dda ke tsaye daga bakin ƙofa tana kallon Joseph tace, "tashi anan wurin". Ya taso ya tsaya a gabanta ita kuma ta kama hannunsa, sannan ta fara magana da Madam Gloria, "wannan ya zama karo na ƙarshe da za ki ƙara saka hannunki ga jikokina, na jima ina faɗa miki hakan da kike babban kuskure ne, ina tsananin son jikokina bana son abunda zai wanzar musu da ɓacin rai ko kuma abunda zai taɓa lafiyarsu". Madam Gloria ta ɗago kai tana duban sirikar tata tace, "Ma! Yanzu ba ki duba yanayin damuwar da nake ciki ba sai ɗan dukan da naima jikanki...ke kenan duk sanda ɗanki ya ƙunsa min kema sai kin ƙunsa min, shikenan ai". Ta ƙarashe maganar tana tasowa ta wuce ta gabansu har tana bangaje Joseph. Ya kalli Kakarsa da damuwa yace,"Granny...". Bai faɗi abunda zai ce ba tasa yatsa a leɓensa, "Shhhh dont stress your self kaji...indai akan banbancin addini ne Mominka ba zata taɓa sauyawa ba, saboda haka kaima kake daina zuwar mata da zancen da ya danganci hakan". Ya ɗaga mata kai, suka maida hankali kan Kukun gida da ke sanar musu cewar Lunch is ready. Nan suka sauka ƙasa inda suka wuce dining section, har tsawon wucewar rabin awa Dad da Mom basu fito ba, dan haka sai su uku suka yi lunch ɗin, su na kammalawa kuma Joseph da Obi suka fita ɗauko Yayansu Emanuel a airpot wanda jirginsu zai sauka da ƙarfe huɗu.
****
A ɓangaren Dad kuwa zaune yake bakin gado, yana shafa kamfutar da ke gabansa, wayarsa a gefe tayi ƙara, ya miƙa hannu ya ɗauka ba tare daya duba sunan me kiran ba, sai da ya kara a kunne daga can ɓangaren aka kira sunansa da, "Major naga kiranka ina bakin aiki shi yasa ban ɗaga ba". Jin muryar amininsa ne yasa shi dakatawa da shafa kamfutar da yake sannan yace, "yayi kyau, nayi tsammanin ma ko kana gida kana hutawa ne". Daga can ɓangaren Major Josiah yace da shi, "ina babu hutu ai, yanzu haka fitowarmu babu jimawa daga meeting da President". Dad ya sauke numfashi yace, "Kuna sane kuwa da garkuwar da akayi ta mutanen da ke kan hanyarsu ta zuwa zamfara state?". Josiah yace,"ƙwarai mun sani". "to amma kuma babu wani mataki da za ku ɗauka akan hakan kenan?". Daga ɓangaren Josiah shi ma nunfashin ya sauke sannan yace,"bamu da ikon ɗaukan wani mataki, saboda ko a yanzu da aka zauna meeting na miƙa wannan issue ɗin, amma shugaban ƙasa yace bai yarda da mu kai farmaki wurin ba...hasalima duk wata magana da muke kawowa akan bada tsaro ga ƙasa sai ya daƙile hakan". "to amma zaman naku akan menene ku ka yi?". "akan basu tsaro ne iyaka yasu bada sauran al'umma ba". Cike da takaici Dad ya girgiza kai sannan yace,"Allah ya kyauta...yanzu abunda nake so da kai Emanuel zai dawo yau, shi ne ina so a haɗa shi da gwarazan securities da zasu raka shi amso mutanen da akayi garkuwa da su". Josiah yace,"babu matsala, we will talk letter yanzu zan shiga office ne". Daga haka suka yi sallama. Dad yaci gaba da scrolling ɗin hotunan waɗanda akayi garkuwa da su ta cikin kamfutar, mata sunfi maza yawa, sai dai abunda ko da yaushe yake ɗaure masa kai shi ne me yasa ba'a garkuwa da christians sai musulmai?, kuma me yasa abun kullum ke ƙarewa akan talaka?
Da dukkan hannunsa biyu ya shafi sumar kansa tare da kwanciya saman gadon fuskarsa na fuskantar POP...ya lumshe ido yayin da hoton wata rayuwa can baya ta shiga haskawa acikin idonsa.
*Bichi.*
"goben ƙarfe nawa zaka wuce?". Baba ke maganar da Amadu wanda ke zaune a gefen mahaifin nasa. "jirgin ƙarfe bakwai zai tashi, saboda haka fitar asuba zanyi inda tsawancin kwana". Baba ya jinjina Kai sannan ya kuma ce masa,"zaka yi kamar watanni nawa kamin ka leƙomu?". "wallah ban sani ba Baba, a yanda nake so dai ace duk wata biyu zanke zuwa, to amma sai abunda ma'aikatar tace". Baba ya numfasa kana yace,"shikenan Allah ubangiji yayi jagora, Allah ya tsare hanya...sai dai idan ka sauka bamu san taya zamu sani ba tunda ba waya a gidan". Ya ɗago da kai ya dubi mahaifinsa cike da tausayawa, yana jin kamar ma yace ya fasa tafiyar, dan tun a ɗazu da suka taru su na masa nasiha sai duk jikinsa yayi sanyi, sai dai babu yanda zaiyi ya san hanyar arziƙi ce ke kiransa. "Baba karka damu dana sauka zan kira wayar Auwalu ɗan gidan Malam Ladan sai ya kawo muku, na faɗa masa zan dinga kiransa yana kawo muku har zuwa lokacin da Allah zai sa ai min albashi na siya muku wayar, ga Lukman sai ya nuna muku yanda ake sarrafata duk da shi ma ba wayewa yayi akanta ba sosai".
Na buɗa baki nace,"tabɗi Ya Amadu Allah kam karka wani sa wannan mara mutuncin yaro ya dinƙa zuwar mana gida, gaskiya ƙwamma ba muyi wayar da kai ba indai haka ne, ranar nan fa ya gama zaginmu a waje wai ƴaƴan me faskaran icce". Mu'azzam ya dokan tsawa da cewar, "dilla can rufewa mutane baki, manya na magana kina sako baki". Na turo baki gaba nace,"Baba fa ya zaga". Yana jifana da mugun kallo yace,"nace ki mana shiru ko, indai ba ki rama ba ai nasa uban ya zaga". Inna Amarya tace, "rabu da ita dan yace Ƴaƴan Me faskare da ba ƴaƴan nasa bane?". Nace, "to ai Inna ba iyaka nan ya tsaya ba, ni dai