NOVEL SHARES -
daban ni da ita ba, ko da an zuba mana idan ɗaya baya nan to sai ɗaya ya jira ɗaya, dalilin da yasa ma Baba wani lokacin ka kiramu da tagwaye. Na kuma kamo hannunta nace, "Adawiyya wani abun nayi miki?". Sai ta fizge taja tsaki tana daɗa rufe kanta da zane, na miƙe na fita jiki a saɓule, Inna Zulai ma da nake mata sai da safe ci kanki bata ce min ba.
Shigata ɗakin Inna tace, "kije Gwaggonki na kiranki, idan kin dawo karki manta ki rufe mana ƙofa bacci zai iya ɗaukeni kamin ki dawo". Na amsa da to sannan na nufa ɗakin Gwaggona, ina shiga na tarar da ita ta gama wanke allo, na zauna gefanta kamar mara lafiya, zuciyata cike fal da tunanin laifin da nayiwa Adawiyya wanda ban san shi ba. Bayan Gwaggo ta gama bawa Basma rubutu sannan nima ta miƙo min sai aikin kauda fuskarta take daga gareni, na miƙa hannu na amsa nayi bismillah sannan na kafa baki na sha kaɗan, ina ajiyewa ta jefeni da wawan kallo, "ɗauki ki ƙarasa shanye shi". Ba shiri na ɗauka na rumtse ido kace maɗaci aka bani, ina kuma shanyewa kawai sai na fashe da kuka ina kifa kai da gwiwa. "me aka yi miki kuma?, idan har akan rubutun nanne to kuwa tabbas yau zan fara sa miki waya ajiki". Nai saurin girgiza mata kai ina cewa,"a'a Gwaggo ba rubutu bane, Adawiyya ce take jin haushina ko magana bata son yi min". Gwaggo taja guntun tsaki ta miƙe tana nufar gadon ta da cewa, "a halinki na rashin kyautawa kika yi mata wani abun". Nace,"Allah Gwaggo ni ba abunda nayi mata". Ta ɗan murmusa sannan tace, "to ni yanzu me kike so nayi miki, faɗanku ne dai wanda ya shiga tsakani kunya kuke ba shi...kuma wata ƙila saboda faɗan da Malam yaywa Uwarta ne take tayata kishi". "a'a Gwaggo tunfa dawowarmu a ɗazu ne". Bayan ta kwanta tace, "to kin gani kuwa dole kin mata wani abun, ai shariya ba halinta bane, ke kuma halinki sai ke...ki kwana anan ba sai kin koma ɗakin Innarki ba". Na miƙe kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki na hau kan gadon, sai da na maƙalƙale Gwaggona sannan na samu bacci ya ɗaukeni sakamakon faɗuwar gaba da naji ya tsananta garen.
Can cikin dare na farka dan gabatar da sallar dare wadda a yanzu ta zame min jiki, idan ban riga Gwaggona tashi ba to ita zata rigani, dama ita kusan kullum cikin raya dare take, na murza idona dan wartsakar da baccin da ke cikinsa sannan na zuro ƙafata na ɗan ƙaro hasken fitila. A tunanina Gwaggona ce ke sallah sai da na ƙaro hasken fitila na ganta kwance tana bacci. Na ƙaro hasken fitilar sosai sannan na kai dubana ga Kulu wadda ta ɗaga hannaye sama tana roƙon ubangijinta, na zuba mata ido sosai kamin nayi la'akari da kukan da takeyi, kana iya jiyo kalamanta da take cikin yarenta, da sautin muryar kuka da ke neman cin ƙarfinta, tun muryar nata na fita a hankali har ta bayyana sose inda nake jiyo maganganun nata raɗau ba tare da sanin me take cewa ba tunda bada yaren da nake ji bane, hawaye gaba ɗaya ya wanke mata fuska, Fatarta ta koma ja. A hankali kuma sautin kukanta da na muryarta ya ragu, ta kifa fuska a tafukan hannunta tana mai ci gaba da kuka a hankali. Tsananin tausayinta ya kamani, nasa hannu na goge hawayen da nima suka sauko min, Lallai a duniya babu marasa tausayi irin iyayen Kulu, babu abunda zuciyata ta ƙissima min akan wannan kukan nata face rashin iyayenta, waɗanda suka manta da ita da rayuwarta tun tsawon shekarun da naji Ya Amadu ya labarta min.
Na sauka daga saman gadon cike da tausayi da jin ƙanta na isa gabanta, nasa hannu na ɗago da fuskarta, na sanya ƙwayar idona cikin nata wanda haskensa ya cika min idanu, lokaci ɗaya ruwan hawayen da ya kuma saukowa daga idonta nima ya sauka a nawa, nasa hannu na goge mata, ban ankara ba naji ta rungumoni jikinta ta matseni tsam a ƙirjinta har ina iya jiyo bugun zuciyarta.
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*MissAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maki hajarki cikin farashi mai rahusa, ke dai tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*12)*
Mun ɗauki tsawon lokaci rungume da junanmu, tun shashsheƙar kukan Kulu na fita har ta daina, ni kuma a nutsuwar dana samu daga wannan jikin nata ne bacci ya soma ɗaukana, sai can kamar kuma tsikarin allura naji ta tureni daga jikinta har ƙeyata ta bugi da bango, ta kauda fuska gefe saboda kar ta haɗa ido dani, lallai acikin ɗabi'un Gwaggona dana Kulu akaina zan iya cewa babu banbanci, dan ko a ɓangaren Gwaggona sau tari ta kan kauda kai daga gareni musamman lokacin da ta san ina buƙatar kulawarta tamkar ba ita ta tsuguna ta haifeni ba, ni kuma hakan na damuna, yana min ciwo, yana kuma sani zubar hawaye, domin banda shaƙuwa irin ta uwa da ƴa da har Gwaggona zata iya jin sirrina, ko kuma na faɗa mata matsalata, Duk sanda na kaiwa Inna Amarya wannan kukan nawa sai tace nayi haƙuri k