n da kaga mu nan ba jin hausa ake ba". "ehh bross yana da speech me kyau, shi fa kawai dan dai yazo a mutumin karkara ne".
Emanuel yace da shi,"to kayi gaggawan sanar da shi yau, becouse within next tomorrow nake so ya fara gudanar da aiki, idan yana da iyali yana tunanin ba zai iya barinsu ba you should let me know za'a samar masa gida cikin gidajen Dad na GRA".
"okay bross". "ina Mommy?". Emanuel ya tambaya a san da ya kai apple baki ya gutsira. Obi yace, "Mommy sun je church ana bikin ƴar gidan Pastor Eze". "what about Dad?". "yana ɗakinsa, na fuskanci yau mood ɗinsa is not good, dan ko da naje gaishe shi bai amsa min ba kai ya ɗaga min kawai, kuma har na fito idonsa a rufe yake". Lokaci ɗaya hankalin Emanuel ya tashi, yay decline call ɗin ya ɗau wayansa ƙarama yay dialling numban mahaifinsa, har sai da ta yi ringing biyu ta katse sannan mahaifin nasa ya kira shi, ya ɗauki wayar murya ɗauke da damuwa ya shiga jerawa mahaifin nasa tambaya ba tare da ya ko amsa gaisuwar da Dad ɗin nasa ke masa ba.
"Dad meke faruwa da kai? Baka da lafiya ne?". Daga can ɓangaren General Tosin Afafa yace da ɗan nasa,"babu Wata matsala Son, ya office naka?". Emanuel bai yadda da maganar mahaifin nasa ba, ya dai ji shi ne kawai, saboda daga yanayin muryarsa za ka fahimci akwai damuwa tattare da shi. "Dad komai lafiya, sai dai ina so zan biyo jirgi gobe nazo na ganku". "no ba sai kazo ba mu ma ending this month zamu dawo, na gama gudanar da aikin da ya kawoni, ni kaina na gaji da zaman ƙasar nan...i dont know what is exactly happening to me amma hankalina gaba ɗaya yayo nigeria". Emanuel zai kuma magana Dad ya tari numfashinsa da cewa,"Son ka bar kallon news ne?". "a'a Dad, jiya ne dai da yau ban kalla ba saboda aiki da ya min yawa a office...yauwa Dad ko Md ya sanar da kai yan da ake ciki game da Contract ɗinmu da NDBH?". Dad yace da shi,"Son for now ka manta da wannan tukunna, ɗazu ina kallon news akwai yaran da akayi kidnapping from university, and the kidnappers are talking about 4millon kana su bayar da su, iyayen yaran kuma basu da kuɗin karɓo su, infact ma suna maganar cewar idan gwamnati ba zata taimaka masu ba zasu bar musu ƴaƴan tunda basu da yanda za suyi, so ina so ka fitar da wannan kuɗi aje a amso yaran daga nan zuwa yamma kaji ko...and dont let your Mum know about this issue plss". Emanuel ya amsa umarnin mahaifin nasa kamin kiran wayar nasu ya katse.
*Kano, Masarautar Bichi.*
Zaune muke a wani tamfatsetsen falo na gidan saurauta wanda aka ƙawata shi da kayan alatu iri-iri na mo re rayuwa, ni dai tun shigowarmu bin ko'ina nake da kallo ina jin dama ace mune acikin wannan daular, Adawiyya da ke kusa dani ta zungureni na juyo na dubeta, tana wani yatsine fuska tace,"Wai ke sai ance mana ƴan ƙauye". Na harareta nace,"to da su wane? Kinga ki rabu dani na kashe kwarkwatar idona yanda zan ji daɗin bada labari wataran, kuma sarai kin sani daga yau ba kuma shigowa zamu yi ba". Tasa hannu ta toshe dariyar da take ƙoƙarin yi, saboda ina nunawa Habiba wani abu kamar bal yana juyawa ta saman cikin ƙwai yana fesar da hayaƙi da ke bada daddaɗan ƙamshin a cikin falon. Ni tun ina jin daɗin zaman ma har na fara gajiya na fara jan tsaki, ga shi Ya Kabiru da ya kawomu yasa ƙafa yay tafiyarsa tun ɗazu da shi da Suhail. Na miƙe tsaye saboda yan da na gaji da zaman, baiwar da aka sa kula da mu ta doka min tsawa akan na koma na zauna, nayi firr da idona nayi ma ta banza kamar ban jita ba. Sai gata ta taso daga in da take cikin sassarfa tayo kaina, dukana za tayi kome oho mata, nasa hannu na dakatar da ita da cewar, "ke ni ba ɓarauniya bace balle kiyi zaton ko sata zanyi muku, ki bar ganin girman masarautar nan taku da daular da ke ciki to wallahi ba ku da abun da zan sata, dan ina da godiyar Allah a matsayin da ubangiji ya ajeni ciki, tashin da kika ga nayi tafiyata zan yi na gaji da wannan zaman shanyar da akai". Za tayi magana sai ga Jawad ya fito daga saitin ƙofar da mu ke tsaye, kunnensa sanye da abun jin kiɗa hannunsa kuma riƙe da waya yana dannawa, tafiya yake ko kallon gabansa bai yi, baiwar ta zube ƙasa tana jera masa kirari irin nasu na ƴan maula wanda har haushi sai da ta bani naji kamar nasa ƙafa na mangareta gefe. Bai ko bi ta kanta ba yazo wucewa ta kusa dani na taɓe baki naja ƙaramin tsaki wan da shi kaɗai ya iya jinsa, nan ya dakata da tafiyar ya ziro hannunsa ta wuyana ya ɗalle min baki, acikin kunnena yake faɗin,"yarinya idan tace zata min rashin kunya acikin gidanmu wallah sanyawa zan yi fadawa su zane min ita, koma nasa a maida ita tarihi sai naga da wanda zata kuma yi". Idan ya barni ma da jin zafin ɗallemin laɓɓa da yayi kaɗai ya isheni, banda kuma take ƙafa da yay min da wani shegen takalmi da ke ƙafarsa irin na ƴan sarauta, ya san da cewar naji zafi tun da yaji bakina ya ɗinke, amma duk da hakan bai ƙyaleni ba sai da ya kuma sa yatsa ya ɗalle min laɓɓana, zafin da naji a wannan karan yafi na ɗazu, idona ya cicciko cikin zafin nama na ɗauke han