NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 37 of 223

sai dai idan bai shigo gidan nan ba Allah saina rotsa wayar tasa dan na tsane shi". Ban ida rufe baki ba Inna ta gwaɓe min laɓɓana, zafi yasa ni sosa wajen ina yarfe hannu. Gwaggona wadda ke zaune daga can ƙofar ɗakinta tace da Ya Amadu, "ni dai na faɗa maka, idan kaje ka ƙara riƙe addininka karka yi wasa da shi tunda kaga dai kai ɗaya ne musulmi acikinsu karsu dulmiyar da kai, kuma kayi taka tsan-tsan dasu domin basu da amana macuta ne, ni wallahi da ace na isa da kai Amadu wannan tafiyar ba zaka yi ta ba, hanyar arziƙi ai da yawa take, baka san ta inda Allah zai kuma ɓullo maka da wata ba...shawarata ka kula da mutuncin kanka". Ya Amadu ya dubeta yana amsawa da, "insha'Allahu Gwaggo zan yi kamar yanda kika ce". Inna Zulai tace,"tafiya ce dai tunda ni dana haife shi na amince to sai yayi ta, babu batun wani da kin isa, ko kin isa ɗin idan nace a'a wannan isar taki bata isa ba...saboda haka ni dai ki rabar min da ɗa da wannan maganganun naki na jafa'i da kike jifansa da su, Ba komai ne ke damunki ba sai baƙinciki da arziƙin da ya same shi saboda ke Allah bai ba ki ɗa namijin da zai hidimta miki ba". Cikin ɗaga murya Baba ya dakatar da maganarta, "Ke Zulai bana son shirmen banza, wannan wanne irin magana ce, Ke ko kunya ma ba kya ji a gaban ƴaƴanki kike wannan sokiburutsun, to ki rufe min baki tun kamin na saɓa miki, shashancin banza kawai". To haka dai Baba yay ta bawa Ya Amadu shawarwari da kuma nasihohi akan zaman da zaiyi idan yaje can, ya jima yana jaddada masa akan yayi ruƙo da gaskiya akan aikinsa, domin ita kaɗai ce zata ba shi nasara a aikinsa ta kuma ɗaukaka shi harta ba shi kariya, shi kuma yana amsawa da insha'Allahu, muma ƙannensa duk muka bishi da adu'a, ni dai harda guntun hawayena alokacin da Ya Amadu ya miƙe zai wuce ɗakinsu, yake cewa mu yafe shi kuma muyi masa adu'a dan ba lallai mu gana ba gobe tunda daga masallaci zai wuce, sai naji kamar yana mana sallamar ban kwana ne ba zamu ƙara ganawa da shi ba. Sai ƙarfe kusan goma sannan kowa ya wuce ɗaki dan kwanciya, har na kwanta naji shiru shiru Adawiyya bata shigo ba, na sauko daga kan gado zan fita, Inna da ke sauya kaya tace ina zani, nace mata,"naga Adawiyya bata shigo bane". tace min, "ki ƙyaleta kawai ba lallai uwarta yau ta barta kwana nan ba". Nace,"a'a bari dai naje na gani, dan naji tace min kanta na ciwo ɗazu". Da sallama na ɗaga labulen ɗakinsu, Inna Zulai na zaune tana jina amma bata amsa min ba, na shiga daga ciki ina cewa, "Inna ina Adawiyya?". Ta ɗago ta kalleni da masifarta tace,"uwar me za ki yi mata da wannan daren, yarinya sai shegen kinibibi irin na uwarta". Lallai ayau na tabbatar da cewar wani na cin darajar wani, banda haka tun a furucinta kan Gwaggona a ɗazu naso na yaɓa mata magana ba ruwana da girmanta, to sai taci darajar mahaifina da kuma ɗanta da ya maida uwata tamkar ita tayi naƙudarsa. "Inna naji tace ne kanta nna ciwo shi ne nazo dubata". Cikin ɗaga murya ta kuma cewa dani, "to da kika zo nan lafiyar za ki bata ne uwar iyayi, to lafiyarta ƙalau kwana ne dai na haramta mata shi a ɗakinku, tun itama baku asirce min ita ba kamar Amadu, saboda haka zo ki fice min a ɗaki kamin ranki ya ɓaci, idan ma barbaɗe aka turoki yi aniyarku ta biku". Ni dai ganin haukarta na daɗa yin yawa na bar gabanta na wuce wajen shimfiɗarsu Sadiya, tabbas akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanina da Adawiyya, duk da cewar sun rufe kawunansu da zanen rufa hakan baisa na kasa ganeta ba, na yaye zanen daga saman kanta, haka kawai na saki murmushi saboda kallon fuskarta da nayi, nasa hannu na taɓa goshinta naji sanyi ƙalau, sai naji daɗi a raina kenan ta rabu da ciwon kan. A hankali na shiga tashinta ina kiran sunanta, sai da aka daɗe sannan ta amsa min, na kamo tafin hannunta nasa a nawa na riƙe, na kai bakina saitin kunnenta nace,"tashi mu tafi ɗakinmu". Daga irin yanda take motsa idonta nasan cewar ba bacci take ba tana jina. Nasa hannu ina girgizata da salon wasa, cikin hargowa tace dani,"dilla Malama ni ki ƙyaleni". Sai na ɗanyi dariya na daɗa girgizata ina cewa, "to ki tashi mu tafi saina ƙyaleki, ai kan naki ya daina ciwo, kin san dai ba zan iya bacci ba kya kusa dani ba". Taja tsaki ta juya kwanciyarta tana cewa, "Ni dama ba wani ciwon kai da nake...kuma idan ba ki kwana tare dani ba ki mutu, kinga ma wallahi idan ba ki rabu dani ba zan tashi na shaƙeki har sai kin bar numfashi, ko lallai ne saina kwana a ɗakin uwar kareren naki". Sosai naji ba daɗin kalamanta, na saki baki ina duban gefen fuskarta da mamaki, ban san me nayi mata ba yau, dan tun bayan dawowarmu daga masarautar bichi ta sauya min, ko magana nayi mata bata amsa min sai dai tayi ta jan tsaki, dana lura da wannan ne ma na tambayeta menene tace min kanta ke ciwo, ashe ba hakan bane, to ko dai nayi mata wani laifin ban sani ba?, tun tasowarmu wani abu bai taɓa shiga tsakaninmu ba akan rigima, dan faɗanmu ma na wasa ne, ko abinci ɗazu ma da aka zuba mana raba mana tayi kowa yaci nasa, bayan bamu taɓa cin abinci
🏠