NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 3 of 223

aƙura sannan Baba yake amsar bashi, shi ɗinma kuma a wurin Bala ne kawai, kuma baya wuce dubu ɗaya ƙasa da hakan, dama ni irin wannan wulaƙancin nake gudu, banda tozarci a gaban mutane yake cewa ayiwa Malam tuni da kuɗin da yake binsa, sanin kansa ne ci da sha da sutura basu gagaremu ba, muna da rufin asirin da munfi ƙarfin roƙa a wurin wani, haka kuma Baba yanada wadatar zucin da babu mai yi masa kallon faƙirin talaka, balle har ake yamaɗiɗi da shi a bainannasi ana cewa ana binsa dubu huɗu, me akai akayi dubu huɗun, na tabbata da Inna Amarya tasan da wannan bashin da tuni ta biya, idan ba ita ba Ya Amadu tunda shi yafi Ya Kabiru ɗan samu duk da cewar shima buga-buga ce yake yi ya samu. Shigowarmu Babu wanda na kula, na saki hannun Ya Kabiru na shige ɗakin Inna Amarya, dukkuwa da cewar kowa na zaune tsakar gida za ai karin kummalon safe, tunda na shiga ɗaki na kifa kaina da gwiwata ban ɗago ba har tsawon wucewar wasu daƙiƙu masu yawa, Inna Amarya ta shigo tana ta kiran sunana amma ban amsa ba, tazo ta ɗago kaina, ta zaro ido tana kallon fuskata dana haɗa uban zufa kace ruwa aka sheƙa min, idona yayi jajur duk sanadin ɓacin rai, da ace Bala iyaka mu da shi yay maganar ba zan damu kamar haka ba. Tayi salati ta sanar da ubangiji, "Mairo lafiya? Wa ya ɓata miki rai?". Bance mata ƙala ba sai rumtse ido danayi sosai tare da jinginar da kaina jikin bango, tayi tambayar duniya akan meke damuna ban bata amsar ci kanki ba. Har ranta ya ɓaci ta tashi ta fita ta bani wuri, ina cikin wannan yanayinne na neman mafitar yanda za'ai a biya bashin da ake bin Baba, sai naji an dafa goshina, da lallausan hannu mai cike da wata iriyar ni'ima, na buɗe idanuna na saukesu akan mara lafiyar gidanmu wadda tun tasowarmu mukafi yi mata kallo da mahaukaciya, shekaru goma sha huɗu kenan haka na taso na ganta bata ummm bata um-um, sai dai tabi mutane da ido kawai, tun tana bani haushi ma har ta fara bani tausayi, saboda duk sanda na kalleta idanunta cike yake taff da ruwan hawaye, ni nama rasa wanne irin ruwan hawaye ne da basa zuba sai dai su tsaya acikin ido. Yanda na ƙura mata ido ina kallonta sai naga ta rufe nata idon, yau ranar farko da naga wannan ruwan hawayen sun zuba tsawon shekaru bakwai, tayi zaman raƙumi tare da kamo kaina ta kwantar bisa cinyarta, ƙirjina ya shiga harbawa, faɗuwar gaba ta tsananta gareni, ban san dalili ba, amma dai na tsinkayi zuciyata da abinda bata taɓa ji ba sai a wannan cinyar, ko kaɗan banji ƙyanƙyaminta ba, dukkuwa yaran gidanmu har toshe hanci suke idan suka zo wucewa ta kusa da ita, to amma ni sanin da nayi mata na samun kulawa daga wurin Gwaggona yasa bana ƙyamarta ko kaɗan, dan a kullum Gwaggo na dafa mata ruwan zafi ta rakata bayi tayi wanka ta bata kaya masu kyau ta saka, ta kuma fesheta da turare masu ƙamshin gaske, irin sittirun da take sakawa ya banbanta da irin wanda muke sawa, namu sittru ne irin na ƴaƴan Malam Audu, ita kuwa duk sitturar data saka sai naji an magantu akai, sai dai idan ba'ayi baƙo ba, ananne zakaji yana faɗar darajar kayan dake jikinta, kuma ni tunda nake da Gwaggona bata taɓa saka kuɗinta ta ɗinka min sutura ba, amma tayi ta ɗinkawa mahaukaciya, ni sai dai Inna Amarya ko kuma kakarmu Yagana, na kanji haushi sosai na cewa Yagana ni nasan Gwaggona riƙona take ba ƴarta bace ni, tunda bata siya min kaya da kuɗinta sai dai ta siya wata mahaukaciya da ta tsinto, kuma ma kaya masu tsada, dan haka ni ba ruwana da ita ko gaisheta na daina yi, wataran har na kanyi tantamar inda Gwaggo ke samun kuɗin da take siyarwa mahaukaciyar gidanmu kaya nake, domin wataranma idan naji kuɗin wasu kayan sai naga ko jarinta na barkono da kuka aka tattara bai zasu kai wannan kuɗin kayan ba, idan na ishi Yagana da mita sai dai ta kalleni tace Yaro yaro ne, ni kuma hakan na ƙara ƙufular dani. Ina kwance akan cinyartata na lumshe ido tare da shaƙar ni'imtaccen ƙamshin dake fita daga jikin zanenta, naji yatsun hannuna sun sarƙe acikin nata, da ɗayan hannunta kuma tana shafa sumar kaina a hankali, lokaci ɗaya naji na fara samun sassaucin raɗaɗin zafin da nake ji a zuciyata, nutsuwar da nake neman rasawa ta dawo, har ina sauke ajiyar zuciya. Can kuma sai nayi zumbur na tashi daga saman cinyartata, na waro ido ina kallonta, ni gani nake idan aka mata magana baji take ba, tunda ko kayi sai dai ta bika da ido kawai, na yatsina fuska na shiga yi mata alama da hannu, ina nufin ta tashi ta fita kar Gwaggo tazo ta sameta, saboda ba zan taɓa mantawa ba da wata rana, bayan Gwaggo ta gama shiryata tana zaune can wajen zamanta a tsakar gida, dama sai dare yayi ne ta ke shiga ɗakin Gwaggo tayi bacci, a wannan lokacinne ina zaune kusa da ita ina mata labari, sai ga Gwaggo tazo ta hauta da faɗa sosai akan ba ruwanta da ƴarta karta ƙara dosar inda nake, idan ba haka ba zata saɓa ma ta, in bata yi wasa ba ma zata koreta daga gidanta, a ranar har naji haushin Gwaggona saboda rashin tausayin da ta nuna akan mara lafiya, na kuma jima ina cewa Allah ya
🏠