Ina so ne na haɗasu su duka ukun na sauke hakkin da ke kaina".
Gwaggo tace,"ni ban gama gane maganar su uku ba, Sadiya da Adawiyya da kuma wa?". "Mairo Mana".
Gwaggo ta gyara zama tace, "a'a dai Malam, Allah na tuba Mairo gaba ɗaya nawa ta-ke, bata ma yi girma da hankalin da za'ace za'a aurar da ita a yanzu ba ai...aiwa Yayyun nata dai ita ma idan lokacinta yayi sai a haɗata da sauran ƙannenta".
Zulai ta ce,"ke kuwa Suwaiba wanna girma kike so Mairo ta ƙarayi, idan kuma ba so kike tayi girman da zata taddomu ba. Ga sa'anninsu nan gaba ɗaya anata aurar da su, wasu ma harda ƴaƴansu".
"ke kika ga girman, ni dai banga girman da Ƴata ke da shi ba, shekara sha uku ne fa, shekarun da basu da maraba da shekara bakwai zuwa takwas". Malam ya murmusa fuska ya ce, "yanzu Suwaiba idan ba ƙin gaskiya ba har ace macen data shekara sha huɗj bata girma ba?". Ta karkata kai gefe tana tura baki gaba kamar ƙanƙanuwar yarinya,"ni ƴata ba tayi wannan shekarun ba, ni dana haifi abata nafi kowa riƙon shekarunta, dan Allah dan Annabi ma ni a daina sawa shekarunta ido".
Malam ya sauke numfashi kana yace,"to anji ƴarki bata yi wannan shekarun ba, amma dai kuma ai kin san ta isa aure ko?".
Gwaggo dai taɓe baki tayi bata ce ƙala ba, har sai da Malam ya kuma yin magana sannan tace, "ni fa Malam canji nake so a samu daga kan ƴata, ba aure nake so ayi mata ba, Karatun zamani nake so tayi me tsayi". Tunda Gwaggo ta faɗi haka bata kuma jiran cewar bakin kowa ba ta ɗaga labule ta fita, Malam ya bita da kallo cike da ɗumbin mamaki, ta sauya sosai fiye da tunani, duk ta yanda yaso yayi magana da ita saita tirje taƙi bashi dama, yanzu harma wani ƙin zama ta-ke yi tare da shi, idan shine kuma ya shiga ɗakinta zama na ƴan mintuna ne zasuyi ta tsiri bacci da bata shirya ba.
Zulai taci gaba da faɗin ita kuwa ba za'a sa ƴaƴanta su lalacewa ba, dan haka Malam ma ya bar tunanin haɗa auransu da Mairo, duk ranar da Mairo ta jawowa gidan magana uwarta zata gane ba gata tayi mata ba.
Ɓangaren Gwaggo kuwa tana fita su kai karo da Kabiru ya shigo, wanda dawowarsa daga aiki kenan, yay mata sannu da gida ta amsa masa, Ya tambayi jikin Mairo tace masa da sannu dan har ma tayi bacci tun ɗazu. "Allah ya sauƙe". Ya faɗi hakan tare da nufar ɗakin Gwaggon, a kusa da kanta ya ajiye mata robar ice cream ɗin da ya siyo mata, ya kuma ɗora ayaba da kankana akai.
Fitowarsa ya sami Gwaggo ta shimfiɗa tabarma ta zauna tana aikin zogale, yaja kujera ya zauna yana buɗe kwanon abinci, ita kuma ta fara magana kamar ba da shi ta-ke ba.
"Kabiru ka faɗawa Babanku muhimmacin karatun zamani, ka fahimtar da shi karatun zamani ko babu aiki anfi ƙarfin dai a cuci mutum balle a raina shi". "Gwaggo wani abu ya faru ne, ko yace yaran nan zasu tsaya da karatunsu ne?". "yana nufin haka mana, tunda yana kiran aurar da su zai yi, saboda Uwar masu gida tayi magana. To ni kuwa ba aure zan yiwa Mairo tah ba, karatu za tayi ta karanci aikin kotu". Ta faɗi hakan tana ci gaba da zagar zogale, Kabiru yay murmushi, maganar da zai yi ta katse sakamakon sallamar Amadu. Shi ma wuri ya nema ya zauna gefen Gwaggo akan tabarma, jikinsa da alamu na gajiya, Kabiru yace da shi,"wai dama ba kai na gani a masallaci ba". Amadu yace da shi,"ni ne mana, Mai gari ne wai yake neman matasan da suka yi karatun boko a wannan ƙauyen, shi ne na kai sunayenmu". Ya kalli Gwaggo yace,"Gwaggonmu ai mana adu'a Allah yasa a dace". Tace,"insha'Allahu ma za'a dace, ga dai Babanku nan ai yana nema ya yiwa karatun Mairo togaciya, yana ikirarin wai aure zai yi musu, saboda Uwani tayi magana".
Amadu ya miƙe daga kishingiɗen da yake,"aure kuma Gwaggo!"? Ya tambaya da mamaki. "uhmm". abunda ta iya cewa kenan. Ya shiga girgiza kai,"inaa dole ma Baba ya sauya tunani". Kabiru ma yace,"ai yama zama dole, ta ya su ɗin da aka samu suka fara katun kuma ace za'a dakatar dasu, karatun nan fa shi zai ji daɗinsa". Gwaggo ta kuma cewa, "ni dai na faɗa kuma zan ƙara faɗa ko za'a tsayarwa da kowa karatunsa banda Ƴata, dan insha'Allahu Mairo sai tayi karatun zamanin mai zurfi har ta zama lauya".
Amadu ya ce,"ah Gwaggo karatun likita dai ai mu shi ne burinmu akan Mairo, tunda tana da hazaƙa". Kabiru ya ɗora da faɗin, "kuma karatun likita ai yafi kowanne karatu muhimmanci da amfani a wajen Ƴa mace". Gwaggo ta taɓe baki, "in dai babu karatun banza ai babu laifi dan Mairo tayi karatun lauya, dan haka karku sa ma ta ƙahon zuƙa akan wani karatun likita, ku barta tayi karatun da zata shiga kotu ta gwabza da kowanne shege ta ƙwatowa Babanku gonakinsa". Kan su ƙara cewa wani abu Gwaggo ta miƙe ta nufa wurin ruwa dan wanke zogalen da Kabiru ya tayata zagewa.
Kulu dake zaune bakin ƙofar ɗakin Gwaggo ta faki idon kowa ta faɗa ɗakin, har yanzu Mairo bacci ta-ke bata tashi ba, ita haka kawai Allah ya haɗa jininta da yarinyar, tana sonta sosai wanda in da mahaifiyarta ta san irin son da ta-ke yi ma ta da ta mallaka ma ta ita.
ta ƙarasa bakin gadon cikin hanzari tai saurin ɗauke r