NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 35 of 223

mintuna bai motsa ba, sai a san da me gadi ya tashi ya zuge gate ɗin da ake dannawa hon da ƙarfi, bayan da farar motar ta nauso ciki sannan ya haɗe murfin idanunsa ya buɗe kana yabi motar da ido har zuwa wurin da aka tanada na ajiye motaci. Mahaifiyarsa Madam Merry tare da Matarsa Madam Gloria suka fito daga bayan motar kowannensu hannunsa riƙe da jaka da alama daga wajen wani taron suke, bayan wucewarsu ne ɗansa Joseph wanda shi yay tuƙin ya fito daga mazaunin driver shi kuma hannunsa riƙe da jarida, yayi tattaki me ɗan nisa sannan ya tsaya yana nazari, sai ya juya ya koma motar ya jefa jaridar aciki, duk abun da yake idon mahaifinsa na kansa wanda ya fahimci dalilin da yasa ya maida jaridar mota, hakan ne yasa shi ɗan murmusa kuncinsa kamin ya daɗa lumshe ido ya buɗe. Madam Gloria ta ɗauki tsawon daƙiƙa 2 tsaye a bayansa amma sam bai san da zuwanta wurin ba, hakan yasa ta ƙara yin tattaki zuwa gabansa ta tsaya, anan ta fuskanci da gasken bai san da zuwanta ba, domin kuwa kansa a ƙasa yake idanuwansa a rufe. Tayi wani ɗan guntun tsaki na ɓacin rai sannan ta ƙara matsowa kusa da shi sosai ta ɗora hannu ɗaya saman ƙirjinsa, ta ranƙwafo da fuskarta saitin tasa, acikin harshen turanci tace da shi, "Me ya sami Jarumina?, ni ce ko kuma wani ne daga waje?". A yanzu ne yasan da zuwanta wurin hakan yasa shi buɗe ido yana dubanta, gaba ɗaya ya ɗago kai lokaci ɗaya kuma cikin zafin nama yay wurgi da jaridar da ke hannunsa ta baya nan ta sauka a saman fuskar Joseph da ke shigowa, Joseph yasa hannu ya dafe jaridar a fuskarsa kamin ta kai ga faɗuwa ƙasa, tsoron abun da ka iya haifuwa yasa Madam Gloria saurin ja da baya, ta maida kallonta ga Joseph da ke tsaye suka haɗa ido yay mata alama da me ke faruwa, ta ɗaga masa kafaɗa na cewar bata sani ba itama. Ta marairaice fuska tayi ƙasa da murya cikin nuna damuwa ta sake cewa, "Oh Jesus Crise, Daddyn Emanuel me yayi zafi haka?, ko wani abu ka gani a jaridar da ya ɓata maka rai?". Zuciyarsa na tafarfasa ya dubeta cikin ƙarajin murya yace da ita,"wai shin har sai zuwa yaushe ne ƙasarmu zata gyaru ne?, sai yaushe shuwagabanni za su gane al'umma amana ne a hannunsu?, har sai yaushe za su yi hani da aikata ta'addanci?, har tsawon wane lokaci za'a ɗauka kamin gwamnati ta fara martaba jami'an tsaro?, me yasa shuwagabanninmu basa tsoron Allah?". Muryarsa ta fita acikin turancin da ya banbanta dana Matarsa, domin kuwa tamkar baturen america, yaja doguwar ajiyar zuciya sannan ya juya yay tattaki zuwa in da kujera ta ke ya zauna, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana girgiza su. Madam Gloria ta ƙarasa inda yake itama ta zauna a kujerar dake kusa da shi, sannan tace da Joseph ya bata jaridar, ya miƙa mata jaridar, ya fita babu jimawa ya dawo hannunsa riƙe da glass cup da kuma kwalin exotic na pineapple, yaja ƙaramin glass table zuwa gaban mahaifinsa ya tsiyaya lemu aciki sannan ya ajiye, Dad yay masa kallo ɗaya sannan ya miƙa hannu ya ɗauki lemun yasha, ya ƙara damƙe kofin kamar zai fasa shi. Madam Gloria da ta gama karanta jaridar ta taɓe baki tana duban mijin nata tace,"sai kuma me?, wanne abu ne aciki da ya shafeka da har zai saka damuwa irin haka?". Sai kuma taja tsaki ta ƙara cewa,"kayan haushinka yana da yawa, before duk ka ɗaga hankalina, nayi tunanin wata matsala babba ce, kawai sai kake ɗora damuwa akan mutanen da ba addininku ɗaya ba, if ace there are all chritians shi ne sai ka ɗaga hankali irin haka". Ya kalleta yace,"baki gane rubutun da ke ciki bane?". "na gane mana, ba magana bane akan kidnapping da akayi, to kai mene naka aciki?, akwai ɗanka ne ko kuma ɗan'uwanka?, ko kuma ance maka dani akayi garkuwa ko kuma Mama?". "take a look!". Ya faɗi hakan yayin da yake ɗaga mata hannu da dakatarwa Kansa a ƙasa, sannan ya ɗago ya dubeta da jinjinawa rashin tausayi irin nata yace, "Addininmu bai ce muso namu ba, muƙi wanda ba namu ba...to bari kiji, da har yanzu ina kan matsayina na Major General na rantse miki da saina sadaukar da raina wajen ƙwato mutanen nan...ki kwatantawa kanki idan wani naki akai garkuwa da shi ya za kiyi? Ko da ace kuwa kina da kuɗaɗen amso shi, haka abun yake ga ahalin waɗan nan bayin Allah, su na nan hankalinsu ba'a kwance ba...saboda haka ni na ɗaukarwa kaina alƙawarin fidda dukiyar da Allah ya bani wajen ganin na ƙwato su". Yana kai nan ya kwashi wayoyinsa ya fice ya barsu a wurin, mahaifiyarsa da ke hayowa saman benen ta bishi da ido har sanda ya shige ɗakinsa ya banko ƙofa garamm, ta girgiza kai sannan itama ta wuce balcony inda ta sami Madam Gloria tayi jugum, Joseph kuma na gefenta yana maganar cewar, "Mom ki dinga shiru da bakinki akan nuna tribalism a gaban Dad tunda baya so, hakan shi ne kwanciyar hankalinki dana kowa ma acikin gidan nan...eventhough nima ba wai son muslims nake ba, amma a ɓangaren kidnapping ina tausayin kowa musamman ace mata ne akayi garkuwan da su". Cikin fusata ta kai hannu ta bugi bakinsa, hakan yasa shi tsuke baki yay shiru yana aikin sosa wurin. Madam Merry wa
🏠