NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 24 of 223

obar ice cream ɗin da Kabiru ya ajiye, dama a ɗazu tana kallon lokacin da ya ajiye kasancewar tana sallah, ta bar ma ta sauran ayaba da kankana, ice cream ɗin kuma ta zura shi ƙarƙashin sif ta yanda babu mai lura da shi. *#Comment and Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *MissAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *8)* Wayewar safiyar alhamis ɗin yau, kowa na gidamu na tsakar gida an zauna ana karin kullo safen, tun daga yaran har manyan, haka ƙa'idar gidanmu take a duk sanda za aci abinci musamman karin kumallon safe to haɗuwa ake gaba ɗaya, yaranmu da iyayenmu mata, su manyanne ake kai musu na su ɗaki, sai Baba ma da yake yin nasa a ɗaki da shi da wadda girki ke hannunta. Kowa abincinsa yake ci hankali kwance amma banda ni wadda natsuwa ta ƙarauce mata dalilin birkicewar tunani tun kwanaki biyu da suka wuce, abincin na gaba ina kallonsa amma hankalina gaba ɗaya ba ya kansa, tun ina jiyo sokiburutsun Adawiyya har na daina ji, na ma daina ganin komai da ke wakana a wajen, sai hoton Gwaggona da Kulu da ke haskawa cikin idona a wancan daren da kuma maganganunsu. Tun bayan komawata ɗaki dana samu na miƙe da ƙyar na koma kan gado na kwanta gudun kar Gwaggo ta fahimci farkawata, sun ɗau tsawon lokaci kamin su dawo ɗakin hannun Gwaggo riƙe dana Kulu, Ina kallonsu ta ƙasan ido ba tare da saninsu ba, dan ko da acema sun kalle ni ba za su taɓa gane idona biyu ba, dan nima yanda suka iya takunsu haka na iya nawa takun. Ina kallon yanda Gwaggo ta kwantar da kan Kulu bisa kafaɗarta tana aikin lallashin kuka da take, wanda sautinsa ke fita a hankali, kai baka ce Gwaggona bace wadda ke nuna tsantsar kyara ga Kulu a fili, "ki bar kukan nan haka Kulu, Basma zata iyaji kuma ta farka, duk da yarinya ce ita amma sanin kanki ne tana da wayon da zata iya ɗago wani abu". Kulu ta ɗago a kafaɗarta tana goge hawayenta, Gwaggo ta saki hannunta tana takawa a hankali ta ƙaraso gado, ina jin duk yanda take komai a hankali gudun karna farka, daga can in da Kulu ke kwance ta jefawa Gwaggo tambayar da ta ɗaure min kai matuƙa nake kuma neman wanda zai warware min ita anan kusa, ban da naci na son in gano wani abu da babu yanda za'ai na gane maganar da Kulu tayi, hausa take yi amma fa hausar a harɗe take, hausar da kai kana ji kasan bakin aronta yayi. "Yaya shi rubutun dangana idan ansha ɗin yana aiki?". Tambayar da ta yiwa Gwaggo kenan, kuma kamar ba zata amsa mata ba sai can tace mata,"to Kulu ayar Allah abar wasa ce, sunayen ubangiji fa aka rubuta da niyyar neman waraka ga buƙatar da ake nema daga gare shi...kiyi bacci haka asubahi na ƙaratowa". Ta kuma cewa da Gwaggo,"ina tsoro kar a bata taƙi sha, kin san halinta ba komai ake bata tasha ba musamman tasan cewa magani ne". "zata sha insha'Allahu, nasan da wanda zan haɗata". Daga haka cikinsu babu wanda ya kuma cewa komai, sai ni da suka bari da nisan tunani acikin ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwata, dan ko maganar wanda za'a bawa rubutun da suke magana akai kasa fahimta nayi tsakanin ni da Basama wa za'a bawa, na san dai ni ce wadda ake baiwa abu na sha naƙi sha matsawar aka danganta shi da magani, sai dai duk yanda naso na fahimci waɗancan sauran Al'amura da suka faru na gagara, haka ma na gagara fassara kalmar *DANGANA* da Kulu ta faɗa, kuma a safiyar yau ɗin kaina sai ya kuma ɗaurewa, domin rubutun da Gwaggo ta ɗauko mu uku ta bawa, da ni da Basma da Adawiyya, saboda na fahimci wani abu har turjiyar ƙarɓa na sha nayi amma sai naga Gwaggo ta banzatar da ni ta nawa Basma faɗan in har bata sha ba zata haɗata da Sunusi, anan na tabbatar da rubutun dangana ba nawa bane nata ne, to amma me yasa aka bamu muka sha ni da Adawiyya?, kuma mece Danganar?. Daga saman kaina na jiyo maganar Inna Zulai na cewa,"ita kuma waccan sillan karan meke damunta ta rafka tagumi kamar wata babbar macen da iyali suka tarar mata". Na buɗe Nauyayyun idanuna da ba su sami isashshen bacci ba daren jiya, na dubeta naga ta gwame baki ta dubi Inna Amarya tace,"waccan yarinyar dai ku dubata akwai abun da ke damunta". Inna Amarya da ke gyarawa Zubaida hijab tace, "ke kina gidan ma baki san bata da lafiya ba?". "to da ma abun da ya shafeku faɗa min kuke?, to Allah ya sauƙe". Tana faɗar hakan ta wuce ɗakinta, Inna Amarya ta rakata da faɗin,"kyaji da gulmarki". Ni kuma Inna Amarya ta hauni da faɗan matuƙar ban daina wannan tagumin ba raina zai ɓaci, Adawiyya ma tace mata aiko abincinma banci ba, nan ta kuma hawarni da faɗa sosai har sai dana ci abincin ba dan ina so ba kuma ba dan yayi min ɗanɗano a baki ba, ina da saka abu a rai sosai ko ya yake. Baba ya kira sunana yace na kira masa Ya Amadu ko Ya Kabiru, har na miƙe sai yace na koma na zauna ya manta ban da lafiya, Adawiyya ta tashi taje. Tare suka dawo da Ya Amadu wanda ke biye da ita a baya, ya tsuguna kusa da Baba, sannan Baba ya miƙa masa wasu takardu yana cewa,"duba nan kaga na menene, shaf ni na manta da su sai yanzu,
🏠