NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 33 of 223

kalli su Adawiyya da ke kan kujera zaune lafiya, na mayar da kallona ƙasan ƙafata a san da wata baiwa tazo gabana tana tambayata,"me ya faru?". Nace musu,"babu komai, da na zauna a kujerar ne sai naji kamar zan faɗa ciki, laushinta yayi yawa". Takaici ya kama Adawiyya da Habiba dan ina kallo suka harareni, su a yanda suke zaune kamar ma sun saba da zama akan irin kujerar ne, akayi-akayi kuma na koma na zauna naƙi nace ni dai ba zan iya zama akai ba. "ƙaraso da ita nan". Cikakkiyar muryar tsohuwar ta ambata a lokacin da ta ɗago da dubanta kaina, tsoro da fargabar abun da zai faru ya kamani, nai saurin zube gwiwoyina ƙasa na shiga bata haƙuri. "dan Allah ranki ya daɗe kiyi haƙuri ki gafarceni, wallahi ba da gangan nayi ba, ban taɓa zama bane akan irin wannan kujerar mai kamar auduga, su kansu ƴan'uwan nawa sunyi ƙarfin hali ne, kiyi haƙuri dan Allah kar a hukuntani, ni ɗin ƴar ƙauya ce ɗiyar talaka". Sai dai kuma me, duk magiya da ban haƙurin da nake Bella bata ji ba, hasalima kanta na kan wasu takardu ne da rubutun ciki ke kamar jagwalgwalo, haka Baiwar ta kamo hannuna ta kawoni har gaban Bella, nasa hannu na goge ƴar guntuwar ƙwallar da ta sakko min, nayi wurƙi-wurƙi da idanu ina jiran tsatstsaraun hukuncin da za'a yanke min, dan na taɓa jin labarin gidan sarauta basa yin da sauƙi, tausayin iyayena ya kamani saboda halin da za'a jefasu aciki idan suka ji cewar masarautar ta kamani da aikata wani laifi. Bata ɗago ba har tsawon daƙiƙa biyun dana ɗauka gwiwona zube a gabanta, sannan ta kuma kallona muka haɗa ido gabana ya kuma faɗuwa saboda kamanninta, muryar nan tata me baƙuwar hausa tace da ni,"zauna akan wannan". Ta faɗi hakan tana min nuni da tum-tum ɗin da ke ƙasa gefen ƙafafunta, hannu na rawa na janyo shi na zauna ina rumtse ido, dan shi ma taushi ne da shi sai dai bai kai kamar kujerar ba. Wannan lokacinma ba da hausa ta yiwa Suhail magana ba, da yarensu ne. "taya ka san Kabir?". Yace da ita,"zuwan da muka yi ƙasar nan a wancan shekarar, muka raka Madaki masallacin liman a ƙauyen Saye. To anan muka haɗu da shi har muka taɓa hira dan mun jima tare, kyawun hali da nagartarsa dana karanta a lokaci ɗaya yasa nayi sha'awar haɗa alaƙa ta abota da shi, hakanne yasa a wannan zuwanma na kai masa ziyara, saboda lokacin da muka baro airpot Sarkin gida ya biya damu ta gidan Liman dan isar da saƙon Me Martaba, shi ne a lokacin tahowarmu nace da Sarkin gida ya tafi kawai zamu iso, da taimakon wani yaro ɗan gidan Ladan muka sami kwatancen gidansu, dalilin da ya sa ma muka kwana acan gudun faɗan Ammi kasancewar dare yayi, Bella su ɗin mutanen ƙwarai ne domin sun karramamu ba tare da sanin su wane mu ɗin ba". Bella ta jinjina kai sannan tace da Ya Kabiru,"na gode da karrama min jikoki da gidanku suka yi, haƙiƙa ina mutunta duk wanda ya karrama jinina, ina kuma kyautatawa agare shi, saboda haka ku saki jikinku daga yau ɗin nan acikin masarautar bichi ɓangaren Bella ku ƴan gida ne ba baƙi ba". Ta juya ta dubi kuyangar da ke tsaye kaina sannan tace da ita,"ace Jakadiya ta haɗo musu abun sakawa a baki". da sassarfa Kuyangar ta juya domin cika umarnin shugabarta. Bella kuma taci gaba da magana da Suhail, "kai kuma wane irin tukwici ku ka yi musu game da karramawar da suka yi muku?". "na faɗawa Ammi sai tace babu wani tukwicin ban girma da za'ayi musu har su kasa mantawa damu sama da ɗaukar nauyin karatun ƴaƴansu, yanzu haka zuwan nan da suka yi sun zo karɓar kayansu ne na tafiya makarantar kwana, shi kuma Kabir ta ba shi ɗaya daga cikin shagunanta dake cikin gari". "shagon ɗauke yake da kaya?". Ta tambaya, Suhail ya kaɗa mata kai,"a'a Bella, babban shago ne dai, zai nemi jari ya zuba". "zancen banza kenan, mutumin da ya bawa naka makwanci, ci da sha, ba kyara ba walaƙanci ai yafi ƙarfin wannan ƙaramar kyautar a wurinka...a yau ɗin nan a nemi kaya masu kyau da inganci a zuba masa a shagon, sannan a mallaka masa maƙullin gidan Hauwa'u da yake Estate ɗin Madaki, dama na gaji da ganin gidan a haka, idan auransa ya tashi ayi min magana...yayi karatun boko?". "ehh yayi yana da certificate na diploma akan aikin wutar lantarki". "masha'Allah, duk da su ɗin mutanen ƙauye ne amma basu bar kansu da duhun jahilci ba, Allah yaywa iyayenku albarka...Suhail a sama masa addmission a ƙasarmu abar tunƙahona". Ta dubi Ya Kabiru tace, "za ka iya zuwa ethopia kaci gaba da karatu?". Kan ya bata amsa Suhail ya amshe da cewar, "ai Bella burinsa kenan yaci gaba da karatu sai dai rashin dama". Tace, "to a mayar da gurbin addmission ɗin da Fawwaz ya samu a matsayin nasa, ina so jirginsa ya ɗaga a ƙarshen wannan watan". Ya Kabiru bai san sanda ya zube gwiwoyinsa ƙasa ba ya shiga jero tarin godiya gareta, Sai dai baija da nisa ba Jakadiyar da ta shigo kamar an jefota ta zube tare da dakatar da shi, "Bella tana yi ne domin Allah, bata son godiya, kayi shiru da bakinka a wurin nan idan kuma baso kake ka fuskanci wani hukuncin ba". Ya Kabiru ya jinjina kai alamar yaji, far
🏠