kanta da son sanin yanayin da take ciki ayanzu, da kuma son ƙara ganin fuskarta dan tabbatar da ganina wanda nake jinsa matsayin hasashe ko gizau.
Lallai Masarautar bichi da girma take, dan baki ma yayi kaɗan ya misalta girmanta saboda gari ce guda. Tun da muka fito haraba nake bin masarautar da kallo da burgewa, komai nata mai kyau ne da ƙawa, tsaruwarta har ɗaukan ido yake. Jefa idanuna nake ta ko'ina ina duban Bayi da Kuyangu da ke kai komo a ayyukansu, ƙwarai ne tun daga waje zaka gane tabbas an narka dukiya wajen tsara masarautar balle kuma ka shigo daga cikinta, idan ma ka shigo matsayinka na baƙo zaka kasa tantance wacce ƙofa zaka sada kanka saboda yawan ƙofofinta.
Muna nan tsaye a inda su Suhail suka barmu suka dawo muka ɗau wata doguwar hanya mai cike da shuke-shuken fulawowi masu ƙamshin gaske da sanyaya wuri, a lissafin da nai bayan ƙofar Ammi ta biyu da muka fita wannan da muka shiga itace ta shida, tafiya muke muna wuce fadawa da ke tsaitsaye tun daga shigowar get ɗin da kuma tsirarrun bayi dake kai komo, duk kuma ta inda muka gimla sai an duƙa anyi gaisuwa da kirari ga Suhail da Ashraf. Mun yi tafiya me nisa naja na tsaya dan tun ɗazu ƙafata ta gaji, nace da Suhail"Buzu wai ina zaku kaimu? ko Anan makarantar ta ke ne?". Ya waigo ya dubeni tare da bani amsar,"a'a ba nanne makarantar ba, nan ɓangaren Kakarmu ne Bella, zan kai ku ku gaisheta ne, kiyi haƙuri ai an kusa zuwa?".
Na gyaɗa kai kawai Ya Kabiru ya kama hannuna yana ce min raguwa.
a yanda na sani tuta a makaranta ne ake dasata, tun da akwai tutar najeriya a makarantarmu, to amma isowarmu gejin da zai sadamu da wata ƙatuwar turaka sai naga dashen tuta a ƙofar wurin daga ɓarin dama, ƴan sanda biyu na gadinta kowannensu riƙe da bindiga a hannu sun ƙame tamkar dasa su akayi, kalar tutar kore da yelo da ja, tare da kwalliyar tauraro a tsakiya me kalar yelo da shuɗi, na ɗauka tsawon daƙiƙa biyu ina kallon tutar da son sanin ko tutar wacce ƙasa ce, sai dai duk nacina na kasa saboda bata ɗaya daga cikin tutocin da aka koyar damu a makaranta.
Cikin makeken falo na gaske muka sanya ƙafafunmu, falo me ɗauke da kayan sarauta ta ko'ina, ni da ƴan'uwana da muke baƙi muka shaƙi ni'imtaccen ƙamshin da ko a gidan waziri da suke gidan turare babu irinsa, da ace zan sami dama da babu abunda zai hana ni roƙar a sammin turaren, nima na kaiwa Gwaggona da Innata suke sawa a ɗakinsu, saboda duk wanda yaji wannan ƙamshin yasan ƙamshi ne na musamman, yanda nake ta zuƙar ƙamshin a hancina yasa na tuna da furucin Sadiya a wata rana, tace ke dai Mairo idan ba'a saceki a ƙamshi ba to za'a saceki a kyau, nai ƴar dariya kawai.
A irin yanda kuyangun falon ke nutse da takatsan-tsan ɗin ganin sun cimma ayyukansu zaka fahimci cewar me ɓangaren bata wasa bace, wata tsohuwar mata ce zaune kan kujera irin ta sarauta me shilla mutum a hankali, tana kishigiɗe a jikin kujerar yayin da hannayenta duka biyu ke kan hannun kujerar ta ko wanne ɓari, idanuwanta na ɗauke ne da siririn farin gilashi, yayin da bayi kusan shidda ke tare da ita, biyu na tsaye ta bayanta su na mata firfita, biyu kuma na duƙe ne a ƙasa suna matsa mata ƙafafu, sauran biyun kuma na daga tsaye a gefen hannun damarta, ɗaya acikinsu tana riƙe da ƙaton faranti me ɗauke da kayan marmari, ɗayar kuma ita ce me ɗauka tana sakawa tsohuwar a baki wadda ke ci a hankali. lallai anan ake sarauta me cike da ƙarfin izza da ƙasaita, anan kuma usulin kyan halitta yake da ido ba zai so ɗaukewa daga kansu ba, gabana ya faɗi a san da muka haɗa ido da ita ta cikin gilashinta, na saurin ɗauke idona ina ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yayin da kuma hoton fuskokin mutum uku suka shiga haskawa a cikin idona, na haɗiye guntun yawu a maƙoshina sannan na nemi wurin da Suhail yay mana nuni na zauna .
"Ranki ya daɗe barka da wannan lokaci". Ashraf da Suhail suka ce da ita bayan ta baro kan waccen kujerar da take ta dawo ta zauna akan wata kujerar ta daban, ta mayar masa da magana acikin yaren da ban san wane yare bane amma yana shige da larabci, sun daɗe su na magana da ita acikin wannnan yaren kamin Suhail yace,"Bella wannan sunansa Kabir abokina ne, waɗan nan kuma ƙannensa ne, sun shigo masarautar ne shi ne nace bari na rakosu wurinki ku gaisa, su na da mutunci sosai domin a gidansu muka sauka ranar da muka shigo cikin garin nan, an karramamu an mutuntamu a gidansu ba kaɗan ba". Suhail na rufe baki daga Ya Kabiru harmu muka rissinar da kai muna miƙa mata gaisuwa, bata buɗe baki ta amsa ba illa iyaka ɗaga mana kai da tayi, sannan naga tayi nuni wa Suhail da hannu, shi kuma ya dubemu yace an bamu izinin zama kan kujera, to a raina saina kawo ko tsohuwar bata magana ne, bebiya ce.
Muna zama kan kujerar nayi zumbur na miƙe a zabure ina aikin zare idanu ina mammatsa hannuna tamkar mara gaskiya, nan kuwa tarin kunya ce ta lulluɓeni duba da yanda aka zuba min ido, Suhail da Ashraf suka haɗa baki wajen tambayata,"lafiya?". Ban basu amsa ba sai dana