NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 42 of 223

tuntuni ina son ganin Suhail saboda na bashi agogonsa daya bani ajiya na manta shima kuma ya manta. Adawiyya da ke kallona ta kyaɓe baki bayan taja tsaki tace,"uwar azarɓaɓi da kika tashi haka jiki na tsuma idan kinje me zaki masa ƴar neman suna". Dama ni shashasha kamar yanda Inna Amarya ta faɗa tunda idan an gwaɓa min magana ba ganewa nake ba, Dan haka ina wucewa ɗaki nake ce mata,"ba na faɗa miki ina son ganinsa ba zan bashi ajiyarsa". Basma ce ta ɗauko min kwallar daga saman sif, saboda tsayina ba zai kai ba kuma kujerarmu ta ɓalle, na ɗauko agogon zan fita nayi karo da Kulu da ke shigowa, ta ɗaga min kai alamar tambaya ina zani. "wurin Abokin Ya Kabiru". Na faɗa ina goge ƙurar dake jikin agogon wanda keta sheƙi, ta ƙara kaɗa min kai alamar me zanyi a wajen nasa. "agogonsa zan kai masa". Na faɗa ina ƙoƙarin raɓawa ta kusa da ita na wuce, saita riƙoni tare da karɓar agogon, ta ɗau tsawon daƙiƙa tana kallon agogon sannan ta ɗago ta dubeni, magana take so tayi amma kuma ta kasa, nayi guntun murmushi ƙasan raina nace, _"haba kulu aini yanzu bana cikin waɗanda kike rainawa hankali da rashin maganarki, dan haka idan za ki magantu ki magantu kawai"._ Na bita da ido ina kallon yanda take daɗa jujjuya agogon a hannunta kamar me neman wani abun ajikinsa, nasa hannu na ɗago da fuskarta ina ɗaga mata gira nace, "magana kike so kiyi ba. To yau kawai ki gwada sa'arki mana ko ikon Allah zai kasance akan maganar taki". Na ƙara ɗaga mata gira dan bata ƙarfin gwiwa. "aina shi me agogon yake?". Ta jefo min tambayar, maimakon na bata amsa sai nayi ɗan tsalle da murna. "kinga ikon Allah ko, dama nace miki ki gwada sa'arki...shikenan yau Kulu ta fara magana". Ta riƙo hannuna daga fitar da nake ƙoƙarin yi tace dani,"ki riƙe masa kayansa da kyau wannan ba zallar ƙarfe bane, Zinare ne, dukiya ce ba ƙarama ba. Da kin ba shi ki dawo". Nayi shiru ina nazarin maganarta kafin na kaɗa mata kai na fita. A ƙofar gida na tadda Suhail shi da Adawiyya suna hira, mamakin da nayi da Adawiyya ta nuna kamar bama faɗa da ita, wannan cin maganin da ɗauke kan babu shi, sai jawoni kusa da ita da tayi, ta amsa agogon da ke hannuna tana cewa da Suhail, "kaima Yaya Suhail ina kai ina bawa mashiriranciya ajiya, ai ba'a bawa Mairo ajiya dan idan bata yar ba to zata mantar da mai shi ne ƙarshe kuma ya salwanta". Na murguɗa mata baki nace, "to ai ni da ke sammakal...kuma Suhail idan baka yarda ba ka tambayi Ya Kabiru tsakanina da ita wa yafi wani mantuwa". Ya dubeni yana murmushi yace,"to aiga amsar anan tunda gashi na baki ajiya kin manta da ita tsawon watanni sai yau". "to ai ba mantawa nake ba sha'afa nake...kayi haƙuri". "tom na haƙura kar ayi kuka". Ya faɗa da zolayata sannan ya kuma cewa, "Bella tace na gaida balarabiyar gidansu Kabiru me kama da jininta...kuma tana zuba idon ranar da zata kuma kai mata ziyara". Mu biyun muka kalle shi a lokaci ɗaya sannan a tare muka ce da shi, "wace balariyar gidanmu?". Ya soshi gefen girarsa kana yace,"tace min dai Mairo". Na sunkwi da kai ina murmushi cike da jin daɗi, maganarsa ta katse tunanin da nake na ɗago ina duban ledar da ya miƙo min, nasa hannu na amsa ina cewa yayi ma Bella godiya. Sannan shi kuma yay mana sallama ya shiga mota ya tafi bayan yace mu sanar da Ya Kabiru yazo bai same shi ba. Muna shiga cikin gida Adawiyya ta fizge ledar hannuna tana faɗin,"dilla buɗe mana muga mene aciki". Nace,"sarkin kwaɗayi kawai". Ta kama hannuna muka shiga ɗakin su Mu'azzam. *Comment&Share.* *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *MissAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *14)* Muna buɗa ledar wani daddaɗan ƙamshi ya bugi hancinmu, na fito da kwalin da ke ciki wanda aka nannaɗe shi da abun ado, Adawiyya ta karɓa daga hannuna ta shiga kiciniyar buɗe shi amma saboda irin naɗin da aka masa ta gagara kuncewa. "kinga ki bari Ya Kabiru ya dawo ya buɗe mana". Bata saurareni ba taci gaba da ƙoƙarin yanke abun da reza, na tashi na fita daga ɗakin ina ce mata, "ni dai idan kin buɗe kin gama gani kya kawo min ɗaki". Gaba ɗaya ma na manta da babin wata Kulu, sai da na shigo ɗakin naga ta tsareni da ido. Na turo baki na wuce na zauna ina cewa,"ai kin fara magana dan haka idan ba za ki min magana da baki ba to ki bar kafeni da wannan manyan idanun na ki masu firgitarwa". Naci gaba da abin da nake yi, ihun Adawiyya da ya karaɗe gidan shi yasa ni tashi na fita da gudu, cirko-cirko na samesu bakin ƙofar ɗakinsu Mu'azzamu sai Inna Zulai da ke cikin ɗakin tana watsa ruwa a wutar da ta kama a ɗakin, na zaro ido waje wanda tashin hankali ya cika cikinsu na dubi Adawiyya da ke aikin yarfe hannu nace da ita, "garin ya haka?
🏠