sa kar nayo halin Gwaggona na rashin kyautawa, gwamma nayi halin Malam shi ne yasan mutum da darajarsa, aiko ile sai ga Malam ya fito daga ɗaki yanama Gwaggo faɗa akan ta daina yi ma ta irin haka.
Na ƙara miƙewa zaune ina ƙara roƙon mahaukaciyar nan akan ta tashi ta fita gudun jaza min faɗan Gwaggo, sabon takaicinma ban san sunanta ba, tunda na taso ban taɓa jin an kira sunanta ba sai dai KE kawai, taƙi motsayawa sai kafeni da ido da tayi, irin kallon da naji yana neman tsinkar da jijiyar jikina, na rufe ido na kauda kai sannan na juyo a fusace na doka mata tsawa nace ta tashi ta fice, ai ban gama rufe bakina ba saiga Gwaggo ta shigo ɗakin, ranta a matuƙar ɓace sai huci take.
Kallo ɗaya tayi min ta ɗauke kai sannan ta maida dubanta ga mahaukaciyar tana yi mata nuni da bakin ƙofa wanda ta ɗage labule, karo na farko da naji Gwaggo ta ambaci sunanta, acikin yanayi na tafarfasar zuciya, "Kulu tashi ki fice, ki fice tun kamin raina ya ɓaci". Cikin sanyin jiki kulu ta miƙe jikinta na rawa, tana zuwa dab da inda Gwaggo ta ke sai ta ɗan dakata da tafiya. " ba zaki fita ba saina saka an ɗakko min ƙatti a waje sun fita da ke". Gwaggo ta kuma kai yatsanta dai-dai idon Kulu tamkar zata tsone shi, "ba tun yau ba nake faɗa miki babu ruwanki da ƴata, ki fita a sabgarta, ke nake taimakawa dan haka ba sai kince zaki sakamin ba ta hanyar shiga rayuwar ƴata. Yau ta kasance rana ta ƙarshe da zan kuma ganinki kusa da Mairo, wallahi duk ranar da kusancin inuwarku ma ban gamsu da shi ba, la shakka sai kin bar gidan nan...fice".
Gwaggo ta ƙarashe maganar a hasale, Kulu kanta a ƙasa ta fice a bar tausayi, jikina yayi matuƙar sanyi da abinda Gwaggo tayi mata, na kuma ji haushin Gwaggona ya kamani, sam bai kamata tayiwa mara lafiya haka ba a matsayinta na musulma, balle ma ita da ta ke ƙaunar naka.
Ficewarta faɗan kuma sai ya dawo kaina, "ke kuma ai kinji me na faɗa mata, idanma ita bata fahimta ba ai ke kin fahimta, ki saɓa daga yanda nace".
"Allah ya baki haƙuri Gwaggo, insha'Allahu ba zaki sake ganina da ita ba".
Bata tankani ba tasa kai ta fice, nayi zaman daɓaro anan wurin, kamar na saka kuka haka nake ji, sai dai ni ɗin ina da taurin zuciya, ba abu kaɗan ke sakani kuka ba, hasali ma abu ɗaya nasan yana sani zubar hawaye, taɓa mahaifina.
Ban san lokacin da Ya Amadu ya shigo ba, sai ganinsa nayi a tsakiyar kaina, da alamu ma ya shura tsawon wasu mintuna tsaye a wurin, ban farga da hakan ba sai dana ji Inna Amarya na cewa, "ga Kununta nan, kasata ta sha, ni dai ban san me akayi mata ba".
Shiru yayi baice komai ba, sai bayan fitar Inna Amarya ne ya rage tsawonsa ya tsuguna gabana, muryarsa acan ƙasan maƙoshi yace,"kuka kika yi?". Na ɗago da dara-daran idanuwana na zubesu cikin nasa, domin ya samu amsar da yake buƙata. "to me ya kawo ɓacin ran?". Naja hanci sannan nace masa, "Bala Mai Shago yana bin Baba bashin kuɗi naira dubu huɗu da ɗari uku, kuma yace yana buƙatar abinsa da akai masa nan bada jimawa ba".
"Bashi?". Ya tambayeni da tantamar abinda na faɗa. "ehh ka tambayi Ya Kabiru ai agabansa ne ma ya faɗa, Kuma sai daya faɗa da ƙarfi duk jama'ar gari suka ji".
Numfashi naji ya sauke kafin ya saka hannu a aljihu ya zaro ƴan ɗari biyar biyar guda goma, ya miƙo min yace na kaiwa Bala ɗin nace masa an gode. Nayi saurin yunƙurawa zan miƙe ya maidani na koma na zauna. "ki fara cin abinci". "Yaya ba zan iyaci ba, idan na kai masa tukunna zanfi samun natsuwar ci". Ya kaɗa min kai kawai, har naje na kaiwa Bala kuɗinsa na dawo Ya Amadu na inda na barsa a zaune, sai dai da alama yayi zurfi cikin duniyar tunani, na zauna kusa da shi na jawo kwanon kunu na buɗe awara dake cikin marar tuwo, na ɗau awarar zan kai bakina sai ganin Ya Amadu nai ya miƙo min wata, kallo ɗaya kawai na masa sannan na buɗe baki ya saka min kafin nan ya kuma ɗauko kwanon kunun ya kafa min a baki na kurɓa, guda uku kawai naci naji na ƙoshi saboda kasa sakewa da nayi da shi, da ace Ya Kabiru ne dama ko baice zai bani da kansa ba zance ni shi zai bani, amma shi Ya Amadu yau ɗaya sai nake jin nauyin hakan, na karayar da kai ina cewa Yaya na ƙoshi, sai ya zare min wannan manyan idanuwan nasa masu shegen firgitarwa, hakan yasa ba shiri naci gaba da karɓa inaci sai dana cinye tass.
"me kika yiwa Gwaggo?". Ya jefo tambayar fuska babu walwala, shi dama fuskarsa kullum haka ta-ke.
"shigowa tayi ta ganmu tare da Kulu, amma wallahi Ya Amadu bayan haka ban mata komai ba".
"daga yau nima idan na ƙara ganinki kusa da Kulu saina yankaki har lahira, i mean it Mairo ba zan ƙyaleki ba, tunda ke ba kya gudun ɓacin ran mahaifiyarmu".
"insha'Allahu zan kiyaye, amma fa ni ai bani ke zuwa inda ta-ke ba, ita ta-ke zuwa wurina".
"su sauran yaran gidan baki kalla idan taje wurinsu guduwa suke su barta ba, ko ke ɗaya ce da ba kya jin magana ba za ki abin da akace miki ba".
Na girgiza masa kai, "A'a Yaya, kawai tana bani tausayi ne, sai naga bai dace dan tana cikin wannan halin ba da ta-ke tsananin buƙatar w