NOVEL SHARES -
a magana acikin wani yare na daban wanda ba hausa ba, hakan yasa ban fahimci mai suka ce ba, sai naga ta miƙe ta wuce ciki ta barmu da Jakadiyar da ke mana bayani da kyautar kayan tafiya makaranta da Ammi tayi mana.
*TALLA! TALLA! TALLA!.*
Ina son shi yana sona, bayan dukkanin yarda da Amana ya gujeni, Soyayya, Ƙauna, Kulawa, Mutunta juna, ganin ƙimar juna suka rushe a bisa *WATA LALURAR*.
Me nayi mishi? a wane dalilin zai
juyamin baya? Me yasa zai gujeni ba tare da sanar da dalili ba?.
A rana ɗaya, a lokaci ɗaya ya ƙyamace ni, ya tafi saboda kawai giftawar wata ƙaddara wadda bani na ɗorawa kaina ba.
cutar da ta zama rubutun ƘADDARA ce agareni, wadda ta ke tamkar ZANEN DUTSE. na shiga damuwa, na shiga ruɗani, na shiga ƙunci, nayi danasanin haɗuwata da shi, naji dama ace banzo duniya ba, naji dama ban ɗanɗana zumar soyayya ba, a wannan lokacin duk wani saurayi ƙyamatata yake, Akan wane dalili hakan ke ta faruwa?
*WATA LALURAR BISA ƘADDARA!!!*
*Read Out in BANZA BATA KAI ZOMO KASUWA by Mommy Hafsatou.*
*#Comment & Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*MissAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
*10)*
Ni dai bin bayan Ammi na yi da kallo har san da ta shige wani ɓangare da ke cikin falon, bin ta nake da idanu da sauyin yanayin da naga ta samu cikin lokaci ƙalilan, jikinta a saɓule hakana walwalar da ta shigo da ita a ɗazun ta ɗauke, a zuciyata na shiga tunanin abun da zai sauyata zuwa wannan yanayi wanda yafi kama da alhini, sai dai mamakina yafi ta'allaƙa akan abun da zai sata a damuwa alhalin tana cikin wannan daular?, Hoto! Kalamar hoton ta sake haskawa acikin kaina ina mai tuna furucinta ga Suhail, lallai ta sami sauyin yanayin ne daga san da ta ɗaga idonta ga jikin bangon gabas sannan tayi furucin ga Suhail, kenan rashin hoton shi ne ya sata a wannan damuwar?, to hoton menene?.
Na sami katsewar tunani a lokacin da Jakadiyar ke min maganar na gwada takalmin makaranta, kuma ko da na gwada yayi min kaɗan kasancewar ina da doguwar ƙafa, Suhail ya jijjiga kai yana cewa, "ke ko Mairo wace iriyar ƙafa ke gareki haka". Murmushi nayi kawai idona na kan takalmin da nake jin dama a bar min shi a haka saboda kyan da yayi, sai dai babu batun hakan dan tuni Ashraf yace Jakadiya tasa a kayan marayu.
Suhail ke tambayar lamba nawa nake sawa takalmin nace nima ban sani ba, Ya Kabiru yace masa ai da yake anfi siya mana silifas lambar bai zama lallai tazo ɗaya da irin wannan ba, amma kambas ɗin da ya siyo min kwanaki lamba arba'in ne, to dai da aka rasa lambar da za'a bawa ƙafata ƙarshe sai takalmansu suka ce na gwada, ina gwadawa ina ƴar dariya ganin ƙafata cikin takalmin maza, kuma daga kan takalmin Ashraf har zuwa na Ya Kabiru kowanne yay min kaɗan, sai da Jawad wan da kansa ke kan wayarsa yace nazo na gwada nasa, ina kuwa sakawa tamkar nawa yay min dai-dai, har Ashraf ke zolayata akan ko shi za'a bar min kawai, nace,"tabɗi me zanyi da takalmin Jawad, duk da yayi min kyau amma bana so, a sayo min sabo irin na ƴan'uwana".
Ni da ƴan'uwana mun yi murna sosai da irin kayan da aka bamu, kayan da bai zama lallai ɗan wani mai kuɗin ma ya mallakesu ba cewar Ya Kabiru, ni a ɓangaren kayan zaƙi da aka haɗa mana ma babu ɗaya da na taɓa cin karo da su a rayuwata, ina jin Ashraf na faɗin ai bamu za muke girki da kanmu ba makaranta ce take dafawa, hasalima ko yaji aka kama mu da shi sai an ƙwace kuma sai an horar damu, saboda haka a kula, ya kuma ƙara jaddada mana da cewar duk wani abu da muke da buƙata ko kuma aka buƙata a makaranta mu kira Suhail.
Ko da aka zo ɓangaren cike takardun makaranta Suhail yace sam ba za'a saka min Mairo Adamu ba kamar yanda Ya Kabiru ya faɗa, yay ta masa tsiyar idan shi ɗan kauye ne sai akace masa kowa ma zai zauna a irinsa ne, dan haka ya maida min da Maryam Adam Bichi, Adawiyya ma Jakadiyya tace ai Rabi'a ne asalin sunanta, dan haka ita ma Suhail bai sanya mata Adawiyya ba, Rabi'a Adam Bichi shi ne sunanta kamar yanda ya faɗa, Habiba kuwa sunanta ne dama aka saka mata. Na ɓata fuska na tubure akan cewar ni dai a maida min da sunan da Babana ya raɗa min, bana son wani Maryam, Ashraf yace to ai ko wurin Baba akaje zai ce Maryam shi ne usulin sunana ba Mairo ba, Jawad da ke gefe yana aikin latsa waya yake faɗin haka za'a kaini makarantar ƴan gayun ina masu ƙauyanci, Na harare shi ta ƙasan ido nace ina ruwansa, ni kaina daga irin kayan da naga an haɗa mana da irin yanda Ashraf ke lissafowa Ya Kabiru doka da ƙa'idojin makarantar nasan cewar ba irin gajigari-gajigari bace, makaranta ce babba.
Bayi huɗun da Jakadiya tasa aka kira mata su ne suka ɗebi akwatunnan kayan da bakko suka fita da su zuwa mota.
Naso ace kamin fitowarmu na ƙara ganin Ammi, dan lokaci ɗaya naji matar ta shiga raina, ina kuma sonta da tausayinta tare da son kasancewa tare da ita, dan wallahi duk wannan murna da zumuɗin da nake akan nuna mana kayanmu gaba ɗayan hankalina yana can