NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 28 of 223

za kai a lokacin da yake kallonta ta gefen ido, a ransa yana ƙirga irin matsalolin da Joy ke haifar masa tun zuwanta kamfanin watanni biyar kenan, dama wannan ne last mistake da yake so ta ƙarayi sannan yaywa tufkar hanci. Jin shirun nasa yayi yawa yasa ta ƙara cewa da shi, "Sir zan iya yi musu iso?". "Am not available, so ki san yanda za ki da su". Sanin cewar ko da ta kuma yin magana ba zai saurareta ba ta juya ta fice da gwiwa a sace. Bayan wucewar daƙiƙu biyar da fitarta MD Simon Ya turo ƙofa ya shigo, har san da MD ya ƙaraso ya zauna a kujerar da suke fuskantar junansu Dr Emanuel bai ɗago ya dube shi ba, sai dai a yanda yaga yana karanta takardun dake aje kan table ɗinsa da kuma yanda ya dunƙule hannu ɗaya yasan cewar akwai damuwa, sai dai bai yi hanzarin katse shi ba har zuwa lokacin da Emanuel ya ɗago ya dube shi tare da tura masa takardun zuwa gabansa. Md ya ɗauki takardun yana karantawa, ya kalli Emanuel a sanda ya gama karantawar sannan yace, "amma Joy bata yi maka wani bayani dangane da shigar report ɗin ba?". "na kore ta". Md ya maimaita maganar tasa,"ka kore ta?". "yes". Md ya jinjina kai da faɗin,"amma dai a wannan karan bani zan sake nemo maka wata sakatariyar ba ko?, dan na gaji da nemo maka kana korarsu ɗaya bayan ɗaya haka kawai babu wani dalili". "Ba zan iya zama da marar gaskiya acikin aikina ba, kai kuma duk marasa gaskiya kake kawo min, so this time around na hutar da kai da kaina zan nemo". Md yay murmushi kawai, dan yasan a ƙarshe dai dole shi ɗin zai sa ya nemo masa. "ka san babban abunda ya ɓata min rai?". Md ya kaɗa masa kai yana me ƙara duban takardun hannunsa cike da takaici. "me yasa tun farko Yemi da yasan mutanen nan bana ƙwarai bane yaƙi sanar damu sai bayan da mu kai accepting contract ɗin nasu sannan zai dawo da takardun yace min ba zai sa hannu ba". "Dr ka ƙara duba sosai da nazari akan wannan lamarin, in har ba akwai wani mugun ƙullin a zuciyar Yemi ba, Babu yanda za'a ce morethan two weeks yana sane yaƙi signing kuma bai sanar ba sai a yanzu da ake son gama shigar da komai sannan zai ce contractor ɗin yayi rejecting, no way dole akwai wani abu a ƙasa". Emanuel ya ɗaga kafaɗa, "abun ya min ciwo amma kuma ba zai dame ni ba". "me yasa zaka faɗi haka? Wannan fa faɗuwa ce ke neman shafar kamfaninmu". Emanuel ya dube shi sosai sannan yace,"ai tun farko nace bana son kamfaninmu ya haɗa contract with any other companies, amma kai da Dad kuka ce ai NDBH ba abin yadawa bane, dan haka ni na cire hannuna, faɗuwarku ba daga ni bane daga gareku ne, kuje ku shawarta yan da za kuyi". Md ya dunƙule hannu ya doki table, "Ya za'ai ana talking of billions kace wai zaka zame hannunka aciki, kasan kuwa irin asarar da kamfanin zai samu, da kusan quarter ɗin kuɗinmu fa mu kai amfani". Yanda Emanuel ya ɗaga kafaɗa irin ko ajikinsa hakan kuwa ya ƙular da Md, ya kuma bi shi da ido har zuwa inda ya zauna kan cushion ɗin cikin office ɗin, ya ɗau coffee yana kaiwa bakinsa. "har wani lokacin shan coffee ma kake da shi?". Emanuel ya kalle shi ta cikin reflection glass na cup ɗin, ya motsa laɓɓansa kan ya kurɓi coffee ɗin sannan ya aje cup yace da shi, "me kake so nayi kuma?". Md ya girgiza kai ya miƙe ya koma kan kujerar Emanuel ya zauna, ya zari farar takarda yay short rubutu ajiki, Sannan ya miƙe yay tattaki zuwa inda Emanuel yake ya ajiye masa takardar a gabansa, ba tare da Emanuel ya dubi rubutun dake cikin takardar ba ya miƙa hannu ya karɓi biro daga hannun Md sannan yay signing a in da Md yay masa nuni. Cikin lokacin da basu haura daƙiƙa biyar ba Md ya buga takardar ya ninke yasa a envelop sannan ya fice daga office ɗin ba tare da yaywa Emanuel sallama ba, yana kuma jin san da Emanuel ɗin ke cewa da shi zai ɗauko ɗan arewa a matsayin sakatare na shi, yay banza da shi bai ce masa uffan ba domin ba abune mai yiwuwa ba dan Dad ma ba zai bar shi ba. *1hour pass.* Ta cikin Kamfutar da ke aje saman table Emanuel ke Vedio call da ƙanensa Obi, tambayarsa yake dangane da halayyar abokinsa ɗan arewa da su kai aiki shekaran baya. Obi ya buɗi baki yace,"Brother kana da study of psychology, dan haka a ɗan iya zaman da mu kai last time da Ahmed na san ka gama karantar halayensa". Emanuel ya kaɗa masa kai alaman haka ne sannan yace masa,"ku yi magana da shi kaji idan zai iya zaman Lagos, ina so zan ɗauke shi aiki matsayin sakatare mai kula da harkar shige da fice na office ɗina". Obi yay tsalle a saman royal bed ɗin da yake kwance, "what a great news, amma gaskiya brother naji daɗi sosai akan wannan tunanin da kayi na ɗaukan Ahmed aiki domin shi ɗin mutumin kirki ne, sam bashi da mugunta acikin zuciyarsa, ni shaidansa ne a zaman da muka yi na karatu da shi". Emanuel ya ƙara tambayarsa da cewar, "mene full name nasa?". "Ahmedu Adamu Bichi". "is he single or married?". "no he is single, amma ban sani ba ko zuwa yanzu yayi aure dan mun ɗau tsawon lokaci ba muyi waya ba since time da na bar nigeria". "i hope ya iya turanci tu
🏠