jiya Liman ya aiko ban san na menene ba". Ya Amadu ya gyara zama da faɗin,"Allah yasa abun da na ke tsumayi ne". Ya faɗi hakan yana faɗaɗa fuskarsa da fara'a. Ya zaro takardun ya dudduba sannan ya fara yiwa Baba bayani farinciki tattare da shi,"ai takardun scholership ne wato tallafin karatun makaranta amma wannan ba daga gwamnati bane na masarautar bichi ne". Baba yace,"ah to masha'Allahu, da sunaye ajiki ne?". Ya ba shi amsa da,"a'a babu sunaye, takardun dai mutum uku ake nema, kuma na yara ne da za su shiga jss1 to ss1 ba wai na ƴan jami'a ba". "to Amadu wacce makaranta ce?". "makarantar gwamnatin tarayya ce da ke Minjibir amma fa ta kwana ce". "makarantar kwana kuma?". "ehh Baba". Gwaggo da ke gefe tace,"kace adu'a tace ta amsu, ni dama ai na jima ina yiwa yaran nan kwaɗayin makarantar kwana". Baba ya dubeta yace,"kin san kuwa makarantar kwana? ke bakiji irin illolinta da ake faɗa ba". Gwaggo ta sake cewa,"babu wata illa acikinta in har zaka bi ɗanka da adu'a, kuma in har ka yarda da tarbiyar da ka bawa ɗanka". Baba yayi shiru bai sake cewa komai ba na tsawon wasu daƙiƙu, kamin nan ya numfasa yace,"to ta maza ce ko mata, ko kuma a haɗe suke gaba ɗaya?". Ya Amadu yace,"ta Mata ce zallah, dan Allah Baba ka amince a miƙa yaran nan Mairo da Adawiyya da Habiba tun da kaga dukansu jss2 za su tafi". Baba yace da shi,"ni bance eh ba, ban kuma ce a'a ba, kawai dai ka aje takardun a wajenka zuwa lokacin da zan yanke shawara". Daga Habiba har Adawiyya da suke ta murna sai murnar ta koma ciki, ni kuwa da ma ina gefe ina fama da damuwar da na kimsawa raina akan baƙon lamarin da na fara cin karo da shi a jiya, nayi farinciki sosai dana ji batun ɗaukar nauyin karatu, ko babu komai an ragewa Baba nauyi, yanzu sai ya saka sauran yaran a makaranta, da ma bana jin daɗin rashin zuwan Basma makarantar boko, Ya Amadu da bai yanke tsammani da Baba zai barmu muje F.G.G.C Minjibir ba, har da tambayarmu ɗaya bayan ɗaya akan abun da muke so mu karanta, Adawiyya tace masa ita ma'aikaciyar lafiya ta ke so ta karanta, Habiba tace me tuƙin jirgin sama, babu wanda bai dara da maganarta ba a wurin, ni kuwa ko da ya tambayeni nace masa ina so na karanci aikin bincike, ta yanda zanke gano abu cikin sauƙi ba tare da ya caja min ƙwaƙwalwa ba, ya murmusa kan yace,"to gaba ɗayanku Allah ya bada sa'a".
Inna Amarya ce ta zaunar da ni tayi min bayanin jinin haila tas, tun daga lokacin zuwansa da lokacin da zai ɗauke, abun da zanyi da kuma wanda zan bari, da tarin tsoratarwa akan yanda zan kiyaye kaina.
Da yamma ina ɗakin Inna Amarya a kwance Saleh ya shigo yace naje inji Ya Amadu, na tashi kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki na fita, a zaure mu kai karo da Mu'azzam yana shigowa, har yay gaba ya dawo baya yana kallona, yay ƴar ƙaramar dariya yace,"Mairo wai lafiya?". Nace da shi,"lafiya lau, me ka gani?". Sai da ya kuma sakin ƙaramar dariya kana ya ce,"gani nai kina tafiya kamar ba Mairon da na sani a baya ba me tafiyar baragada, kuma har na bangajeki ba ki halin tsiwar taki ba, ko dai baki da lafiya?". Ya ƙarashe tambayar yana ɗora hannunsa a saman goshina, baki kawai na ɗan turo gaba na harare shi na wuce na barsa a wajen. Jingine daga jikin bango zaune na tadda Ya Amadu, shi ma tun shigowata yake bina da kallo, da ga ɗan nesa da shi na tsuguna da cewar,"gani Yaya". sai da ya sauke numfashi kana yace,"zo nan". Na tashi na ƙarasa kusa da shi na zauna, ya kamo hannuna ya taɓa tafin hannuna da kuma goshina da wuyana. "me ke damunki?". Na girgiza masa kai alamar babu komai. "yaushe kika fara ƙarya?". Na ɗago ido na dube shi wanda shi ma ni ɗin yake kallo.
Ya kwantar da kaina bisa kafaɗarsa, "faɗa min wani abu akayi miki? Ina kallonki ɗazu ba ki ci komai ba, kuma daga jiya zuwa yau kin rame sai kace kuɗin guzuri, walwalarki tayi ƙasa gaba ɗaya, ko ciwon cikinne har yanzu?". Nanma banyi magana ba na kuma girgiza masa kai. Sai ya yunƙura ya gyara zamansa sosai, ya fuskantoni tare da tallaɓar haɓata, ya sa na buɗe idanuna na sakasu acikin nasa, yaywa idanuwana kallon tsanaki tare da duban nazari sannan yace,"ni Yayanki ne mai tsananin sonki da ƙaunarki, wanda kaf cikin ƙannena idan aka cire Habiba nafi sonki da kowa, ku biyun nan bana so naga kun yi kuka balle wata damuwa ta dameku, faɗa min menene damuwar?, a makaranta ne ko kuma acikin gidan nan?". Na girgiza masa kai da ƙarfi nace,"duka babu ko ɗaya, kawai ina jin jikina babu daɗi ne". Sai naga ya tamke fuska, ya muskuta ya gyara zaman tare da barin fuskantata, "tashi kije". Naji kamar nasa kuka, ni Mairon ya zan yi, ta ina zan fara faɗawa Ya Amadu abubuwan da naji na gani, a hankali na fara magana,"Ya Amadu wasu al'amura ne suka shige min duhu wanda na ke neman sani akansu". kamar suɓutar baki kuma nace,"Ya Amadu wacece Kulu a gidan nan?, kuma menene zina? Ya ya kuma zina take?, sannan menene Dangana?". Naga ya wani juyo akaikaice yana dubana, ku san tambayar tawa ta girgiza shi, irin mamakin da naga ya bayyana ƙarara a saman fuskarsa na