NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 30 of 223

nunsa daga saman wuyana na wurgar da irin yanda shi ma zaiji zafi, na jiyo na fuskance shi da ƙarfi nace,"Allah ya isa mugu azzalumi, kuma wallahi nima sai dai idan baka shigo ƙauyenmu ba sai na rama". Ya kuma kawo hannunsa zai gwaɓe min baki maganar dattijuwar da ke shigowa ta dakatar da shi. "Jawad me na ke gani haka?, yara na wajenma kai ba zaka ƙyale ba". Yay min duba kaɗan sannan yace da ita, "Ammi bata da kunya ne, ba ki kalla yan da take zumɓurowa mutane baki ba". Ta nufi kujera tana zama tace,"wani abun kayi mata shi yasa, ya kamata ka rage zafin zuciya, haka kawai dai yarinya ba zata zumɓura maka baki ba babu abun da kayi mata, wuce ka bamu wuri". Maimakon ya wuce kamar yanda ta umarce shi sai ya nemi ɗaya daga cikin wasu tsinannun kujeru na alfarma ya zauna akai, ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yaci gaba da danna wayarsa. Ni kuma na tsuguna na gaida matar, ban san ya akai ta lura da goge ƙwallar da nayi ba sai ji nayi tana cewa,"ka kalla har kuka sai da ka sanyata tsabar mugunta irin taka Jawad, yarinya taso kizo nan kinji, ya sunanki?". Nace da ita, "Mairo". Kan tace komai Jawad ya bushe da dariya yana cewa, "ji wani suna wai Mairo, kai ƴan ƙauye ma da kayan haushi su ke". Na ɗago kai na dube shi nace, "kaima ai sunan naka ba daɗi ne da shi ba, mene wani Jawad ko daɗin ji babu suna sai kace za'ai amai". Wata tsohuwar mata da ta shigo ta doka min tsawa da cewar ya isheni haka ko yanzu asa bayi su sokeni tun da ina yiwa Yarima rashin kunya. Na harareta ta ƙasan ido sannan nayi tattaki zuwa gaban dattijuwar kamar yanda ta umarce ni, kuma har na ƙarasa gabanta kaina na ƙasa ban ɗago ba dan tun shigowarta ma ni ban kalleta ba, sai yanzu da ta sa yatsunta ta ɗago da haɓata tana cewa, "ba kyau yiwa Babba rashin kunya karki ƙara kinji Maryama, idan kuma ba haka ba zansa a cire sunanki daga waɗanda za'a kai makaranta, kina so nayi hakan?". Na kaɗa mata alaman a'a, take kuma Yawun bakina ya ƙafe da amsar da zan bata, sakamakon kallon fuskarta da nayi wanda ta sani faɗuwar gaba da ban da taɓa jin irinta ba. Kallon fuskarta nake da ɗumbin mamaki da al'ajabin kamannin da nagani a fuskarta, kamannin da suka so ruɗar dani suka kuma nemi zautar da ni. Na rumtse idona sosai ina jin shigar wani abu ajikina dalilin kamo hannuna da tayi ta zaunar kusa da ita, in banda kar nayi saurin rantsuwa zan rantse nace hannun nan ya taɓa riƙeni, Na ƙara kallonta kamin na lumshe ido, idanuna da ke rufe na hasko min hoton halittar dana jima da sani a saman fuskar wannan matar, yanda zuciyata ke ayyana min shi ne kawai mafarki nake, dan haka na buɗe idona a zabure na saukesu akan manyan akwatuna guda uku da aka aje agaban Ammi, tare da jakar bakko guda uku suma shaƙe da kaya, hakan ya kuma tabbatar min dai da ba mafarki nake ba, ta gefen ido nake bin Ammi da kallo ta yanda ba zata gane ba har san da na sauke idona kan zarazaran yatsun hannunta, ni dai tabbas idan ba tunanin da ya cika min kai a kwanakin nan bane ke neman zarar dani ba, to babu tantama akan abun da idanuwana suke gane min. Ya Kabiru da shi da Suhail su kai sallama a falon, hankalin kowa ya tattara kansu ban da ni, wacce na zuba idanu a wuyan Ammi da son gano abun da nake zargi, sai dai har na gama ƙare mata kallo ban hasko komai ba. Na maida hankalina ga maganar da ake wacce ta shafi tafiya makarantarmu, Suhail ke cewa da Ammi, "Ammi ba dai Mairo har ta zama ƴar gidanki ba". Tai murmushin manyace kana tace masa,"ka bari Suhail, yaron nan Jawad ne daga shigowarsa ya sata kuka, ko ce masa akai su Ziyan ne da ya saba cin zalinsu". Wanda ya shigo bayan shigowar Ya Kabiru yana zama kan kujera yace,"to ai yarinyar ce kamar su Ziyan ɗin, gata nan kamar a hure ta faɗi, kuma da alama abun da ya tsana tayi masa na turo baki dan gashi nan na gani da idona, kinga ko Ammi ai dole ya sata kuka". Na ɗago ido na kalle shi ina daɗa turo bakina gaba nace,"ni fa bakina ne a haka". Kowa na gurin ya dara har da Ya Kabiru, shi kuma wanda naji Ammin ta kira da Ashraf ya daɗa cewa, "A'a Mairo wannan ɗan ƙaramin bakin naki kam da gani da gan-gan kike turo shi". Sai kuma ya gyara zama yana fuskantar Ammi wacce ke complain ɗin wai Suhail ya cire mata hoto. Shi kuma yana cewa ba yin kansa bane Mai Martaba ne yasa shi, ta ɗan kaɗa kai kaɗan kana tace, "ai shikenan, amma sanin Mai Martaba ne hoton nan shi nake gani naji daɗi a ƙasar nan...amma ba komai Suhail kai da ka biye masa naka laifin zanta gani". Ta ƙarashe maganar da murya mai ban tausai wadda har sai da na juyo na dubeta, dan a yanda muryar tata taso sarƙewa sai tai min kama da sautin dana taɓa ji, sai dai ba zan tantance sautin wane ba. Ashraf yace,"Ammi mun gama komai dangane da tafiyar yaran nan, sai dai fa da ƙyar muka shawo kan Baba ya amince, dan haka Gwaggonsu da kuma Inna Amarya su na miƙo tarin godiyarsu ga wannan masarauta da kuma shi Suhail da ya zama sila, irin tarin adu'oin da su kai sai dai nace kema ki bisu da irinsu kawai". Ammi ta gyaɗa kai sannan ta mayar masa d
🏠