NOVEL SHARES -
incikin da yake ciki na daɗa bayyana a saman fuskarsa, kamin ya kada baki yace,"tabbas duk wani me aikin alkhairi domin sarki rabba baya son godiya sai adu'a". Aiko nan ya shiga yiwa Bella adu'oi ita kuma tana mai murmusa fuskarta da alama tana jin daɗin adu'ar.
Ta ɗau tsayin wasu daƙiƙu tana kallona ba tare dana sani ba, sai a yanzu dana bar kallo ga Ya Kabiruna na dawo da shi gareta, muka haɗa ido da ita ta sakar min siririn murmushi ni kuma nai saurin sauke kai ƙasa ina wasa da yatsuna.
Na jiyo muryarta tana cewa,"Ashraf ba dan na san duka ahalina ba, da sai nace Maryam jinina ce". Taci gaba da kallona tana ci gaba da faɗin,"idan kayi mata duban tsanaki akwai wasu kamanni sirrantattu irin na jinina a tare da ita". Ta sauke numfashi kana tace,"ina ma ace ke jinina ce Maryam da naji daɗi, kema kuma da kinji daɗi, za kiga gata da ƙauna daga wurina, za ki mo re jin daɗin rayuwa, tun shigowarki a kallo ɗaya naji ina sonki". Ta dubi su Adawiyya tace, "kuma fa ina sonku, amma naji nafi son Maryam". Ta kamo hannuna ta haɗe da nata ba tare da ta ji ƙyanƙamina ba, sannan tace,"idan har kin kammala sakandire nan da shekkara huɗu to zan tafi da ke ethopia ki ƙarasa karatunki acan...me kike son zama idan kin gama karatu?". Ina murnushi nace, "Gwaggona tace Lauya zan zama". "to ki dage kiyi karatu sosai sai Allah ya cika burin mahaifiyarki". Dukanmu muka amsa da amin inda nima nace, "Bella Allah ya ƙara miki llafiya da nisan kwana". Jin shiru banji ta amsa ba yasa na ɗago ƙwayar idona ina dubanta, wadda idonta ya karkata gefen kunnena ta ɗaga yatsa tana nuni da wajen, maganar da zata yi ta yanke a san da Jakadiya ta faɗo ɗakin tana sanar mata da cewar tayi baƙi daga Sudan. Nan Bella ta miƙe ni kuma nabi bayanta da kallo, sai dai kuma abun da na gani a bayan wuyanta ne yasa na miƙe tsaye zumbur cike da al'ajabi. Na rumtse ido na dafe goshi hoton abubuwa da dama na haskawa acikin idona.
Mun ci abincin da aka kawo mana me daɗin gaske, ban kuma ji kunya ba na juye saurana a leda in kaiwa Gwaggona da Inna Amarya. Bamu muka dawo gida ba sai magriba, cike da sha tara ta arziƙi da muka samo a wurin Ammi da Bella.
_____________________________________
*Binti* *idris* *traditional* *herbal* *medicine* *and* *more*
Sanyi mugun ciwo ne sanyi shine babbar cutar da take taka rawa wajen raba ma'aurata ta hana su suku da jin dadi yar uwata kada ki tsaya kunya ki tashi ki nemi magani domin babu cutar da ubangiji ya saukar be saukar mata da maganin ta dan haka ni *Bint* *idris* *ibn* *Abdulwahab*
Nake Kira gare ku yan uwana mata da maza kuyi maza ku garzayo ku nema wa kanku lafiya ga masu neman karin bayani sai su tuntube ni ta wanan number Kira ko WhatsApp 07066959285
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
INA MASU FAMA DA DATTIN MARA KO AMOSANIN MARA WLH GA QAQQARFAN MAGANIN WANKIN MARAR MACE KO NAMIJI
DA KASHE DUK WANI SANYIN DAKE MARAR MACE KO NAMIJI
1* QURAJEN GABA
2* 'DA'DEWAR GABA
3* SA'BAR GABA
4* QAYQAYIN GABA
5* WARIN GABA
6* RASHIN SHA'AWA
7* RASHIN NI'IMA
8* YAWAN'BARIN CIKI
9* JIN ZAFI LOKACHIN SADUWA
10* RASHIN JIN DADI YAYIN SADUWA
11* Tsinkewar maniyyi rashin haihuwa
12*ciwan jiki kai kayin jiki
13yawan ciwan kai
Da dai sauran su
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Maza ku garzayu kuzo ku nemi naku maganin a farashi mai sauki munyi ragi kasu talatin cikin Dari na kayan mu kada ku sake wanan garabasar ta wuce ku yan uwa 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*11)*
*Area 4, House NO2, Asokoro District, Abuja.*
Gida ne na gani na faɗa wanda aka narka dukiya a wajen gininsa, tun daga waje kana iya ganin Ƙaton balcony da ke fuskantar gate ɗin gidan, dogon namiji ne me cikar zati yana tsaye ne daga cikinsa da irin tsayuwa ta jaruman sojoji ya sarƙe hannayensa ta baya, jikinsa sanye da t-shirt irin ta kakin soja haɗe da baƙin wando jeans, sumar kansa ba wata mai yawa bace sai dai irin askin da ke sumar aski ne bana musulmi ba, idanunsa kewaye da siririn medical glass. Farin dattijo ne kyakykyawa me kimanin shekaru 56-57, a irin tsayuwar da yay zaka ce ko an dasa shi ne a wurin, hancinsa ne kawai ke fitar da numfashi sai ƙwayar idonsa da ke kan get ɗin da yake fuskanta, a kallo ɗaya zaka yi masa ka gane yayi nisa acikin zurfin tunani. Har tsawon wucewar wasu