NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 26 of 223

gane ba tambayar da yay tsammaci ji daga gareni bane, daga yanda naga ya tsareni da ido yana karantar wani abu tare da yanayin da na nutse a ciki ya saka na ce masa,"Yaya ko akwai wata kalma ta rashin dacewa a tambayana?". yace,"Mairo aina kika ji kalmar zina?". Nayi shiru na rasa abun ce masa, abunda kawai na ɗauka daga yanayin yanda ya mayar min tambayar shi ne kalmar tana da girma da kuma tsauri, ya katse tunanina da faɗin,"ke yarinya ce Mairo, ina ga lokacin da za ki san ma'anar wannan kalmar bai yi ba tukunna, domin ta yiwa kanki girma, ki jira zuwa wani lokaci za'ayi maku bayani a islamiya". Na kaɗa masa kai kawai sannan nace, "to sauran tambayan fa?". Ya ɗanyi ajiyar zuciya kana yace, "Dangana kalma ce ƴar'uwar haƙuri, irin haƙurin da mutum zai jure zafi da raɗaɗi akan wani abu da ya sameshi na tsanani acikin rayuwarsa, kamar mutuwa ko kuma mummunar ƙaddara". Na tsare shi da ido ina jiran sauran amsar, yay shiru kamar ba zai ce komai ba, cike da ƙosawa na kuma maimaita masa tambayar wace Kulu?. "ban san wace Kulu ba, ban kuma san daga ina tazo ba...". Nai saurin tarar numfashinsa,"Ya Amadu ba zan taɓa yarda da wannan maganar taka ba". "to Mairo ai maganar na fara kika yi saurin tarar numfashina ba ki tsaya kinji ƙarshen zance ba...ban san wace Kulu ba, ban kuma san daga ina ta ke ba, abun da kawai na sani ranar da aka haifeki ranar Kulu tazo gidan nan, da yake Gwaggo a can birnin kano ta haihu da suka tashi dawowa sai muka ga sun dawo tare da ita, kuma ko da aka tambayi Baba wace ita yace mara lafiya ce sun tsinceta ne a hanya, suka ga ba za su iya tafiya su barta acikin halin neman agaji da take ciki ba, shi ne suka ɗaukota suka taho da ita za su riƙeta a wurinsu har zuwa ranar da Allah zai sa ƴan'uwanta su nemeta". Nayi wani guntun murmushin jinjina ala'amarin Kulu, ban yi tantama ko ɗaya ba akan abun da ya faɗa ba dan nasan ba zai min ƙarya ba, tausayin Kulu kuma ya kamani matuƙa. "shikenan abun da kike son sani?". Na kaɗa masa kai,"a'a Ya Amadu, ina so na san sau nawa Kulu tayi magana tun zuwanta gidan nan?". "Kulu ai bata magana, yanda kika ganta haka take ba um ba umum...". Shigowar Ya Kabiru ta katse maganar da zanyi, muka maida dubanmu kansa, ya zauna yana cire rigar jikinsa, cikin tattausan muryarsa yake faɗin,"Zina na ɗaya daga cikin manyan kaba'iran da Allah ba ya so, ma'anar zina a taƙaice jima'i tsakanin namiji da mace, ba komai ke haifar da zina ba fa ce sharrin shaiɗan, biyewa ruɗin zuciya tare da afkawa matsananciyar soyayyar ɗa namiji da mace zata iya sadaukar da komai nata akansa...ki gujeta, ki kuma kiyayeta, domin abar ƙyama ce, tana da daɗi sai dai daɗinta na lokaci ƙalilanne, baƙin cikinta kuma tabbatace ne har ƙarshen rayuwa, ubangiji kuma ya tanadi hukunci me tsananin gaske ga waɗanda suka aikatata". Yay shiru ya miƙe yay tattaki ya saƙale rigarsa jikin ƙusa, Idona bai gushe da kallonsa ba, ina me cike da mamakin yanda akai yaji zancen da muke, har san da ya dawo ya zauna bakin tulun littafan da ke cikin wata ƴar ƙaramar durowar ɗakinsu ban ɗauke idona akansa ba. Nace,"to Yaya Kabiru mene shi jima'in da ka faɗa?". Ya buɗe baki zai bani amsa Ya Amadu ya dakatar da shi, "haba Kabiru, ya za'ai ka dinga faɗa mata kalmomin da sun fi ƙarfin kanta ne". "ba su fi ƙarfin kanta ba, hasalima yana da kyau ta sansu tun yanzu". Ya Amadu ya dubeni tare da cewar, "tashi kije". Na miƙe sanyi ƙalau na fice daga ɗakin. Ina shiga ɗaki kuma na tadda Kulu a bakin ƙofa tana gyara warwaron da ke tsintsiyar hannunta, na kalli warwaron sannan na kuma kallonta, na cuno baki gaba na miƙa mata hannu, "bani abuna". Ta dube ni sannan ta ciro ta bani, na wuceta na shiga ciki, ina ji ajikina da yanda ta ke bina da kallo, abun da ya bani mamaki shi ne warwaron dana ƙwace hannunta ba shi ne nawa ba, irinsu dai ɗaya, dan ina ɗaga ƙasan matashi naga nawa da na cire na ɓoye, kenan na hannunta na Gwaggo ne, na ɗago na dubeta har yanzu tana tsaye tana kallona, na murguɗa mata baki kaɗan sannan nace,"sai na faɗawa Gwaggo kina taɓa mata kaya". *Parkview Estate, Ikoyi, Lagos State.* "Bullshit! taya za'ai Samuel ya ƙi sanya hannu akan abunda na tura masa, yaushe ya kai matakin da ya fara take umarnina?". Dr Emanuel kenan, ingarman zakin namijin da ke zaune kan lumtsatstsun cushion ɗin da ke kewaye a matsakaicin parlon ke wannan maganar a cikin harshen turanci, muryarsa na fita cikin ƙaraji, ya zare farin glasses ɗin da ke sanye a idonsa ya ɗago ya dubi wanda ke tsaye a gabansa. "ina buƙatar ganin Samuel a office ɗina in the next 3hours". Yanzunma dai acikin harshen turanci yay maganar, Onoka ya rissinar da kai cike da girmamawa ogan nasa, sannan ya karɓi files ɗin hannunsa ya fita. *2hours Pass.* *Emzor Pharmaceutical Industries Limited.* *#Comment & Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *MissAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *9)* *Parkview Estate, Ikoy
🏠