure. Ina shiga na bawa Gwaggo kayan nace ta ajiye min kuma kar aci min tsire, tace na dawo na ɗauki kayana ita bata amsar kayan kashedi, ina ƴar dariya na wuce ina cewa,"ni dai na bada kuma na faɗa kar aci min tsire". na fita fuskana ɗauke da dariya sosai saboda mitar da naji Gwaggona nayi wai tasan saboda Basma nake kora wannan kashedin. Da sallamata na shiga ɗakinsu Ya Kabiru, yana zaune kan yaloluwar katifarsa da littafi a hannunsa, haka yake shi sam baya gajiya da duba takarda. Na ƙarasa kusa da shi na zauna na sarƙafe hannayenmu sannan na ɗora kaina bisa kafaɗarsa. "Yaya wai baka gajiya da duba takarda ne?". Ya rufe littafin yana ce min,"lokaci ne Mairo kema soon za ki zama irina tun da ba kya wasa da karatu". Ya faɗi hakan yana shafa kumatuna. "Yaya ɗazu Suhail yazo baka nan". "ehh munyi waya da shi yake faɗa min". "yana da kirki sosai...yauwa ka kalla ma Bella ta bada kyauta a kawo min". Ya muskuta yana gyara zama yace, "ahh ke dai akwaiki da farin jini, Allah ya haɗa jininku da Bella, to shi ne kuma ba za'a nuna min kyautar ba". "ta ƙone". Ya kalleni ta gefen ido sannan yace,"kaman ya ta ƙone?". "Tsautsayi, Adawiyya ta ɗauko fitila ta suɓuce ta faɗi kuma a kusa da ledar, kamin ta ɗebo ruwa ledar ta kama gaba ɗaya". Shirun da yay yasa na ɗago na dube shi, kamin nayi magana ya tari numfashina da cewar, "wannan ai shashancin banza ne". Ganin zaiyi faɗa na hau ba shi haƙuri. Ya sarƙafe yatsun hannunmu wuri guda yana ce min,"Mairo nah". "na'am Ya Kabiru nah". "do you know what i want from you?". Tuni na ɗauke tambayar da yayi min cikin harshen turanci, kasancewar tun da akace zamu tafi makaranta yana zaunar damu ya koya mana kalmomin turanci, kuma ina ganewa sosai dan a makarantarmu ba wani turanci ake mana ba malamai sunfi yin hausa wai saboda makarantar gwamnati ce. Na gyaɗa masa kai, "No Yaya sai ka faɗa". Ya gyara zamansa in da ya fuskantoni, yasa hannu ya ɗago haɓata, ya umarce ni akan in sanya ƙwayar idona cikin nasa. murmushin fuskana yaƙi ɗaukewa a sa'ilin da ƙwayar idona ta sarƙafe cikin tasa, kallona yake babu ko ƙiftawa ya ce,"ki kula min da kanki a makaranta dan Allah, banda shirmen banza da ƙawaye, Karatu ya kai ki dan haka shi kawai za ki yi, ki dage ki zama mai ƙoƙari abar kwatance a wurin Malamai...sannan ban lamunce miki ba dai-dai da ranar ɗaya Suhail yaje makarantar ya buƙaci ganinki kije, bar ganin su ne silarku a makarantar, wallahi naji labari sai ranki ya ɓaci fiye da tsammaninki, karki ga bana ƙasar kiyi tunanin ba zan sani ba...zuciyata zata ke sanar min halin da kike ciki da dukkan abunda kike aikatawa...kuma ki tabbata in har kika wuce ta ɗaya a aji to la shakka zamu yi hannun riga da ke". Na gyaɗa masa kai nace,"insha'Allahu Ya Kabiru zan zama mai kiyaye dukkan umarninka". Na faɗa ina ƙoƙarin maida ƙwallar da ta taru a idona. Ya ɗauko wani zobe a aljihunsa fari mai kyau ya saka min, sannan yace na tashi naje na kwanta da wuri kar azo tafiya gobe bacci bai isheni ba. Ina shiga na tarar kowa na zaune yana cin abinci, yau an makara acin abincin dare kasancewar Inna Amarya ke da girki kuma yau sunje unguwa basu dawo ba sai gabanin magariba. Na wuce na zauna kusa da Adawiyya ina cewa,"lallai ma ke ɗinnan, to kinci rabonki". Fuskar nan tata a haɗe ta galla min harara ta ɗauke kwanon abincin ta juya min baya, idan nayi amfani da hankalina har yanzu dai bata bar fushi dani ba, saboda haka na miƙe naje nace da Inna Amarya ina nawa abincin, tace na tambayi Adawiyya ai haɗe mana tayi, kamar ba zan tambayeta ba kuma sai nace da Basma ta tambayo min ita aina ta aje min nawa. "ta duba ɗakin girki yana murfin tukunya". Abin da tace da Basma kenan a ƙufule. Na shiga na ɗauko, abincin ma naji duk ya fita akaina dan haka na tashi daga
🏠