NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 27 of 223

i, Lagos State.* "Bullshit! taya za'ai Yemi zaiƙi sanya hannu akan abunda na tura masa, yaushe ya kai matakin daya fara take umarnina?". Dr Emanuel kenan, ingarman zakin namijin dake zaune kan lumtsatstsun cushion ɗin dake kewaye a matsakaicin parlon ke wannan maganar acikin harshen turanci, muryarsa na fita cikin ƙaraji, ya zare farin glasses ɗin dake sanye a idonsa ya ɗago ya dubi wanda ke tsaye a gabansa. "ina buƙatar ganin Samuel a office ɗina in the next 3hours". Yanzunma dai acikin harshen turanci yay maganar, Onoka ya rissinar da kai cike da girmamawa ogan nasa, sannan ya karɓi files ɗin da Dr Emanuel ya miƙo masa ya fita. *2hours Pass.* *Emzor Pharmaceutical Industries Limited.* Emzor Kamfanin ne na ƙera magunguna wanda aka kafa tun a shekarar 1984 a ƙasar Najeriya. Kamfanin da aka kafa da manufar yin samfurori masu inganci na magunguna. Kamfanin yana daga cikin jerun mayan kamfanunuwa guda goma da suka shahara a nigeria. Tun bayan da Obafemi Afafa mamallakin kamfanin ya rasu, Babban ɗansa me suna Tosin Afafa yaci gadon kamfanin kasancewarsa ɗa ɗaya tilo a wurin mahaifin nasa. To shi ma ayanzu ya maida Babban ɗansa me suna Dr Emanuel Tosin Afafa the CEO of the company, wanda ya kasance mai ƙwazo da himma wajen ganin kamfani na samun ci gaba ƙwarai da gaske. Duk da a baya bai taɓa zaton zai iya ɗaukar ragamar nauyin kamfanin ba, dan acewarsa ba ya jin zai iya ɗaukar all those responsibilites na shareholdings, business trip and rest, to amma da ya ke mahaifin nasa General Tosin tsayayye ne wanda ba ya magana biyu haka dole ya haƙura, ya ke kuma gudanar da ayyuka yanda ya kamata, kuma a sabbin tsarinsa da ya ke son aiwatarwa a yanzu yana so ne Mahaifinsa ya yarje masa ya shigo da sauran ƙannensa cikin wannan harkar, to amma mahaifin nasa yaƙi ba shi dama, ya sanar masa suma da akwai sauran kamfanin da yake son buɗewa wanda kuma yake tunanin watsa ƙannen nasa aciki wato Joseph da Obi. Duk da shi ɗin arnene da babu hasken musulunci tare da shi, amma kuma yana da kwarjini, cikar zati haɗe da wani irin farin jini da ko acikin musulmai ba kowa ubangiji ke mallakawa irinsu ba, shi yasa da yawan musulmai da suka san kyawun halayyarsa suke masa adu'ar Allah yasa ya musulunta. Tafiya yake da irin taku mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali na irin mutanen da jin daɗi har yay musu yawa, bai san talauci ba domin bai taso acikinsa ba, haka kuma bai san wahala ba dan bai saba da ita ba, sai dai kuma shi ɗin mutum ne mai tsananin tausayin talaka da son taimaka masa, walau ɗan'uwansa kafiri ko kuma musulmi. Tun da ya sanyo ƙafa cikin kamfanin ya sauya yanayin fuskarsa in da ya tamketa, dan sam baya bawa ma'aikatan fuskar da za su aikata abun da suka ga dama acikin ma'aikatar saɓanin yanda yake so su kasance. A duk wani taku da yake Oluwa na biye da shi a baya, hannunsa ɗaya riƙe da ash suite ɗin Oga ɗayan kuma riƙe da brief case nasa, har san da suka ƙaraso bakin office ɗinsa ne kuma ya miƙawa sakatariyarsa Joy kayan ta ƙarasa shiga da su. Joy ta shigo ta rataye rigar suite ɗin ajikin hanger, sannan ta kai brief case ɗin ta aje kan table tare da daɗa gyara wurin, ta tsaya tana kallon Dr Emanuel wanda ke tsaye a bakin window, ya zuba duka hannayensa cikin aljihun wando, yana ƙare kallo ga yanayin garin damunar da hadari ya haɗo a yanzu idanu na nuna ruwa na gab da sauka, ko da Joy tayi masa magana sai da ya ɗauki tsawon daƙiƙa kamin ya juyo yana zare baƙin glass ɗin da ke kewaye saman siririyar farar fuskarsa, Joy tayi saurin janye idanunta daga kallon nasa, ta rissinar da kai tana wasa da yatsun hannunta zuciyarta kuma na bugawa, har ya ƙaraso yaja kujera ya zauna bata sani ba sakamakon lulawa da tayi acan duniyar tunanin da ta ke yinsa a kullum na son ace yau ta mallaki Oganta. A hankali ya motsa laɓɓansa kamar wanda bai son yin magana, "ki cewa MD ina son ganinsa yanzu". Ta ɗago ido cikin rissinar da kai tace masa, "Bayani dangane da Vitro Health su na so ne mu haɗa contract da su akan magungunan da za'a fitar ƙarshen watan nan". "ki aje takardun zan yi tunani akai first kamin nayi singining, ki kuma ƙara min bincike akan kamfanin sosai kamin na bar office". Ta amsa masa da to sannan ta ƙara da cewa, "Jiya bayan fitarka babu jimawa kayi baƙi daga EDIG, yanzu haka ma su na reception su na jiranka". "dama ina da appointment da su ne a jiya da yau ɗin?". Daga yanda yayi mata tambayar ta san tayi ba dai-dai ba, dan haka sai da ta haɗiye wani yawu a maƙoshi kana ta amsa masa,"a'a baka da, hasalima cikin watan nan kaf baka sanya appointment da kowa ba". Ya bar shafa computer ɗin da yake ya kwantar da kansa jikin kujerar da ke juyi da shi, hannayensa a dunƙule ya lumshe ido sannan yace da ita,"amma me yasa kika barsu su na jira?". Jikinta ya hau tsuma ta fara inda-indar magana,"Naji sun ce ne maganar da za kuyi tana da muhimmanci, shi yasa har na amince musu akan su dawo a yau ɗin". Tai maganar tana aikin sosa ƙasan kuncinta. Ya girgi
🏠