NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 221 of 223

miƙe ta bar min gidan bama ɗakin ba. ta fice ta barni tana jarabar ɓata ma ta cake ɗin da nayi, sauranma sai mage ta bawa ta cinye akan ta ban na ƙarasa shi...nace zan haɗa mata sharri wurin Jay tace na manta itama tana da Habibi, yarinyar nan tunda Ya Kabir ya haɗasu da Abdurrahim ta fitsare kamar shi. ashe dalilin tahowarmu da ita kenan, yace tausayin yarinyar da yake ji ne yasa shi ganin babu wanda ya dace da ya aureta kamar Abdurrahim, kuma kasancewar munbi duk da wata hanya da Nawwara zata ja hankalinsa nan da nan kuwa Abdurrahim ya amince da ita. yanzu haka bikinsu wata uku ya rage dan zuwanmu da wata bakwai muka je can inda har iyayen Abdurrahim ɗin muka tafi suka nema masa aurenta. *After 2days.* "ina kika maida wan nan kayan?* yana tsaye daga bakin closet ya kama ƙugu yake tambayana. nace da shi,"yanzu dan Allah kaya nawa gareka da zaka ce min ina na kai maka wannan kayan". sai yay murmushi ya wurgo min singlet ɗin hannunsa yana cewa,"to sarkin dalla dalla...kayan da Ishaq ke ɗinka min nake nufi". har yanzu hankalina na kan kayan Babies ena da nake ninkewa ina zubawa a riyo ɗinsu, haka nake kullum banda aikinyi sai na fito da su na ƙara ninkewa, takaicin hakan na ƙume Nawwara dalilin da ya sa ma kenan idan taga ban fito parlo ba zata kira wayana tace wai ina fama da rashin aikinyi. "ka manta kai kace na tattarasu gaba ɗaya na bawa Abubakar...kai Jay wai me yasa kake da mantuwa tun baka tsufa ba". yasa hannu yana shafo bayan wuyansa, ba tare da ya ce komai ba ya ƙaraso inda nake shima ya zauna a ƙasa kusa da ni, sai kallon cikina yake kafin nace da shi. "lafiya? kafa daina kallan mun yara dan kyauna nake so suyi ba naka ba". "ni dama ai nafi so suyi kyanki, kawai dai ina mamaki ne idan na tuna yanda da cikin nan ke a shamule". sai kuma ya tankwashe ƙafa ya kuma matsowa kusa da ni yana faɗin,"Preety wai nayi ƙoƙari kuwa ranar first night enmu?, har yanzu ji nake kaman a maido shi baya". na sauke masa ɓawon ayaban da na gama ci a fuska, ina cewa,"idan kwaɗayin ayaba ne ya kawoka ba baka zanba...gwara ka tashi kaje ka haɗa kayan wankinka dan ni daga nan har na haihu kayan ƴaƴana kawai zanke taɓawa". sai kawai naji hannunsa cikin rigana ya fito da breast ena yana faɗin,"ni ai ba mayen ayaba bane...kema kin san da wannan". na taɓe baki nace,"kasha iya shanka, twins na zuwa ya zama ƙwalelenka, tsakaninka da shi kallo daga nesa". *_Fashin Baƙi._* Na haifi kyawawan ƴaƴanna twins Mace dana miji, ranar suna kuma da aka sha shagalin da ko biki albarka suka ci sunayensu masu albarka, Namijin akasa masa Adam(sunan Baba) mu ke kiransa da Ramadhan, macen kuma Hajara wadda muke kiranta da Nihla. aiko munsha sababi wurin Yagana akan ba'a saka sunanta ba, wai dama ba son tsakani da Allah muke mata ba, da muna sonta har zuciyarmu sai muyi mata kara. Jay yace tasha kuruminta haihuwa ai yanzu aka fara, ta rubuta ta aje haihuwa ta gaba sunanta ne, tace daga baya kenan nan da shekara uku ko biyu ai tana gidanta na gaskiya. Anyi auren Abdurrahim da Nawwara inda suma suka tare nan kusa damu babu nisa, dan abotarsu da Yaya da gaske ne, kusan kullum kuma Nihla na wurin Nawwara acewata ni kam nafi son Ramadhan me sunan Babana, yaron da na ɗora dukkan so da ƙaunata akansa, ɗaukansa ma ban fiya so ayi ba, har faɗa mu kanyi da Jay wani lokacin dan idan na tattara hankalinta akan Ramadhan bana fuskantar kowa da komai. shima kuma duk sanda yaso ya rama idan ya ɗauki Nihla sai na kusan kuka sannan yake saurarona, dan shima yafi son mai sunan Mamansa. Ya Ahmad yayi aure shima, ya auri wata ma'aikaciyarsu me suna Ngozi ada, lokacin da ta zo wurinsa ta faɗa masa tana so ta shiga addininsu yaji duk duniyarsa babu macen da yake so sama da ita, kuma ta amsa kalmar shahada ta tashi daga Ngozi ta koma Nusaiba, su na nan zaune a lagos. Adawiyya ma tayi aure, ta auri tsohon saurayinta na farko da ta wulaƙanta shi akan Suhail. Inna Amarya kuwa ta kamu da paralize, inda aka maida ita gidansu taci gaba da jinyarta acan, ni dai tun ranar farko da muka je dubata ban ƙara sanin a halin da take ciki ba yanzu, ta zama bar tausayi maganarta sam bata fita, kamar me gwaranci, duk tabi ta ƙare ta lalace, ranar da muka je tana ta miƙo hannu wai zata taɓa su Nihla na doka ma ta tsawa nace "kull ɗinki, har yanzu ban mata da ke ki kai ajalin Gwaggona ba, ganina ma da kika yi anan darajar Mijina kika ci, amma ni ko a lahira ban fatan haɗuwa da ke, kuma har ki mutu ban yafe miki da abubuwan da kika mana ba". da zamu taho kuwa sai kuka take, Allah masanin abunda ta ke son cewa damu, ni kuwa a raina cewa nake dama ta mutu bata nemi yafiyar waɗanda ta cuta ba taji daɗin cin ubanta a ƙabari. shi kuwa sai wani jimami yake yana tausaya ma ta, haushi ma yasa har muka isa gida ban ƙara kula shi ba. Bross Almustapha ma yay aurensa, yana zaune da matarsa acan London. bayan tsawon wani lokaci, ina ɗauke da cikin wata tara Allah yayiwa Yagana rasuwa, bayan tayi fama da rashin lafiya, jinyar da ta za
🏠