NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 40 of 223

ani kuma zata zo masa da muni kuma dole ya karɓa in har ya yarda yayi imanin da Mahallicinsa, Allah ya kan jarabci bawansa ne domin gwada ƙarfin imaninsa ya gani shin zai iya cinye jarabawar, idan har kuma yayi riƙo da wannan ƙaddarar to zaki kalla ko akan wanne Al'amari ne ƙarshensa yazo masa ta yanda bai yi tsammani ba. Saboda haka ki sani Allah da kansa yana faɗa a Alqur'ani cewa "Ahsiban-nasu an yutraku an ya quluu amanna wahum la yuftanun". Mutane su na tsammanin zamu bar su barkatai alhalin sun ce haƙiƙa mu munyi imani?. To kinga kenan tabbas mumini ake jarrabawa, wannan kuma jarrabawar taki ce, ki roƙi ubangiji ya baki ikon cinyeta ba wai ki zama ko da yaushe cikin kuka ba, wannan kukan babu abunda zai yi miki. Suwaiba ta faɗa miki abunda kike tunanin faruwarsa anan gaba muddin tana raye ba zata bari hakan ta faru ba, nima kuma nayi miki wannan alƙawarin, matuƙar ina raye babu mai sanin wannan sirrin naki, na ɗauke ki ne tamkar ƴar cikina...Suwaiba kuma ta ɗaukeki ne matsayin ƴar'uwar da kuka fito ciki guda, Ko wani ya nemi ya tozartaki wallahi sai inda ƙarfin Suwaiba ya ƙare, ba zata bari ba ko da ace hakan zai zama silar rayuwarta ne". Wucewar sakanni kamin na jiyo muryar Kulu na cewa, "Malam gani nake kaman ƙaddarar zata iya juyawa, ina tunawa da maganar Kakata da take cewa Barewa bata gudu ɗanta yayi rarrafe...haka kuma mahaifina ya taɓa ce mana abunda iyaye suka aikata a ƙuruciyarsu to shi ƴaƴansu suke aikatawa idan sun taso...Malam kayi haƙuri, waɗannan kalamai biyun da nake tunawa su ne suke sakani zubar hawaye su kuma ɗaga hankalina sannan zuciyata ta ƙara yin rauni, ayanzu haka ina mai dana sanin sunan dana raɗa mata, ina gudun karta tashi akan turbar me wannan sunan, Dama ace sunana na raɗa mata da ba zan kasance a fargabar rayuwarta ba a duk inda zata tsinci kanta kuwa, sai dai kuma idan itama ta gamu da irin tawa ƙaddarar". Kukan da ya ci ƙarfinta yasa ta yin shiru, kamin taci gaba da cewa, "wallahi ina jin tamkar na kashe kawunanmu ko dan saboda na huta da ɗanɗanar wannan baƙin cikin rayuwar da nake yi, itama kuma ta huta da fuskantar baƙin ciki anan gaba". Kuka yaci ƙarfinta sosai tana kuma cewa, "gwara ita na kanji tana bina da kyakykyawar adu'a wani lokacin, amma ɗan'uwanta fa?, Allah ɗaya yasan acikin rayuwar da ya ke ciki yanzu, Allah kuma kaɗai yasan irin kalaman da yake jifana da su a kowacce rana ta rayuwarsa, hakkinsa kaɗai ba zai barni samun natsuwa da kwanciyar hankali ba, ita kanta ina shakkar ta san sirrin komai anan gaba domin zuciyarta irinta Kakarta ce, ba zatayi min da sauƙi ba muddin tasan Sirrin Ɓoye...Malam na roƙeka kai da Yaya ku taimaka min da maganin da zamu sha mu mutu, wallahi ba kaina nake tausayi ba, rayuwarta na ke tausayawa...ku bar batun zan koma wajen iyayena domin kuwa zuwa yanzu sun manta da rayuwata...amma ga wannan takardar tana ɗauke da adireshin gidanmu, Bayan raina na aminta akan kuje, idan kunje kun sami mahaifina a raye kuce ina neman gafararsu, ku sanar musu ni da Hussaina mun bar duniyar, amma Hassan yana raye, ina roƙon alfarmar su neme shi su mallaka masa abunda na mallaka gudun kar ya tagayyara a rayuwarsa, idan kuma ya buƙaci mahaifinsa su bashi hoton da yake cikin wannan saƙon yaje yayi yaƙin nemansa"... Shirunta yayi dai-dai da sandarewar ƙafafuna, shin ta wacce fuska zan fassara Al'amarin Kulu ne wanda yake da matuƙar ɗaure kai?, menene ya faru acikin rayuwarta, jiyo takun motsin fitowa nai saurin barin wajen na koma ɗaki, kuma har ɓarawon bacci ya ɗaukeni Kulu bata dawo ɗakin ba, sai a washe gari dana farka sakamakon hasken rana da ya dallare min idanu wanda ya shigo ta ƙofar taga, nayi zumbur na miƙe na sauka daga gado tunawa da nayi da banyi sallah ba. *Comment&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *MissAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maki hajarki cikin farashi mai rahusa, ke dai tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *13)* "Amadu ya kira yace yanzu haka jirginsu zai tashi, kowa ya sasu a adu'a Allah ya sauke su lafiya". Sallamewata kenan daga sallah naji Baba na wannan maganar. Nasa hannu na goge guntuwar ƙwallar da ta sakko min, dan banji daɗin tafiyar Ya Amadu ba alhalin banyi sallama da shi ba, ajikina sai nake jin kamar yayi tafiyar da ba zan ƙara ganinsa ba ne. Na miƙe daga bisa sallayar da nake na fita tsakar gida, na ɗauka tsintsiya na hau aikina kasancewar yau nike da shara, Adawiyya na wanke-wanke inata tsokanarta amma ci kanki wannan bata ce dani ba, kamar bata san ina yi ba. Har ga Allah na manta da mun samu saɓani da ita, sai a yanzu da nayi mata magana naga ta ɗago ido ta ɓalla min harara, jikina sai ya ƙara yin sanyi, nai sauri-saurin kammala shara sannan naje n
🏠